Gaya Educational Development Association-GEDA

Gaya Educational Development Association-GEDA Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Gaya Educational Development Association-GEDA, Educational Research Center, Gaya Local Government, Gaya.

08/12/2024

Hello

12/03/2024
GAYA EDUCATIONAL DEVELOPMENT ASSOCIATION - GEDAA kokarin bunkasa ilimi a fadin karamar hukumar Gaya da wannan kungiyar m...
04/03/2024

GAYA EDUCATIONAL DEVELOPMENT ASSOCIATION - GEDA

A kokarin bunkasa ilimi a fadin karamar hukumar Gaya da wannan kungiyar mai albarka take yi ta fara gabatar da extra-lesson ga daliban da suke kokarin rubutu jarrabawar JAMB ta bana a makarantar special primary school dake kofar gidan mai martaba Sarkin Gaya.
Muna fatan Allah swt ya taimaki wadannan dalibai da sauran yan uwa yan gwagwarmaya da suke wannan kokarin Allah ka biya musu duk bukataunsu albarkacin shugaban halitta S A W.

Daga
P.R.O
Sulaiman Balarabe Hassan
Yusuf Muhammad Makama

ZIYARAR DA KUNGIYAR GAYA EDUCATIONAL DEVELOPMENT ASSOCIATION-GEDA TA KAI GOVERNMENT GIRLS SECONDARY SCHOOL RINDA-TOZO (G...
16/02/2024

ZIYARAR DA KUNGIYAR GAYA EDUCATIONAL DEVELOPMENT ASSOCIATION-GEDA TA KAI GOVERNMENT GIRLS SECONDARY SCHOOL RINDA-TOZO (GGASS R/TOZO) DON BAWA DALIBAI SHAWARWARI DANGANE DA JARRABAWAR JAMB DSS.

A ranar laraba 14-02-2024 kungiyar GEDA karkashin jagorancin mataimakin shugaban kungiyar,Comr.Aminu Sarki s**a kaiwa makarantar Government Girls Arabic Secondary School Rinda-tozo (GGASS R/TOZO) domin bawa daliban makarantar dabarun yanda ake fuskantar ire-iren wadannan jarabawar.
Daya daga cikin mahalarta wannan makaranta ya yiwa dalibai nasiha dangane da su rinka bawa lokaci muhimmanci domin duk abin da aka saka masa lokaci hakika ana tsammanin kowa zai halarta kafin wannan lokacin.
Dadin dadawa mun jiyo wani mai maganar yana bawa daliban shawara dangane da ilimi a matsayinsa na ginshikin rayuwar dan'adam shima ya bawa daliban shawarwari dangane da yin biyayya ga malamai domin sune silar zaman duk wani abun da mutum ya zama.
A wannan ziyarar ne aka fedewa dalibai me ake nufi da jarrabawa sannan akayi musu bayanin menene ma'anar JAMB da UTME,sannan yayi kokarin fito musu da yadda ake pre-registration na jamb sannan ya basu shawarwari game da course din da ya kamata mutum ya cike da combination dinsu daga karshe ana yi kira ga daliban su kasance a cikin karatu ko da yaushe domin samun nasarar cimma kudurinsu a rayuwa.

Daga karshe hukumar makaranta ta yi murna sosai da wannan ziyarar da wannan kungiyar mai albarka ta GEDA tayi musu inda s**a yi ma kungiyar fatan alkhairi da fatan samun abun da s**a saka a gaba.

Amadadin Shugaban wannan kungiyar COMR.AMINU MUHAMMAD YUSHA'U muna mika sakon godiyarmu ga daukacin malamai da dalibai na wannan makaranta mai albarka bisa goyon bayan da s**a bamu da hadin kai don ganin an yi abin cikin tsari Alhamdulillah anyi lafiya an gama lafiya.




from
Office of Chairman
Comr.Aminu Muhammad Yusha'u

Through!
Office of
P.R.O
Sulaiman Balarabe
Yusuf Muhammad Makama

16-Feb,2024M
08-08-1445H

09/02/2024

SHUGABANCIN KUNGIYA

SOON INSHA ALLAHU

GAYA EDUCATIONAL DEVELOPMENT ASSOCIATION-GEDASAKON BARKA DA JUMA'A!!!Karkashin jagorancin Shugaban wannan kungiyar mai a...
09/02/2024

GAYA EDUCATIONAL DEVELOPMENT ASSOCIATION-GEDA

SAKON BARKA DA JUMA'A!!!

