23/07/2023
TSAKANIN KIMIYYA DA SUNNAH AKAN KISAN TSAKA
Wani ɗan uwa ya yi min tambaya akan tsaka cewa wai a ina aka ce tana da guba a cikin hadisi? Sai na ce masa ban sani ba. Daga baya sai na ga ashe ana ta zance ne akan tsaka sakamakon wani labari da BBC Hausa s**a buga. Duk da ba na son shiga irin wannan sabgogin amma dai ina da wani ta'aliƙi kamar haka.
A cikin hadisai mabanbanta Manzon Allah (SAW) ya yi umarnin cewa a kashe tsaka tare da ambaton ta a matsayin sheɗaniyar halitta.
Daga cikin hadisan akwai hadisin Bukhari da Muslim wanda s**a ruwaito daga Ummu Sharik da take cewa: "Manzon Allah (SAW) ya yi umarni da a kashe tsaka sannan ya ce: ita tsaka ta kasance ita ce kaɗai dabbar da ta dinga ƙoƙarin hura wutar da kafirai s**a yi nufin ƙona Annabi Ibrahim (AS) a cikinta". Abubakar Ibnul Arabiy yana cewa: "Wannan yana nufi izuwa ga cewa cutarwa wata ɗabi'a ce ta dindindin a wajen tsaka"
A wata riwaya ta Ahmad da Ibnu Majah da Ibnu Hibbana (wannan lafazinsa ne) cewa aka yi wata bararriyar baiwar Al-Fakih Ibnul Mugeerah ce ta shiga gidan Aisha (RA) sai ta ga wani mashi a ajiye, sai ta ce da Aisha: me kuke yi da wannan? Sai ta ce: muna kashe tsaka ne da shi. Saboda Manzon Allah (SAW) ya ba mu labarin cewa lokacin da aka wurga Ibrahim (AS) a wuta ba wata dabba a duniya sai da ta yi ƙoƙarin kashe wutar, in ban da tsaka; ita kam ƙoƙarin hura wutar ta yi. Saboda haka Manzon Allah (SAW) ya yi umarni da a kashe ta.
Sai dai wannan riwaya ta saɓa wa abin da Urwah ya ambata daga Aisha (RA) a cikin Bukhari da Muslim inda take cewa: "Na ji Manzon Allah (SAW) cewa tsaka hatsabibiyar dabba ce, amma ban ya ce a kashe ta ba". Amma dai wasu Sahabban irin su Abu Sa'idin al-Khudriy (RA) sun tabbatar sun ji daga Manzon Allah (SAW).
Har ila yau, a cikin Saheehu Muslim daga Abu Huraira (RA) ya ambaci fifikon ladan da Manzon Allah (SAW) ya zayyana ga wanda ya kashe tsaka kwaf ɗaya, sai kuma wanda ya yi mata duka biyu, daga nan kuma sai duka uku.
Duba izuwa ga waɗannan hadisan shine ya sa Al-Allamah Muhammad Bn Salih Al-Uthaimeen yake cewa: "Kashe tsaka Sunnah ce wacce take da lada mai yawa".
A taƙaice, duk wanda ya kalli hadisan zai ga cewa sun yi umarni da a kashe tsaka ne saboda hatsabibancinta. Amma dai ni a iya ɗan ƙaramin bincikena, ban san hadisin da ayyana cewa tana da guba ba. Me yiwuwa in an tsananta bincike a samu.
A ɓangaren masana kimiyya kuwa, suna da bincike daɗaɗɗe akanta. Abin da na taɓa karantawa da daɗewa shine maganar wani Farfesa mutumin South Africa dake cewa tsaka ba ta da wani abu na cutarwa, hasalima a cewar sa, tana taimakawa wajen kawar da ƙananan ƙwari daga gida.
Haka ma Farfesa Aaron M. Bauer; wani masani a fannin Biodiversity a jami'ar Villanova University dake Pennsylvania ya yi magana cewa shi a ganinsa, kasancewar ɗan adam da tsaka sun rayu tsawon dubban ɗaruruwan shekaru ba tare da wata matsala ba, to bai kamata a kashe ta ba.
Irin waɗannan maganganun ba su da wata ƙima a gun musulmin da ya san girman Manzon Allah(SAW) sannan kuma yake gaskata shi. Saboda haka kashe tsaka shine gaskiyar da mu musulmi muka yarda da ita.
Sai dai kuma, a ƙashin gaskiya nima na saurari maganar likitan dabbobin da ake ta magana akai amma ni ban fahimci cewa tana ƙaryata hadisan bane. Don ba ta ce kar a kashe tsaka ba. Ba ta ce tsaka ba ta cutarwa ba. Sai dai kawai ta yi magana ne akan masdarin da tsaka ke samo ƙwayoyin cutar da take cutar da mutane da su, wanda shine ya saɓa da abin da muka saba ji. Ɗan Adam kuma ya gaji ɗabiar saurin jayyayya da abin da ya saɓa wa wanda ya saba ji.
Ina shawararta kaina da sauran ƴan uwa cewa mu dinga bin abubuwa a sannu. Kafin mutum ya yi magana akan mas'ala akwai buƙatar ya fahimce tukunna.
Allah Ubangiji shine mafi sani.
Munkwafo daga shafin
Sheikh, Dr. Kabir Asgar As-Salafy