Madinatul Ahbab

Madinatul Ahbab Qur'an, Hadith, Sira, Fiqh, Sunnah, Tafsir, and Shari'a

Alhamdulilah
11/06/2024

Alhamdulilah

27/12/2017

Click Here to Download Haba Jama'a Musa Lura Fadar Bege

26/04/2017

Babu laifi a yi gwajin Genotype, ya ma inganta Manzon Allah SAW Ya yi umurni da abu mak**ancin haka, sannan idan ya bayyana akwai qaqqarfar...

25/04/2017

Akwai Hadisai da dama wayanda Abu Dawoud da Ibn Majah da Dabarani da wasunsu sun ruwaito cewa kada a mayar da hannu sai an shafa fuska amma...

12/04/2017

Hukumar Custom tana yin gwanjo ne na kayan da ta kwace a hannun wadanda s**a karya dokokin shiga da ficen kayayyaki k**an yarda doka ta tan...

10/02/2017

Fasali a cikin bayanin TSARKI (rabe raben tsarki)
http://madinatulahbab.blogspot.nl/2015/11/fasali-cikin-bayanin-tsarki-rabe-raben.html

JANABA ta kasu kaso biyu
http://madinatulahbab.blogspot.nl/2016/01/janaba-ta-kasu-kashi-biyu.html

Niyyar wankan tsarki
http://madinatulahbab.blogspot.nl/2014/04/niyyar-wankan-janabahaidanifasi-dana.html

Hukunce Kukuncen wankan JANABA Farillai Sunnoni da Mustahabbai
http://madinatulahbab.blogspot.nl/2016/01/wankan-janaba-farillai-sunnoni-da.html

WANKAN JANABA
http://madinatulahbab.blogspot.nl/2014/04/wankan-janaba.html

Banbanci tsakanin Maniyyi, Maziyyi, Wadiyyi da Hukunce Hukuncen su
http://madinatulahbab.blogspot.nl/2016/10/banbanci-tsakanin-maniyyi-maziyyi.html

Idan anga gyara ko kuskure ko za'ayi karin bayani ko ana neman karin bayani a tuntubemu ta: [email protected]

Madinatulahbab.blogspot.com

15/01/2017

HADISI NA FARKO: MANZON ALLAH (S.A.W) ya na cewa Wanda ya karanta Qulhuwallahu Ahad kafa 10x ALLAH ya yi masa Alkawarin zai gina masa ...

14/10/2016

Hadith: abdalul a'a mali ilallahi husnu zanni ala ibadillahi, Wa sharrul a'a mali ilallahi su'uzzanni ala ibadillahi.

Fassara: Aikin daya fi fifikon daraja a wurin ubangiji shine kyautata zato (ko kuma kyakykyawan zato) a bisa bayin ALLAH, aikin dayafi zama mafi sharri a wurin ubangiji munana zato ga bayin ALLAH

BANBANCI TSAKANIN MANIYYI, MAZIYYI, WADIYYI, DA KUMA HUKUNCE-HUKUNCEN SUWajibine kowani baligi ko baliga su san hukunce-...
13/10/2016

BANBANCI TSAKANIN MANIYYI, MAZIYYI, WADIYYI, DA KUMA HUKUNCE-HUKUNCEN SU

Wajibine kowani baligi ko baliga su san hukunce-hukuncen su domin gyara ibadunsu.

HUKUNCIN FITAR MANIYYI shine: fitowar sa tana wajabta wankan janaba akan namiji ko mace.

LAUNIN MANIYYIN NAMIJI: ruwane mai kauri fari wanda yake fitowa yayin babbar sha'awa k**ar saduwa, ko wasa da zakari. Sannan yana tunkudo juna lokacin dayake fitowa, kuma warinsa yana k**a da warin hudar dabino, ko damammen gari, idan ya bushe yana kamshin kwai.

LAUNIN MANIYYIN MACE: Ruwane tsinkakke, mai fatsi-fatsi, Wani lokacin kuma yana zuwa fari, wanda yake fitowa yayin babbar sha'awa k**ar saduwa, ko wasa da farji. Sannan yana tunkudo juna lokacin da yake fitowa. Kuma warinsa yana k**a da warin hudar dabino ko damammen gari, idan ya bushe shima yana kamshin kwai.

HUKUNCINFITAR MAZIYYI: hukuncin sa shine a wanke farji gaba daya, da kuma inda ya shafa, kuma a sake alwala.

LAUNIN MAZIYYI: Ruwane tsinkakke da yake fitowa, yayin karamar sha'awa, k**ar tunanin aure ko kuma tuna wacce kakeso, ko matarka, ko kallon matar ko namijin da k**e sha'awa. Haka kuma yana fitowa yayin wasa tsakanin miji da mata, saidai shi baya tafiyarda sha'awa, kuma wani lokacin ba'a sanin yafito.

Malamai suna cewa, Maziyyi yafi fitowa mata, fiye da maza.

HUKUNCIN WADIYYI: wadiyyi yana daukar hukunce-hukuncen fitsari ne.

WADIYYI: Wani ruwane mai kauri dayake fitowa a karshen fitsari, ko kuma karshen bahaya ga wanda ya jima bai yiba, yana fitowa ga wadanda ba suda aure, ko wadanda s**a yi nisa da abokin
rayuwarsu ta aure, ina nufin namiji ko mace.

Amman fa ku sani komai saida niyya
madinatulahbab.blogspot.com

ALLAH S.W.T shine mafi sani!!!

04/07/2016

HUKUNCIN ZAKKAR FIDDA KAI TA KARSHEN RAMADAN.

Atakaice malamai Sun kasu izuwa makarantu uku kofahimta uku.

1- bai halatta ba sam Sam afitar da ita da kudi saboda ba haka ANNABI yace ayiba. Ra'ayin mazhabar Imam Malik da shafi'i da Ahmad.

2- ya halatta a fitar da ita da kudi .Imam Abu hanifa da kadan daga mazhabar shafi'i da Ahmad.

3- ya halatta afitar da ita da kudi amma sai a lokacin da bukatar kudin tafi tsanani ko in da wata masalaha . Mazhabar Imam Ahmad.

Daga zauren "Ramadan kareen" whatsapp

Address

No6 Na'alhaji Way Hayingada Dutsin-ma
Dutsin-Ma

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Madinatul Ahbab posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share