Litattafan Hausa

Litattafan Hausa

Share

Munbude wannan gidane don musanar da daku ta yadda addinin islama yazo kasar Hausa

22/03/2026

MATSATSUBI CIGABAN KUNDIN TSATSTUBA 12
Abdulaziz Sani M Gini
A baya mun tsaya ne a inda ake zayyana bayani akan gimbiya Luzaiya😏😏:-
Tana da ƙwala-ƙwalan idanu a ƙarƙashin gira mai ƙyallin baƙi kuma sun kasance masu haske sosai, hancinta dogone siriri k**ar alƙalami a ƙasansa an dasa mata ƙaramin baki mai ban sha'awa.(🙄🙄🙄🙄 wannan bayani haka 🙄🙄).
ldan tayi murmushi sai kaga k**ar kyawun nata ya linka kansa.(Wata sabuwa😝😝😂).

# # # # #
Tana tafe a hankali cikin izza ta iso gaban mahaifinta shi kuwa sai ya miƙe ya tare ta sannan ya k**a hannunta na dama ya sumbaci kan yatsunta sannan ya zaunar da ita kusa dashi suna masu duban juna cikin murmushi da nuna zunzurutun ƙauna.
Luzaiya tace "Ya kai Abbana ina can gidana yanzu ina shirin fita rangadi bayan gari sai ga saƙonka ya riskeni cewar na dakatar da fita shin lafiya kuwa?"
Sarki Fahalul Bahafus yace "E, to lafiyar kenan amma ba ƙalau ba. Abin da yasa nace ki fasa fita shine labari yazo mini cewa rundunar mayaƙa ta sauka a bayan gari kuma ba'a san me ya kawo suba.
Don haka yanzu na tura aje aji dalilin zuwansu ƙasata."
Koda jin haka sai Luzaiya tayi murmushi tace "Ai koma dame s**a zo dai dai muke dasu, ya kai Abbana ni kam nasan cewa a halin yanzu yadda kake da tarin gwarzaye mayaƙa babu wata runduna da zata iya cin mu da yaƙi."
Sarki ya ƙyalƙyale da dariya yace, "Tabbás haka zancenki yake 'yata domin inda na kasance azzalumi da tuni yanzu na mallaki duk ƙasashen dake maƙwabtataka damu." Sarki na gama faydin haka kenan sai ga Jambu ya dawo ɗauke da wasiƙa,da zuwa sai ya miƙa takardar ga sarki shi kuma ya baiwa magatakarda ya umarceshi daya karanta ta.
Take magatakarda ya warware ya fara bayani k**ar haka:-
"DAGA JARUMI NAZMIR BIN HALUFA ZUWA GA SARKI FAHALUL BAHAFUS NA BIRNIN MAHAZÜS.
GAISUWA TARE DA BIYAYYA A GAREKA YAKAI WANNAN SARKI, KAYI SANI CEWA NI MANZO NE DAGA SARKI BASHAKUR NA BIRNIN DAHAMUL KUMA BAI TURONI GARE KA DAN KOMAI BA SAI DON NA YANKE KANKA NA KAI MASA KUMA NA TAFI DA KYAKKYAWAR 'YARKA GIMBIYA

