29/12/2023
HAKURI 'IRIN NA ANNABI AYYUB.
Allah T yabawa annabi ayyub arziki na dukiya da 'ya'ya maza har 7 da 'ya'ya mata kwatankwacinsu, sai Allah yayi nufin ya jarabci bawansa kuma annabinsa ayyub, sai kasuwancinsa s**a karye, yayansa s**a mutu, gidansa ya rushe, dabbobinsa s**a mutu sannan Allah ya jarabceshi da rashin lafiya ajikinsa.
Lokacin da rashin lafiya ta tsananta gareshi mutane s**a gujeshi don tsoron karsu gogi kalan rashin lafiyan, s**a fitar dashi wajen gari ba wanda yatsaya tareda shi sai matarshi tana masa hidima tana kula dashi, takanje tayi aiki a gidaje don tasamu kudin dazata kula da kanta da mijinta.
Bayan wani lokaci sai mutanen gari s**a kyamaceta tsoron kada su gogi cutan mijinta a jikinta har yakai babu wanda zai dauketa aiki.
Ance annabi ayyuba ya rayu tareda wannan cuta tsawon shekara 18 yana hakuri bai taba kai kuka ga kowa ba, lokacin da matarsa taga yanayi ya tsananta a garesu sai tace, ya annabin Allah ka roki Allah ya yaye maka wannan bala'i, sai yace shekara Nawa mukayi acikin jin dadi? Tace 80, yace inajin kunyar Allah saboda banyi rayuwar da takai na jin dadinaba da Allah yayimin acikin wannan bala'i.
Sai matarsa lokacin data rasa mafita ta yanke shawaran siyar da Rabin gashinta don tasamu abincin da zasuci, lokacin data kawo abincin annabi ayyub ya tambayeta ina tasamu bata fada ba, washe gari ta siyar da gashinta saura takara samo musu abinci s**aci.
Lokacin da kanta ya yaye sai annabi ayyub yaga babu gashi sai ya fahimta meke faruwa, sai yaji kunyan ubangiji kar yaroki shi yabashi lafiya sai yace kamar yadda Qur'ani yazo dashi.
"ربي إني مسني الضر وأنت أرØÙ… الراØÙ…ين"
Ya Allah ni cuta ta sameni kuma Kaine mafi jinkan masu jinkai.
Sai al'amari yazo daga wurin Allah madaukakin sarki cewa, "أركض برجلك هذا مغتسل بارد و شراب"
Ka shuri kasa da kafarka ruwa mai Sanyi zai fito nasha da wanka.
Lokacin da Allah T ya h**e mai wannan ruwa na waraka da yasha yayi wanka sai yatashi garau kamar bai taba yin cuta ba, sai matarshi ta dawo bata ga