Karkashin jagorancin Shugaban wannan kungiyar mai albarka ta GEDA Comr. Aminu Muhammad Yusha'u da sauran jagororin ta suna mika sakon barka da juma'a ga daukacin jama'ar wannan gari namu mai albarka na Gaya.
Sannan suna kira ga mutane a dage da addu'ar zaman lafiya ga garinmu da ma kasa baki daya.

Daga karshe sunyi addu'ar wannan kuncin da tsananin da alummar Kasata suke ciki Allah ya kawo musu dauki bi-jahi sayyyadil Anami (S.A.W)

from
Office of Chairman
Comr. Aminu Muhammad Yusha'u

Through!
Office of
Public Secretary
Sulaiman Balarabe Hassan
Yusuf Muhammad Makama

ZIYARAR DA KUNGIYAR GAYA EDUCATIONAL DEVELOPMENT ASSOCIATION-GEDA TA KAI MAHMUD AMIN MODEL TAHFIZUL QUR'AN DON BAWA DALI...
06/02/2024

ZIYARAR DA KUNGIYAR GAYA EDUCATIONAL DEVELOPMENT ASSOCIATION-GEDA TA KAI MAHMUD AMIN MODEL TAHFIZUL QUR'AN DON BAWA DALIBAI SHAWARWARI DANGANE DA JARRABAWAR JAMB DSS.

A jiya litinin 05-02-2024 kungiyar GEDA karkashin jagorancin Comr.Aminu Sarki s**a kaiwa makarantar Mahmud Amin Tahfizul Qur'an wacce take a Dun-Dun domin bawa daliban makarantar dabarun yanda ake fuskantar ire-iren wadannan jarabawar.
Daya daga cikin mahalarta wannan makaranta ya yiwa dalibai nasiha dangane da su rinka bawa lokaci muhimmanci domin duk abin da aka saka masa lokaci hakika ana tsammanin kowa zai halarta kafin wannan lokacin.
Dadin dadawa mun jiyo wani mai maganar yana bawa daliban shawara dangane da ilimi a matsayinsa na ginshikin rayuwar dan'adam shima ya bawa daliban shawarwari dangane da yin biyayya ga malamai domin sune sababin zaman duk wani abun da mutum ya zama.
A wannan ziyarar ne aka fedewa dalibai me ake nufi da jarrabawa sannan akayi musu bayanin menene ma'anar JAMB da UTME,sannan yayi kokarin fito musu da yadda ake pre-registration na jamb sannan ya basu shawarwari game da course din da ya kamata mutum ya cike da combination dinsu daga karshe ana yi kira ga daliban su kasance a cikin karatu ko da yaushe domin samun nasarar cimma kudurinsu a rayuwa.

Daga karshe hukumar makaranta ta yi murna sosai da wannan ziyarar da wannan kungiyar mai albarka ta GEDA tayi musu inda s**a yi ma kungiyar fatan alkhairi da fatan samun abun da s**a saka a gaba.

Amadadin Shugaban wannan kungiyar COMR.AMINU MUHAMMAD YUSHA'U muna mika sakon godiyarmu ga daukacin malaman wadannan makaranta mai albarka bisa goyon bayan da s**a bamu da hadin kai don ganin an yi abin cikin tsari Alhamdulillah anyi lafiya an gama lafiya.




from
Office of Chairman
Comr.Aminu Muhammad Yusha'u

Through!
Office of
P.R.O
Sulaiman Balarabe
Yusuf Muhammad Makama

6-Feb,2024M
26-07-1445H

Address

Gaya Local Government
Gaya

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Gaya Educational Development Association-GEDA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share