14/03/2023

ASKIYA MUHAMMADU EL-TURE
****************************

A zamanin da, an yi wani sarki da ya shahara kwarai da gaske a wata daula da ake kira songhai a nahiyar Africa ta yamma. Ana kiransa ASKIYA MUHAMMAD NA DAYA. Amma sunansa na asali shine Muhammad El-Ture.
Shi wannan sarki dai da karfin tuwo ya kwace sarautar daular songhai daga hannun wani dan sarki da ke kujerar mulki.
Kasar songhai wata daula ce da ta mamaye kudancin sahara tun daga kasar Senegal har zuwa kasar Hausa, ta wuce ta shiga kasar cadi.
Daular ta fara kafuwane daga wani gari da ake kira Gao a gabar kogin kwara a cikin kasar mali.
Dalilin da ya kawo bunkasar wannan daular kuwa shine, a lokacin da sarkin Gao da ake kira Sonni Ali ke mulki sai wani sarki makwabcinsa da ke sarauta a Tambutu wanda ake kira da Umaru ya aikawa Sonni Ali da sakon ya turo masa da taimakon mayaka, saboda kafirai sun kawo wa kasarsa hari.
Ko da yake Sonni Ali musulmine kuma bai damu da aikin musulunci sosai ba, amma duk da haka ya ji kiran da sarki Umaru ya yi masa, ya kuma kai masa taimako har aka ci nasara; wannan nasarar ita ta ba Sonni Ali damar ya kai wa garin jenna da kuma sauran kasashe hari. Burinsa kuwa shi ne ya fadada babbar daula inda zai shinfida mulkinsa.
Daular songhai dai ba a san sahihin tarihinta ba sai lokacin da Addinin Musulunci ya shigo kasar. Watau malaman Alqur'ani ne s**a fara rubuta tarihinta.

Sarki na farko da yafa shiga addinin musulunci a kasar shine wanda ake kira, Za kosoi. Da ya musulunta sai mutanensa masu yawan gaske s**a shiga addinin Musulunci tare da shi.

Mutanen songhai yawancinsu manoma da masunta da 'yan kasuwa ne.
A lokacin da Sonni Ali ke mulkin kasan songhai, Askiya Muhammad shi ne wazirinsa, kuma babban amininsa. Ko da yake suna da bambancin ra'ayi.


Zamu kwana anan zamu tashi

Kafin kafin ASKIYA MUHAMMAD ya zamasarki

13/03/2023

Gobe insha Allah

LABARIN ASKIYA MUHAMMAD ZAI DORA DAGA INDA AKA TSAYA A BAYA

13/03/2023

Gobe zamuci gaba da karatun littafin na mijin duniya insha

20/03/2021

Zamu ci gaba da karatun litattafin askiya a Ranar talata insha Allah

28/11/2020

CIGABA
Ko da yake Sonni Ali musulmi ne kuma bai damu da aikin musulunci sosai ba,amma duk da haka ya ji kiran da sarki umaru ya yi masa,ya kuma kai masa taimako har akaci nasara;wannan nasara ita ta ba Sonni Ali damar ya kai wa garin Jenna da kuma sauran kasashe hari.burinsa kuwa shi ne ya fadada babbar daula inda zai shinfida mulkinsa.
Daular Songhai dai ba a San sahihin tarihinta ba sai lokacin da addinin musulunci ya shigo kasar.watau malaman alkur'ani ne s**a fara rubuta tarihinta
Daga Dan uwanku Yusuf Muhammad sani R/lemo
Muhadu a gobe in Allah ya kaimu

22/11/2020

Kasar Songhai wata daula ce da ta mamaye kudancin sahara tun daga kasar Senegal har zuwa kasar Hausa,ta wuce ta shiga kasar cadi.
Daular ta fara kafuwa ne daga wani da ake kira gao a gabar kokin kwara a cikin kasar Mali.
Dalilin da ya kawo bunkasar wannan daular kuwa shine,a lokacin da sarkin gao da ake kira Sonni Ali ke mulki sai wani sarki makwabcinsa da ke sarauta a tambutu Wanda ake kira umaru ya aika wa Sonni Ali da sakon ya turo masa da taimakon mayaka,saboda kafirai sun kawo wa kasarsa hari. Muhadu a gaba

17/11/2020

ASKIYA MUHAMMADU EL-TURE
Azamanin da an yi wani sarki da ya shahara kwarai da gaske a wata daula da ake kira Songhai a nahiyar afrika ta yamma ana kiransa ASKIYA MUHAMMADU NA DAYA . Amma sunansa NA asali shine Muhammad el-ture
Shi wannan sarki dai da karfin tuwo ya kwace sarautar daular Songhai daga hannun wani Dan sarki da ke kujerar mulki.

Photos from Litattafan Hausa's post 15/11/2020

ZAMU FARA DA NAMIJIN DUNIYA LABARIN ASKIYA MUHAMMADU
NA MUHAMMAD SARKI

Want your school to be the top-listed School/college in Festac Town?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Address


Festac Town