25/03/2022
FASSARAR AL-QUR'ANI.
Darasi Na Tara 009
Suratul Baqara/سورة البقرة
Chapter: 2 Verse 73-83.
بسم الله الرحمن الرحيم
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinqai.
Ci gaba da Bayanin irin ni'imomin da Allah yayi akan Banu isra'ila.
ثُمَّ قَسَتْ قُلُوبُكُمْ مِنْ بَعْدِ ذَلِكَ فَهِيَ كَالْحِجَارَةِ أَوْ أَشَدُّ قَسْوَةً وَإِنَّ مِنَ الْحِجَارَةِ لَمَا يَتَفَجَّرُ مِنْهُ الْأَنْهَارُ وَإِنَّ مِنْهَا لَمَا يَشَّقَّقُ فَيَخْرُجُ مِنْهُ الْمَاءُ وَإِنَّ مِنْهَا لَمَا يَهْبِطُ مِنْ خَشْيَةِ اللَّهِ وَمَا اللَّهُ بِغَافِلٍ عَمَّا تَعْمَلُونَ
MA'ANA:
San'nan kuma zukatanku, s**a ƙeƙashe daga bayan wancan(ai,daga bayan wancan ni'imomin da Allah yayi muku da Kuma ayoyin Shi da ya nuna muku abayyane yadda yadda yake rayar da matacce) Saboda haka (sai su yahudawan nan) s**a zamanto k**ar duwatsu (wajen kekashewar zuciya) Ko mafi tsananin ƙeƙashewa (ai, koma fiye da duwastu ma'ana ai zuciyar wadannan yahudawa tama fi duwastu kekashewa a domin kuwa) kuma (ana samu) lalle ga duwatsu, haƙika, akwai abin da maremari suke ɓuɓɓuga daga gare shi, kuma lalle ne daga gare su,(Duwatsun) haƙiƙa, akwai abin da yake tsatstsagewa har ruwa ya fita daga gare shi, kuma lalle ne, haƙiƙa, daga gare su,(duwatsun) haƙiƙa, akwai Wanda yake faɗowa domin tsoron Allah kuma Allah bai zama gafili ba daga barin abin da kuke aikatawa (ma'ana ai Ubangiji Allah bai manta irin abubuwan da kuke aikatawa ba na saba mishi da kafircewa da ayoyin shi, ku banu isra'ila).
أَفَتَطْمَعُونَ أَنْ يُؤْمِنُوا لَكُمْ وَقَدْ كَانَ فَرِيقٌ مِنْهُمْ يَسْمَعُونَ كَلَامَ اللَّهِ ثُمَّ يُحَرِّفُونَهُ مِنْ بَعْدِ مَا عَقَلُوهُ وَهُمْ يَعْلَمُونَ
MA'ANA:
Shin (Yanzu ku muninai) kuna tsammanin (su yahudawa) za su yi imani saboda ku, (ne) alhali kuwa, haƙiƙa, wata ƙungiya daga gare su sun kasance suna jin maganar Allah, sa'an nan kuma su karkatar (ai, sai su canza) da ita (da son zuciyar su) daga bayan sun gane ta (haƙiƙa maganar Allah ce), alhali (kuwa) su, suna sane (ma'ana ai su da hankalinsu kuma sun san abinda sukeyi da abinda Sukayi cewa ba dede bama amma kuma dukda haka suna ci gaba da aikatawa ko ajikin su)?
وإذا لقلو الذين ءامنوا قلوا ءامنا وإذ خلا بعضهم الى بعض قلو أتحدثونهم بما فتح الله عليكم ليحا جوكم به عند ربكم افلا تعقلون
MA'ANA:
Kuma idan (su yahudawa) sun haɗu da waɗanda s**a yi imani s**an ce: "Mun yi imani," kuma idan sashensu ya wofinta zuwa ga sashe, s**an ce (ga 'yan uwansu yahudawa cewa) "Shin, kuna yi musu (musulmi) magana da abin da Allah Ya buɗa muku ne (acikin attaura) domin su yi muku hujja da shi a wurin Ubangijinku?" Shin fa, ba ku hankalta (ne 'yan uwa yahudawa)?
