Arewa Students' Orientation Forum, Gombe State Chapter

Arewa Students' Orientation Forum, Gombe State Chapter

Share

Arewa Students' Orientation Forum (ASOF) is a non-profit educational organization aimed at orienting

02/11/2024


20/01/2024

ABUBUWA 6 DA YA KAMATA ƊALIBAN JAMB SU YI LA'AKARI DA SU, KAFIN ZAƁAR MAKARANTA

Mafi yawa daga cikin ɗaliban da ke rijistar jarrabawar JAMB UTME, su na halartar cibiyoyin rijista ne, ba tare da sanin haƙiƙanin makarantun da ya kamata su sanya a matsayin zaɓukansu (choices) ba. Hakan ya sa mu ka yi nazari, tare da wallafa muku wasu abubuwa shida, da ya kamata a ce kun yi la'akari da su, kafin zaɓar kowacce makaranta, a matsayin wacce ku ke muradin yin karatu a ciki.

Yin zaɓin ƙwarai ta fuskar makarantun da ake son yin karatu a ciki, ko akasin hakan, na taka gagarumar rawa, a cikin sha'anin samun guraben karatu (Admissions), da ma bayan kammala karatun.

Ga Jerin Abubuwan Da Ya Kamata Ku Lura Da Su Kafin Zaɓar Kowacce Irin Makaranta :

1• Ku tabbatar an tantance makarantar, tare da course ɗin da ku ke son karantawa :

Wannan ita ce gaɓa mafi muhimmanci, a ya yin da ake yunƙurin zaɓar Makaranta, ko Jami'ar da ake muradin yin karatu, domin kuwa akwai Jami'o'i da Makarantu da dama da su ke karantar da wasu kwasa-kwasai, ba tare da sahalewar hukumar NUC, ko sauran hukumomin da ke da alhakin tantancewa ba. Saboda haka ku tabbatar NUC ta tantance Course ɗin da ku ke son karantawa a Jami'ar da ku ke da muradi, domin karantar wani Course ba tare da tantance shi ba, dai-dai ya ke da ɓata lokaci.

2• Cathment Area Na Makarantar :

Ya na da kyau ku san Cathment Area na dukkannin wata Makaranta, ko Jami'ar da ku ke son cikewa, domin kuwa catchment area ne, zai nuna muku sauƙin yiwuwar samun Admission ɗinku a wannan makarantar, ko akasin haka, duba da cewar, kowacce makaranta ta na ɗaukar kaso mafi tsoka na ɗalibanta ne, a yankunan da ke matsayin cathment areas ɗinta. Misali : Babbar Cathment Area ɗin Jami'ar Bayero, ita ce Kano, saboda haka dukkannin ɗaliban da su ka nemi gurbin karatu a Jami'ar daga Kano samun Admission zai fi musu sauƙi, fiye da wanda ya nemeta daga Ekiti.

Ku Lura : Ba wai muna nufin ka da ɗalibi ya nemi Jami'ar da ba ta cikin cathment area ɗinsa bane, a'a kawai dai mun bayyana irin rawar da cathment area ta ke takawa ne, wajen samun gurbin karatu (Admission) cikin sauƙi, da irin fifikon da makarantun su ke bawa Ɗaliban jihohinsu.

3• Sanin Tarihin Yawan Tsundumar Makarantar Yajin Aiki :

Ba ya ga Yajin Aikin al'ada, da ƙungiyoyin ASUU da ASUP su ka saba shiga, lokaci bayan lokaci, akwai makarantun da su ka yi shura wajen shiga Yajin Aikin cikin gida, wanda hakan ke kawo tasgaro ga karatun Ɗalibansu, tare da tsawaita musu zaman gida. Saboda haka fahimtar ko makarantar da ka ke son nema ta na yawan tsunduma Yajin Aikin cikin gida, muhimmin abu ne, gabanin neman gurbin karatu a cikinta.

4• Abin Da Makarantar Ta Ke Buƙata Kafin Bada Admission :

Sanin kowa ne, makarantun Najeriya su na da mabanbantan abubuwan da su ke buƙata a kowacce gaɓa ga Ɗaliban da su ke nemansu, kafin basu guraben karatu, saboda haka ya na da kyau ku lura da abin da su ke buƙata, tare da auna kanku a mizanin cika ƙa'idojin nasu, kafin nema. Misali: wasu makarantun su na karɓar maki 200 ne a matsayin minimum Cut-Off mark; ya yin da wasu su ke karɓar maki 160 (za ku iya kwatanta abin da za su buƙata ne, ta hanyar duba Admission requirements ɗinsu na shekarar da ta gabata).

