18/11/2023
YADDA AKE ISTIKHARA (ISTAHARA)
Da farko dai ita sallar istikhara ba Wani Abu bane illa neman zaɓin Allah mafi alkhairi akan Duk Wani abinda aka saka a gaba yadda kuma ake yinta shine za'ayi sallah ne raka'a biyu (2) kowace raka'a kuma za'a karanta fatiha da sura,
Idan anzo tahiya kuma bayan ka gama karatun tahiyar sai kayi salatin Annabi saw sai ka karanta wannan addu'ar Kamar haka
(ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﻲ ﺃﺳﺘﺨﻴﺮﻙ ﺑﻌﻠﻤﻚ، ﻭﺃﺳﺘﻘﺪﺭﻙ ﺑﻘﺪﺭﺗﻚ،
ﻭﺃﺳﺄﻟﻚ ﻣﻦ ﻓﻀﻠﻚ ﺍﻟﻌﻈﻴﻢ ﻓﺈﻧﻚ ﺗﻘﺪﺭ ﻭﻻ ﺃﻗﺪﺭ، ﻭﺗﻌﻠﻢ
ﻭﻻ ﺃﻋﻠﻢ، ﻭﺃﻧﺖ ﻋﻼﻡ ﺍﻟﻐﻴﻮﺏ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻥ ﻛﻨﺖ ﺗﻌﻠﻢ ﺃﻥ
ﻫﺬﺍ ﺍﻻﻣﺮ,
Anan Sai ka fadi kalar buƙatar da kake neman zaɓin mafi alkhairi a wajrn Allah (SWT), Sai Kaci gaba da faɗin
ﺧﻴﺮ ﻟﻲ ﻓﻲ ﺩﻳﻨﻲﻭﻣﻌﺎﺷﻲ ﻭﻋﺎﻗﺒﺔ ﺃﻣﺮﻱ ﻓﺎﻗﺪﺭﻩ ﻟﻲ ﻭﻳﺴﺮﻩ ﻟﻲ ﺛﻢ ﺑﺎﺭﻙ
ﻟﻲ ﻓﻴﻪ، ﻭﺇﻥ ﻛﻨﺖ ﺗﻌﻠﻢ ﺃﻥ ﻫﺬﺍ ﺍﻻﻣﺮ ﺷﺮﻟﻲ ﻓﻲ ﺩﻳﻨﻲ
ﻭﻣﻌﺎﺷﻲ ﻭﻋﺎﻗﺒﺔ ﺃﻣﺮﻱ ﻓﺎﺻﺮﻓﻪ ﻋﻨﻲ ﻭﺍﺻﺮﻓﻨﻲ ﻋﻨﻪ
ﻭﺍﻗﺪﺭﻟﻲ ﺍﻟﺨﻴﺮ ﺣﻴﺚ ﻛﺎﻥ ﺛﻢ ﺭﺿﻨﻲ ﺑﻪ)
"Allahumma inni astakhiruka bi'ilmika , Wa astaqdiruka bi - qudratika, Wa as'alaka min fadlika al -azim Fa-innaka taƙdiru Wala aƙdiru, Wa ta'alamu Wala a'alamu, Wa anta' allamul-ghuyub. Allahumma, in kunta taʼlamu anna hadhal - amra
Anan Sai ka fadi kalar buƙatar da kake neman zaɓin mafi alkhairi a wajrn Allah (SWT), Sai Kaci gaba da faɗin
Khairun-li fi dini wa ma'ashi wa'aƙibatil amri (ajili amri wa'ajilihi ) Fakdirhu wa yassirhu li thumma barik li Fihi, Wa in kunta ta'lamu anna hadha-lamra shar-run li fi dini wa ma'ashi wa'aƙibati amri (fi'ajili amri wa ajilihi) Fasrifhu anni wa srifni anhu. Waƙdirli al-khaira haithu kana Thumma ardini bihi.
Bayan nan Sai kayi sallama, shikenan.
Amma Anaso Idan anyi a ƙara maimaitawa gwargwadon yadda aka samu iko.
Masu kuma tambayar me zasu gani idan sunyi istihara??
Amsar shine ba'a ganin komai sai abinda Allah yaso, Amma idan kayi to yadda zaka gane alkairi ne ko akasin haka shine, (idan alkairi ne zakaji son Abin ya ƙaru a zuciyar ka, Dan haka sai ka ƙara himma wajan aikatawa, idan Kuma ba alkairi bane sai kaji son Abin yana raguwa a cikin zuciyar ka daga nan Sai Kayi ƙoƙarin barin Abin.)
Addu'ar da zaka