Musulunci rigar enci

Musulunci rigar enci Assalamualaikum warahmatullahi ta ala wa barkatu tsira da amincin Allah sutabbata ga shugaban halitta

18/04/2025

Allah kabamu Albarkacin manzon Allah sallallahu alaihi wasallam

Allah yajikanka yagafartamaka mai anguwa bappayo london mai dorowa gombe
18/04/2025

Allah yajikanka yagafartamaka mai anguwa bappayo london mai dorowa gombe

18/04/2025

Assalamua laikum warahmatullahi ta ala wabarkahu barkada ranar juma a

18/04/2025

Juma at mubarak

06/12/2023

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Sanusi Sani Aye, BN Hussein, Abdul Auwal, Umar Jafar, Umar Yusuf Chinade, Rabiu Abdullhamit, Zùlkìflù Æilù, Usman Abdulrahab, Kafin-Relatives Kafin-Relatives, Wuri Ontop Biu

S 💖 A 💖 W Allahumma salli ala Muhammad wa ala Ahli Muhammad k**a sallaita ala Ibrahima wa ala Ahli Ibrahima innaka hamid...
10/11/2023

S 💖 A 💖 W Allahumma salli ala Muhammad wa ala Ahli Muhammad k**a sallaita ala Ibrahima wa ala Ahli Ibrahima innaka hamidul majid Allahumma barik ala Muhammad wa ala Ahli Muhammad k**a barakta ala Ibrahima wa ala Ahli Ibrahima innaka hamidul majid sallallahu ta ala alaihi wasallam

13/02/2023
21/09/2022

MATSALOLIN ISTIMNA'I [MUSTURBATION]

Matsalolin da Istimina'i (Wasa da Al'aura) ke haddasawa.

Tare Da:- Sayyida Fatima S. Mai Yasin (Dual Scholar)

Kadan daga cikin illolin da istimna'i ke haifarwa ga wanda ya yi shi ko bayan an daina.

● Kankancewar zakari da maraina
● Saurin kawowa ko rashin karfin mazakuta
● Karancin maniyyi ko tsinkewar maniyyi.
● Yawan mantuwa
● Rage hazakar kwakwalwa
● Yana haddasa Mantuwa..
● Ramar jiki ko 'karancin sha'awa,
● Ya na iya haddasa rashin haihuwa ,
● Raunin jiki, raunin garkuwar jiki,
● Jin ciwon kai akai-akai, ciwon baya,
● Fitar maniyyi haka nan kawai.
● Bushewar fatar kan zakari.
● Kankacewar zakari ko sauya masa sigarsa
● Bugawar zuciya da sauri,
● Zubar gashi,
● Kurajen fuska da basu jin magani.

Wanda yakeyi ya daina, yayi addu'a, ya nemi yafiyar Ubangiji. Ba abune mai kyau ba. Bayan illoli akwai fushin Ubangiji.

Dafatan Allah Yakarawa Rayuwa Albarka

21/09/2022
21/09/2022

Hudubar Manzon Allah ﷺ Ga Musulmi Ta Qarshe A Ranar Arfa.

Annabi (S.A.W) Ya Fara Da Cewa:

Ya Ku Mutane Ku Bani Hankalinku, Domin Mai Yiwuwa Bazan Sake Kasancewa Da Ku Bayan Wannan Shekaran Ba, Saboda Haka Ku Saurari Abinda Nake Gaya Maku Da Kyau, Kuma (Ku Isar Da Abinda Zan Gaya Maku) Ga Wadanda Basa Wannan Wuri A Yau.

Ya Ku Mutane Kamar Yadda Kuka Riki Wannan Wata, (Na Hajji) Da Wannan Rana (Ta Arfa) Da Kuma Wannan Gari (Na Makka) Da Girma Kuma Abin Tsarewa, To,

Haka Kuma Ku Riki Ran Musulmi Da Kuma Dukiyoyinsu Da Girma Abin Kuma Karewa, Ku Maida Wa Mutane Kayan Da S**a Baku Amana.

Kar Ku Cuci Kowa, Saboda Kar Wasu Su Cuce Ku, Ku Tuna Fa,

Hakika Allah Zai Yi Sakayya Akan Ayukkanku, Allah (Swt) Ya Hana Cin Riba,(Wato Kudin Ruwa) Saboda Haka, Duk Abin Da Aka Kulla Ta Kudin Ruwa Sai An Warware Shi.

Ku Yi Hattara Da Shaidan, Domin Kiyaye Addininku. Yanzu Kan Ya Fidda Ran Batar Da Ku Akan Manyan Abubuwa (Na Sabo) Saboda Haka Ku Guji Binshi Akan Kanana.

Ya Ku Jamaa Hakika Kuna Da Hakki Bisa Matayenku, Kuma Suma Suna Da Hakki Bisa Kanku, To Hakkin Su Ne Akanku Da Kuciyar Dasu, Kuma Ku Tufatar Dasu Akan Jin Kai.

Ku Bi Dasu Kyakkyawan Biyarwa, Ku Kuma Tausasa Musu Domin Su Majibintan Al Amurran Kune, Kuma Mataimakan Ku, Hakki Ne Akansu Da Kar Su Yi Abota Da Duk Wanda Bakwa So, Kuma Su Nisanci Zina.

Ya Ku Jama'a Kuyi Kyakkyawan Bauta Ga Allah (SWT) Ku Tsaida Salloli Biyar (5) Na Farilla, Ku Azumci Watan Ramadan Ku Kuma Bada Zakka.

Ku Aikata Aikin Hajji In Har Kun Sami Daman Yi.

Ku Sani Fa, Ko Wane Musulmi Dan Uwan Musulmi Ne.

Dukkan Ku Dai Dai Kuke. Ba Wanda Yake Da Fifiko Saman Wani Sai Ta Tsoron Allah, Da Aikata Kyawawan Ayyukka.

Ku Tuna Fa (Ya Ku Jama'a) Wata Rana Za Ku Tsaya Gaban Ubangijinku, Domin Sak**akon Ayyukanku, Saboda Haka Ku Yi Hattara Kada Ku Yi Sake Da Hanya Madaidaiciya Bayan Na Kau.

Ya Ku Jama'a Ba Wani Annabi Ko Manzo Da Zai Zo Bayana Kuma Babu Wani Addini Da Zai Zo (Bayan Addinin Musulunci)

Saboda Haka Kuyi Tunani Sosai Akan Wannan Magana.

Dafatan Allah Yakarawa Annabi Muhammadu Daraja

Address

Gombe

Telephone

+2349061436183

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Musulunci rigar enci posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The School

Send a message to Musulunci rigar enci:

Shortcuts

Share

Category