Today been last Friday of de month we pray to see next Ramadan may Allah SWT accept our ibadah and grant all de Muslim Ummah Jannatul Firdaus Aameen ya Allah 🙏🏽
Institute of Qur'anic studies funtua
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Institute of Qur'anic studies funtua, Education, Katsina Road Dutsen reme, Funtua.
Salam Ina ma Yan uwa barka da safiyar laraba alkhairi da ke ciki Allah ya hada mu da shi sharrin da ke ciki Allah ya Kare mu daga gare shi
01/02/2022
NASIHA MAI MATUƘAR TSADA DA MUHIMMANCI GA MASU SAKIN BAKINSU GA CIN MUTUNCIN SHUGABANNI:
Abudullahi bnu Aun ya hakaito cewa: ya je wajan Muhammad bnu Siriin (ɗaya daga cikin ginshiƙan tabi`ai guda huɗu) sai ya ambaci wasu munanan halaye na Hajjaj bnu Yusuf (Wani azzalumin sarki da aka taɓa yi a zamaninsu) a gabansa.
Sai Ibnu Siriin ya ce da shi:
إن الله ينتقم للحجاج كما ينتقم منه وإنك إذا لقيت الله غدا كان أصغر ذنب أصبته أشد عليك من أعظم ذنب أصابه الحجاج. فيض القدير (1/ 116)
Allah fa zai saka wa Hajjaj (zaluncin da mutane s**a yi masa) kamar yadda zai sakawa mutane zaluncin Hajjaj a kansu. Kuma ka sani idan ka haɗu da Allah mafi ƙanƙantar laifin da ka aikata ya fi tsanani a kanka fiye da mafi girman laifin da Hajjaj ya aikata.
Abin nufi da wannan nasiha ta Ibnu Siriin shine: Ko da shugaba ya zama azzalumi hakan ba ya halasta maka shiga huruminsa da cin mutuncinsa ba tare da haƙƙi ba.
Idan kuwa ka ci mutuncinsa to haƙƙinsa yana kanka, ranar alƙiyama Allah zai titsiyeka ya ƙwatar masa haƙƙinsa kamar yadda shima za a titsiye shi a ƙwatarwa al`ummar da ya mulka ya zalunta haƙƙinsu, don Allah ba azzalumin sarki ba ne.
Ibnu Siriin ya ci gaba da cewa Ibnu Aun: ka ji da kanka don a ranar lahira ɗan ƙaramin laifinka sai ya fi damunka fiye da babban laifin shugabanka, don laifinka shi za a tambaye ka ba laifin shugabanka ba.
ِAlmunawy ya yi tsokaci kan wannan magana ta Ibnu Siriin da cewa:
فمن ذكر واحدا من هذا الصنف تشفيا لغيظه أو انتقاما لنفسه أو احتقارا أو ازدراء ونحو ذلك من الحظوظ النفسانية فهو آثم. فيض القدير (1/ 116)
Ma`ana: Wanda ya amabaci wani abu na aibukan wani fajiri don huce haushi ko don ɗaukar fansa ko don raini ga mai wannan siffar ko don wani abu na buƙatun ƙashin kai (kamar masu s**an shugaba don manufa ta siyasa ba don maslahar al`umma ba) to shi mai laifi ne.
Don haka dan uwa yi ƙoƙari ka damu da zunubanka fiye da damuwarka da surutu kan zunuban shugabanni, don ranar alƙiyama kanka za ka kare ba su ba.
Yi wa kanka ƙiyamullaili kada ka je a tsare shugaba bayan an ƙwato haƙƙinka daga gareshi kai kuma a ce ka ba shi nashi haƙƙin na zaman zagi da cin mutunci da kake masa, wata kila a wajan kakara ciko ya biyo gyartai, kana tsammanin ka hango shugabanka a hanyar Jahannama sai a samu akasi duk zunuban na sa kai da ire-irenka kun riga kun kwashe masa ya shige aljanna ya barku kuna hamma.
✍ Allemawy
Institute of Qur'anic studies funtua Education
🌲🌼NURUL HUDA🌼🌲
بسم الله الرحمن الرحيم
الحمدلله رب العالمين والصلاة والسلام على سيدنا محمد خايم النبيين وإمام المر ساين وعلى آله وصحبه أجمعين
Da sunan Allah me rahama mejinkai.
Godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai
Tsira da Aminci su kara tabbata agurin shugaban mu ANNABI MUHAMMAD cika Makin annabawa Kuma shugaban manxanni da iyalansa da sahabansa baki daya.
(حصن المسلم) من اذكارالكتاب والسنه
Garkuwar musulmi daga addu'o In Alqur'ani da sunnah
بسم الله الرحمن الرحيم
((فاذكروني أذكركم واشكرولي ولاتكفرون))
Ku ambaceni xan ambace ku ku gode mini kada ku kafircemini(baqara 152)
((يأيها الذين آمنوا اذكر الله ذكرن اً كثيراً وسبحوه بكرة واصيلا))
Yaku wadanda s**ai emani ku ambaci Allah ambato meyawa
((الذاكرين الله كثيراً والذاكرات اعدالله لهم مغفرة واجراًعظيما))
Da masu ambaton Allah da yawa maxa da masu ambaton Allah da yawa mata Allah ya tanadar masu gafara da lada mai girma (ahxab 35)
((واذكر ربك في نفي نفسك تضرعا وخيفة ودون الجهر من القول باالغدووالآصالولاتكن من ألجأ هلين))
Kuma ka ambaci ubangijin ka a cikin xuciar ka kana me qanqan da kai da tsoro bada daukaka murya bah da safe da yamma Kuma kada kaxamo daga cikin gafalallu(A'araf 205)
Oh Allah! Only You Know The Secret Of Our Hearts. Accept Our Silent Wishes & Supplications, Save Us From The Torment Of Hell Fire, Give Us Good in This World & in The Hereafter, Forgive Us Our Sins, Forgive Our Parents and Also Our Loved Ones, Protect Us From Shaytaan & All Evils And Make Jannatul Firdausi Our Final Destination.
Allahumma aamin 🤲🏻🤲🏻🤲🏻
Salam yan uwa da fatan kun tashi lfy alkhairi da ke cikin wannan yinin Allah ya hada mu da shi sharrin kuma Allah ya zare mu daga gare shi
SALAM YAN UWA BARKAN MU DA WANNAN RANA TA JUMAA ALLAH YA SADA MU DA ALKHAIRAN DA KE CIKIN TA AMEEN
05/06/2020
Salam yan uwa da fatan kun sha ruwa lfy
Click here to claim your Sponsored Listing.
Location
Category
Website
Address
Katsina Road Dutsen Reme
Funtua