Sai Allahu SWT yace"
أَوَلَا يَعْلَمُونَ أَنَّ اللَّهَ يَعْلَمُ مَا يُسِرُّونَ وَمَا يُعْلِنُونَ
MA'ANA:
Shin, kuma (su yahudawannan) ba su sanin cewa lalle ne Allah Yana sanin abin da suke ɓoyewa (na siffofin annabi Muhammad SAW acikin attaura) da (kuma) abin da suke bayyanawa (na cewa sunyi Imani abaki aboye kuwa qarya sukeyi, shin ashe basu san cewa Allah ya san komai ba da sukeyi)?
Sai Allah yace"
وَمِنْهُمْ أُمِّيُّونَ لَا يَعْلَمُونَ الْكِتَابَ إِلَّا أَمَانِيَّ وَإِنْ هُمْ إِلَّا يَظُنُّونَ
MA'ANA:
Kuma daga cikinsu (su yahudawa) akwai ummiyyai, ba su da sanin Littafi,(ai, basu amfanuwa da abinda yake cikin littafin attaura) face tatsuniyoyi (na wofi da s**a biyewa), kuma su ba kome suke yi ba face suna yin zato (ma'ana ai basuda wata hujja da s**a riqa daga Allah a cikin dukkan abubuwan da suke aikatawa saide zato da rayawar jahilcin su kawai, Kuma s**e ai hakan daga Allah ne).
Shine sai Allah yace"
فَوَيْلٌ لِلَّذِينَ يَكْتُبُونَ الْكِتَابَ بِأَيْدِيهِمْ ثُمَّ يَقُولُونَ هَذَا مِنْ عِنْدِ اللَّهِ لِيَشْتَرُوا بِهِ ثَمَنًا قَلِيلًا فَوَيْلٌ لَهُمْ مِمَّا كَتَبَتْ أَيْدِيهِمْ وَوَيْلٌ لَهُمْ مِمَّا يَكْسِبُونَ
MA'ANA:
To, bone ya tabbata ga waɗanda suke rubuta littafi da hannuwansu (ai suke furta magana da bakunan su) sa'an nan kuma su ce wannan daga wurin Allah yake, domin su sayi kuɗi kaɗan da shi (ai, a domin su samu wasu yan kudade a duniya) san nan bone (narkon azaba) ya tabbata a gare su daga abin da hannayensu ke rubutawa, kuma bone (Narkon Azaba) ya tabbata a gare su daga abin da suke sana'antarwa (wato littafin Allah).
وَقَالُوا لَنْ تَمَسَّنَا النَّارُ إِلَّا أَيَّامًا مَعْدُودَةً قُلْ أَتَّخَذْتُمْ عِنْدَ اللَّهِ عَهْدًا فَلَنْ يُخْلِفَ اللَّهُ عَهْدَهُ أَمْ تَقُولُونَ عَلَى اللَّهِ مَا لَا تَعْلَمُونَ
MA'ANA:
Kuma s**a ce (su yahudawa wai) Wuta ba za ta shafe mu ba, face, 'yan kwanuka ƙidayayyu. (Wai kkwanakinda iyayen su s**a bautatawa dan maraqi, Shine Sai Allah yace ya Muhammad SAW) Ka ce: (musu shin) "Ashe kun riƙi wani alkawari a wurin Allah (ne na cewa baze kona ku ba face na wassu kwanaki?), sa'an nan (Kuma) Allah ba zai saɓa wa alkawarinSa ba ko kuwa kuna faɗin abin da ba ku sani ba bisa ga Allah?" (Ma'ana su yahudawa bakomai bane face suna fadin abinda basu sani bane dangane da Allah).
Sai Allah kude sani da kyau, wato yace"
بَلَى مَنْ كَسَبَ سَيِّئَةً وَأَحَاطَتْ بِهِ خَطِيئَتُهُ فَأُولَئِكَ أَصْحَابُ النَّارِ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ
MA'ANA:
Na'am!(ma'ana a'a ba haka bade abin nufi kawai Shine duk) Wanda ya yi tsiwur-wurin mugun abu, (ai ya aikata mugun abu) kuma laifinsa ya kewaye shi,(ai ya zamo lefukan shi sun rinjayi alherin Shi) to, waɗannan su ne 'yan Wuta, su a cikinta madawwama ne.
وَالَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ أُولَئِكَ أَصْحَابُ الْجَنَّةِ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ
MA'ANA:
Kuma waɗanda s**a yi imani (da Allah da manzon Shi) kuma s**a aikata ayyukan ƙwarai, waɗannan, 'yan Aljanna ne, su a cikinta madawwama ne.
Sai Allah yace ya Muhammad SAW kace ga Banu isra'ila"
وَإِذْ أَخَذْنَا مِيثَاقَ بَنِي إِسْرَائِيلَ لَا تَعْبُدُونَ إِلَّا اللَّهَ وَبِالْوَالِدَيْنِ إِحْسَانًا وَذِي الْقُرْبَى وَالْيَتَامَى وَالْمَسَاكِينِ وَقُولُوا لِلنَّاسِ حُسْنًا وَأَقِيمُوا الصَّلَاةَ وَآتُوا الزَّكَاةَ ثُمَّ تَوَلَّيْتُمْ إِلَّا قَلِيلًا مِنْكُمْ وَأَنْتُمْ مُعْرِضُونَ
MA'ANA:
Kuma (ku tina) a lokacin da Muka karɓi alkawarin Bani-Isra'ila:(ai al-kawarin ubanninku cewa) "Kada ku bauta wa kowa face Allah, kuma ga mahaifa ku kyautata (musu) da makusantan ku (Dangi da 'yan uwa) da marayu da matalauta, (dukkan wadannan ku kyautata musu) kuma ku faɗi magana mai kyau zuwa ga mutane, kuma ku tsayar da salla, kuma ku bayar da zakka, sa'an nan (Sai gashi Nan) kuka juya baya (akan dukkan al-kawarin dake Tsakanin ku da Allah), face kaɗan daga gare ku,(sune s**a riqe wannan al-kawarin) alhali kuwa (mafi yawanku) kuna masu bijirawa (alkawarin).
وَإِذْ أَخَذْنَا مِيثَاقَكُمْ لَا تَسْفِكُونَ دِمَاءَكُمْ وَلَا تُخْرِجُونَ أَنْفُسَكُمْ مِنْ دِيَارِكُمْ ثُمَّ أَقْرَرْتُمْ وَأَنْتُمْ تَشْهَدُونَ
MA'ANA:
(Kuma ku tina) Lokacin da Muka riƙi alkawarinku; (cewa) ba za ku zubar da jininku ba, kuma ba za ku fitar da kanku daga gidajenku ba; sa'an nan kuka tabbatar (ai, sai gashi kuna zubar da jinin junanku kuma kuna koyar 'yan uwanku daga gidajen su) alhali kuwa kuna bayar da shaida (a kanku).
ثُمَّ أَنْتُمْ هَؤُلَاءِ تَقْتُلُونَ أَنْفُسَكُمْ وَتُخْرِجُونَ فَرِيقًا مِنْكُمْ مِنْ دِيَارِهِمْ تَظَاهَرُونَ عَلَيْهِمْ بِالْإِثْمِ وَالْعُدْوَانِ وَإِنْ يَأْتُوكُمْ أُسَارَى تُفَادُوهُمْ وَهُوَ مُحَرَّمٌ عَلَيْكُمْ إِخْرَاجُهُمْ أَفَتُؤْمِنُونَ بِبَعْضِ الْكِتَابِ وَتَكْفُرُونَ بِبَعْضٍ فَمَا جَزَاءُ مَنْ يَفْعَلُ ذَلِكَ مِنْكُمْ إِلَّا خِزْيٌ فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا وَيَوْمَ الْقِيَامَةِ يُرَدُّونَ إِلَى أَشَدِّ الْعَذَابِ وَمَا اللَّهُ بِغَافِلٍ عَمَّا تَعْمَلُونَ
MA'ANA:
Sa'an nan kuma, (Sai) ga ku, ya (ku) waɗannan! (Yahudawa) Kuna kashe kanku, kuma kuna fitar da wani ɓangare daga gare ku daga gidajensu, kuna taimakon juna a kansu da zunubi da zalunci kuma idan k**ammu s**a je muku kuna fansarsu (wato sai gashi kuna aikata wani bangare na alakwari shine fanso 'Yan uwanku, amma kuna sabawa wani bangare na alkawarin) alhali kuwa shi fitar da su ('yan uwanku daga gidajen) abin da aka haramta muku ne (amma kuna aikatawa). Shin fa, kuna imani da sashen Littafin ne, kuma ku kafirta da sashe? To, mene ne sak**akon wanda ke aikata wancan daga gare ku face wulakanci a cikin rayuwar duniya? Kuma a Ranar alqiyama ana mayar da su zuwa ga mafi tsananin azaba. Kuma Allah bai zama Mai gafala ba daga barin abin da kuke aikatawa.