5• Ka fahimci tsarin Screening na makarantar :

Wasu daga cikin Makarantu, su na tantance sakamakon kammala Sakandire (O'Level Result) ɗin ɗalibi ne kawai, sai su bashi Admission (bayan ya kai Cut-Off mark ɗinsu), ya yin da wasu kuwa su ke gudanar da jarrabawar Post-UTME (Aptitude Test). Kun ga kenan, a wasu makarantun samun kyakykyawan sakamakon O'Level kawai ya wadatar a baka Admission, ya yin da a wasu kuwa, lamarin ya sha ban-ban.

6• Tsadar kuɗin makarantar :

Nasan ɗaliban da ke karanta wannan rubutu ganau ne, kan yadda tsadar kuɗaɗen Registration, ya raba ɗalibai da dama da makarantunsu, a kakar karatun da ta gabata, saboda haka akwai buƙatar ɗalibi ya binciki tsadar kuɗin registration na makarantar da ya ke son cikewa, dan ganin ko zai iya biya, ko akasin haka. Idan ya fuskanci kuɗin ya fi ƙarfinsa, sai ya sauya tunani zuwa wata makaratar.

DOMIN TAMBAYA, KO NEMAN SHIGA ASOF JAMB GROUP, KU TUNTUƁI WANNAN LAMBAR : 08039411956.

Rubutawa : Miftahu Ahmad Panda

08039411956.

16/01/2024

YADDA AKE RIJISTAR JAMB UTME (MATAKI BAYAN MATAKI)

• Bayan Ɗalibi, ya buɗe JAMB Profile, tare da mallakar Profile Codes, abu na farko da ya kamata ya yi, shi ne ya garzaya JAMB CBT Centre mafi kusa da shi, ɗauke da lambobin Profile Codes ɗin da aka turo masa; sakamakon kammala sakandire (idan ba awaiting result bane); da kuma kuɗin rijista Naira 6,200 (ga Ɗaliban da basa sha'awar rubuta jarrabawar Mock), ya yin da waɗanda ke son rubuta Mock kuma, za su je da Naira 7,700.

• Idan Ɗalibi ya je CBT Centre zai bada kuɗin rijistar da ya je da su, da kuma Profile Codes ɗin da aka turo masa ta Message, inda a nan ne za a yi amfani da lambobin wajen saya masa lambobin ePIN.

• Bayan an saya wa Ɗalibi ePIN, za a bashi JAMB Form ya cike bayanansa, wanda ya ƙunshi rukunoni biyar (A,B,C,D & E).

Bari mu ga bayanan da ake buƙata, a kowanne rukuni :

:

• Cikakken Suna.

• Kwanan Watan Haihuwa.

• Lambar Waya.

• Ƙaramar Hukuma.

•Jiha.

• Ƙasa.

• Profile Codes.

• ePIN.



• Akwai Buƙata Ta Musamman ?, Ko Babu ?.

• Adireshin Ɗalibi.

• Jiha, Da Garin Da Ɗalibi Ya Ke Son Rubuta Jarrabawarsa.

• Ɗalibi ya na da sha'awar rubuta jarrabawar MOCK, ko A'a ?.



A nan ne Ɗalibi zai zaɓi makarantu huɗu da ya ke so, tare da Courses ɗin da ya ke son karantawa, a makarantun (1st Choice, 2nd Choice, 3rd Choice, & 4th Choice).

Abin Lura: Ba lallai sai Jami'a Ɗalibi zai iya cikewa ba, A'a kowanne Ɗalibi ya na damar cike Jami'a, Kwalejin Ilimi, Kwalejin Fasaha (Polytechic), ko Monotechnic.



A nan ne Ɗalibi zai zaɓi darussan da ya ke son rubutawa a jarrabawarsa ta JAMB (Subject Combination).

Akwai buƙatar Ɗalibi ya nutsu sosai, wajen zaɓar Subjects Combination ɗinsa, domin kuskure a wannan mataki ya kan iya hana Ɗalibi samun Admission, duk yawan makin da ya samu a JAMB kuwa.

DUKKANNIN ƊALIBAN DA KE SON SANIN HAƘIƘANIN SUBJECTS COMBINATION ƊIN COURSE ƊIN DA SU KE SON CIKEWA, SU TUNTUƁI WANNAN LAMBAR : 08039411956.



Abin da ake buƙatar cikewa a wannan rukuni na E shi ne, sakamakon kammala Sakandire ɗin Ɗalibi, wanda ya haɗarda :

• Nau'in jarrabawar da ya yi (NECO, WAEC, NABTEB, ko NBAIS.

• Sunan Makarantar da ya yi jarrabawar.

• Shekarar da ya yi.

• Ta gwamnati ce, ko ta kuɗi ?.

• Da kuma lambar rijista (Registration Number).

∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆

Bayan Ɗalibi, ya cike dukkannin waɗannan bayanai, a jikin Form ɗin da za a bashi, Jami'an CBT Centre ɗin da ya halarta, za su shigar da bayanan a shafin hukumar JAMB; Sannan su ɗauki hoton ɗalibin; tare da Thumprints ɗinsa.

BAYAN ƊALIBI YA KAMMALA DUKKANNIN WAƊANNAN MATAKAN, SHIKENAN! YA KAMMALA RIJISTAR JAMB UTME.

√• Kafin Ɗalibi Ya Bar CBT Centre : ZA A BASHI REGISTRATION SLIP, NOVEL, DA CD.

Ga masu tambaya, ko neman shiga ASOF JAMB GROUP, kaitsaye su tuntuɓi wannan lambar : 08039411956.

Rubutawa : Miftahu Ahmad Panda

08039411956.

11/10/2022

HUKUMAR JAMB TA FARA BAYAR DA GURABEN KARATU NA KAKAR 2022/2023.

√• Za ku iya duba Uploading ɗin da aka yi muku, a yanzu.

•Hukumar JAMB ta buɗe sashen bada guraben karatu, na shafin ta (CAPS), tare da fara Aikin bada guraben karatu, ga ɗaukacin ɗaliban da makarantu s**a Aike da sunayen su, a kakar 2022/2023 da ake ciki.

A yanzu dai, ɗalibai za su iya halartar shafin na JAMB CAPS, domin dubawa, ko sun samu Admission (Admission Status). Ya yin da ake buƙatar su karɓa ko yin watsi da guraben karatun da s**a samu (Accept or Reject Admission).

•Akwai buƙatar ɗaliban da s**a rubuta jarrabawar JAMB UTME a wannan shekarar, ko kuma, suke neman guraben karatu ta hanyar shiga Jami'a kaitsaye (DE), su kasance masu yawan bibiyar shafin na JAMB CAPS (musamman waɗanda makarantun da suke nema s**a rubuta jarrabawar Post-UTME).

•Kada ɗalibi ya damu cewar makarantar da yake nema bata bashi Admission ba, dan haka bai da buƙatar duba Admission ɗinsa na JAMB, A'a, akwai buƙatar ɗalibai su kasance masu yawan bibiyar shafin nasu na JAMB CAPS, domin kuwa, makarantu da dama suna fara bayar da guraben karatu ne ta CAPS, kafin daga bisani, su ɗora Admissions ɗin a shafukan su.

√• Bugu da ƙari, su ma ɗaliban da s**a yi Uploading na sakamakon su na O'level ko A'Level, a yanzu suna da damar dubawa, ''Uploading ɗin nasu ya yi √'', ko akasin haka X.

Alƙalamin✍️ : Miftahu Ahmad Panda.

08039411956.

16/08/2022

Gwamnatin tarayya ta amince da tsarin biyan Albashi na ''UTAS'', wanda ƙungiyar ASUU ta gabatar ma ta.

✍️Panda

25/07/2022

SAƘON GAYYATA ZUWA ZANGA-ZANGAR LUMANA!!

Ƙungiyar Arewa Students Orientation Forum (ASOF), tana gayyatar ɗaukacin Membobinta na jihohin Arewa guda 19, da babban birnin tarayya Abuja, zuwa zanga-zangar lumanar da ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta shirya, da nufin bayyana fushinta kan Yajin Aikin ƙungiyar Malaman Jami'o'i (ASUU) da ya ƙi ci - ya ƙi cinyewa.

Za a gudanar da zanga-zangar ta kwanaki biyu ne, a gobe Talata da Jibi Alhamis, 26 da 27 ga watan Yulin da mu ke ciki, inda za a haɗu a Sakateriyoyin ƙungiyar ƙwadago na jihohi, da misalin ƙarfe 7:30 na safe.

ILIMI DAMAR MU CE, BA ALFARMA AKE MANA BA.

✍️Miftahu Ahmad Panda (Mataimakin Magatakardan ASOF na ƙasa).

08039411956.

21/06/2022

JAMB POLICY MEETING 2022

√• Ministan Ilimi, Mallam Adamu Adamu, ya amince da ranar Alhamis 21 ga watan Yuli (July) mai kamawa, a matsayin ranar gudanar da Policy Meeting na hukumar JAMB, wanda kuma a cikin sa ne za'a tsara yadda Admission ɗin shekarar da muke ciki ta 2022 zai kasance, tare da fitar da mafi karancin makin shiga Manyan Makarantun ƙasar nan (Minimum Cut-off mark).

~ Taron yana samun halartar Ministan Ilimi, Shugaban hukumar JAMB, Shuwagabannin Jami'o'i, tare da dukkannin masu ruwa da tsaki a fannin Ilimin ƙasar nan.