Sai Allah yace toh"
أُولَئِكَ الَّذِينَ اشْتَرَوُا الْحَيَاةَ الدُّنْيَا بِالْآخِرَةِ فَلَا يُخَفَّفُ عَنْهُمُ الْعَذَابُ وَلَا هُمْ يُنْصَرُونَ
MA'ANA:
Waɗannan su ne waɗanda s**a sayi rayuwar duniya da Lahira (ai s**a zami Qarya a maimakon Gaskiya a), domin haka (Allah yace) ba za a sauƙaƙa azaba ba daga kansu, kuma su, ba ataimakonsu (ai babu mai temakon su akan azabar da Allah ze musu har abada).
SHARHI ATAQAICE:
Su wadannan ayoyi wadanda suke bamu labarin irin abubuwa na ni'imoni da Kuma abubuwa na kafirci da Banu isra'ila s**a aikata, kuma har kawo izuwa zamanin Annabi Muhammad SAW ga irin abubuwa da suke yi na munafirci da kafircewa ayoyin Allah.
Kuma ayoyi ne da nuna mana cewa su yahudawa mutane masu sonzuciya marasa Amana dan gane da maganar Allah, karya da yaudara sukeyi ga mabiyan su a domin samun abinda Duniya.
Kuma su yahudawa sune Wanda Allah ya basu dama ya musu ni'ima da ilimi ,amma se gashi suna saba alkawarin Allah, na cewa za suyi ibada gareshi ma'ana zasu bi abinda yake cikin attaura, Kuma za subi Annabin Qarshen zamani, sai kuma gashi sun saba alkawarin saboda hassada da zalunci irin na wasu daga cikin su.
Kuma ayoyi ne da s**a fallasa yahudawa maqiya Allah maqiya Manzon Allah Annabi Muhammad SAW Na irin abubuwa da s**a boye a cikin littafin attaura na siffofin annabi muhammad SAW da halayyan shi, s**a hana a bayyana su ga mabiyan su da sauran mutane, sai s**a caccanza abubuwa da yawa acikin Littafin attaura a domin su boye Gaskiya Kuma su samu abin Duniya.
Wadannan ayoyi ne da suke yi mana wa'azi da gargadi cewa kada mu sake mu fadi karyan akan Allah ,ko mu aikata wani abunda bamuda ilimi akanshi, a saboda ga irin Sak**ako da kaskanci da wulakanci da mutum ka iyi samu a saboda aikata hakan.
Kuma ayoyi ne da suke fadakar damu mu Al-ummar Annabi Muhammad SAW akan dukkan Wanda yayi Imani da Allah kuma yayi Imani da Manzon Allah kuma yayi aiki mai kyau, toh shi Kam yana a cikin aljannah.
Sa'annan Kuma dukkan Wanda yaqi Allah ya kauda da Kai ga abunda Annabi yazo dashi, yabi hanyar shedan ya zabi Qarya akan Gaskiya, toh haqiqa shikan ya halaka kuma Yana a wuta.
WALLAHU A'ALAM.
Ya Allah Ka tsaremu daga Azabar wuta, kasa mu a cikin aljannar fiddausi.
+2348168311092
Tambayoyi akan darasi.