••• Kada dai ku manta, ana cigaba da Change Of Institutions •••

✍️Miftahu Ahmad Panda.

14/06/2022

JAMI'AR TARAYYA TA MAIDUGURI TA FARA SAKIN ADMISSION NA KAKAR KARATU NA 2021/2022

Muna sanar da ɗaukacin membobinmu da suke neman gurbin karatu a jami'ar tarraya ta Maiduguri (UNIMAID) ce wa jami'ar ta fara sakin gurbin karatu (admission) na kakar karatun 2021/2022.

Saboda haka muna shawartan ɗalibai da su yawaita ziyartar shafinsu na CAPS a taƙaice domin bincikawa da amincewa da karɓar gurbin karatun.

Za ku yi amfani da E-mail address da pasword da kuka yi amfani da shi yayin rijistar JAMB domin ziyartar shafinku na CAPS.

Fatan alheri.

Abdul-Azeez Bajoga
P.R.O
ASOF GOMBE STATE

06/06/2022

ASOF2022.

GOMBE STATE POLYTECHNIC BAJOGA (GSPB)

....SALES OF ADMISSION FORM FOR THE 2021/2022 ACADEMIC SESSION.

Makarantar Mai suna a sama tana sanar da dalibai masu sha'awar shiga makaranta cewa lokaci yayi da zasu dauki Dalibai domin fara Karatu a shekarar karatu na 2021/2022 a fanni daban daban da Courses din da suke dasu a Makarantar bayan samun dama da sahalewar Hukumar kula da Harkokin makarantun polytechnic na kasa wato National Board For Technical Education (NBTE).

Za'a cike tare da biyan kudin ne a Site din Makarantar ta yanar gizo in aka shiga www.gspb.edu.ng

Sauran Bayanai da Courses din yana tattare a takardan dake tare da wannan Rubutun wadda Makarantar ta fitar.

SIGNED:
U.M ALI (Nabeel Bajoga)
ASOF Gombe State Coordinator.

28/02/2022

AREWA STUDENTS' ORIENTATION FORUM GOMBE STATE CHAPTER

UNIVERSITY OF MAIDUGURI 2021/2022 ONLINE SCREENING

Jami'ar tarayya ta Maiduguri wato UNIMAID na sanar da dukkan ɗalibai da s**a zaɓi makarantar a zaɓin farko sannnan s**a samu maki 140 mafi ƙaranci a jarrabawarsu ta JAMB cewa za ta buɗe shafinta na post-UTME/online screening na kakar karatu ta 2021/2022 a yau Litinin, 28/02/2022 sannan zata rufe shi ranar 04/04/2022 wato za a ɗauki tsawon sati biyar ana wannan tantancewa ta yanar gizo. Adireshin shafin shi ne: http://putme.unimaid.edu.ng

Saboda haka muke tunatar da ɗaliban da suke neman gurbin karatu a wannan jami'a da su garzaya shagunan cafe mafi kusa da su domin wannan aiki. Hoton dake sama na ƙunshe da duk wani ƙarin bayani.

Abdul-Azeez Muhammad Adamu (Abdul-Azeez Bajoga)
P.R.O.
ASOF Gombe State Chapter
28.02.2022

ASOFB ONLINE MATHEMATICS COMPETITION in Bauchi 06/12/2021

MUHIMMIYAR SANARWA AKAN GASAR ASOF TA MATHEMATICS COMPETITION.

Har yanzu zaku iya neman shiga gasar Mathematics competition, daga yau har zuwa ranar 08/12/2021.

Sakamakon samun korafe korafe. Kungiyar ASOF ta sake bada damar shiga gasar mathematics competition.

Dukkannin daliban da suke da sha'awar shiga wannan gasa, za su iya shiga wannan link din da ke kasa, domin yin rijista, ta hanyar cike bayanan su 👇

https://asomc.websites.co.in

Ku sani akwai karramawa ta Award, da kuma muhimmiyar kyauta ga dukkannin wadanda s**a samu nasarar zama zakaru a wannan gasa, a yayin bikin cikar ASOF shekaru 6, wanda zai gudana anan gaba kadan.

Concern by
ASOF Mathematics competition committee

Signed by
Kabiru Dauda
ASOF COORDINATOR
BAUCHI STATE CHAPTER.

ASOFB ONLINE MATHEMATICS COMPETITION in Bauchi ASOFB ONLINE MATHEMATICS COMPETITION in Bauchi

11/10/2021

ASOF. Family . 6th Anniversary

December 2021

Kindly contact this Numbers 09037155972 or 08130040437 to get your own T- Shirt for ASOF. Family ahead of preparing ASOF. 6th Anniversary State.

Want your school to be the top-listed School/college in Gombe?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Telephone

Website

Address


Gombe