Charity Foundation Dutsin-Ma

Charity Foundation Dutsin-Ma To serve and assist A humanitarian organisation that helps orphans and poor ones.

ALHAMDULILLAH!Marar lafiyar da kuka tallafawa tana ci gaba da samun sauki..Allah ya saka muku da alheri Amin
06/08/2026

ALHAMDULILLAH!

Marar lafiyar da kuka tallafawa tana ci gaba da samun sauki..

Allah ya saka muku da alheri Amin

01/08/2026
29/07/2026

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Abubakar Bala, Suwaiba Umar, Hadiza Musa, Evraheem Yeakup, Shamsiyya Ahmad, Zarahh Abdul, It'x Believer, Ibrahim Sulaiman, Mukhtar Mamman, Maikasuwa Lawal, Abubakar Abdullahi, Queen Rahmarh, Familat Katara, Ibrahim Tanimu, Baban Malam Sule, Ahmad Babangida Garhee, Ahmad Dutsinma Emran, Bahari Tanimu, Annu Auta, Muhammad Abubakar, Ibrahim Sani Usman Dtm, Maryam Usman, Isyaku Abdulaziz Salis, Bilkisu Musa

TAYA MURNAA madadin dukkan Exco da membobi na wannan Gidauniya muna amfani da wannan kafa wurin taya MATAIMAKIN SHUGABA ...
27/07/2026

TAYA MURNA
A madadin dukkan Exco da membobi na wannan Gidauniya muna amfani da wannan kafa wurin taya MATAIMAKIN SHUGABA NA BIYU na wannan Gidauniya murnar samun Digiri na III a fannin ilimi (PhD in Educational Management) jami'ar Umaru Musa Yar'adua University Katsina.
Dr Malam Shamsudeen Salisu VC II Congratulations

Allah yayi jagoranci yasa albarka Amin

PRO 1

A tsawon shekaru 24 da wannan Gidauniya ta shafe iya wannan sune kaɗai aikace-aikacen da ta saka a gaba!Muna godiya da d...
24/07/2026

A tsawon shekaru 24 da wannan Gidauniya ta shafe iya wannan sune kaɗai aikace-aikacen da ta saka a gaba!

Muna godiya da dukkan irin goyan baya da gudummawa da kuke bamu tsawon wanann lokaci Allah ya saka da alheri ya saka acikin mizani Amin

PRO 1

Alhamdulillah! MUNA GODIYA KWARAI DA GUDUNMAWAR KU ALUMMA.A ranar Lahadi 19 ga watan July, Gidauniyar Charity Foundation...
23/07/2026

Alhamdulillah! MUNA GODIYA KWARAI DA GUDUNMAWAR KU ALUMMA.

A ranar Lahadi 19 ga watan July, Gidauniyar Charity Foundation Dutsinma ta je asibiti domin tahowa da Malama Balaraba wadda kuka bada gudunmawar ku domin a kula da lafiyar ta a asibitin WELLNESS dake cikin birnin Katsina.

Kamar yadda muka shaida anyi nasarar yi mata aiki ne tun a ranar da muka kaita ta da daddare.

An cire mata hannun da ya kasance yake barazana ga lafiyar ta da rayuwar ta.

Alumma Allah ya saka muku da alheri, da gudummawar ku ta kudade, da kuma godiya ta musamman ga duk wanda ya taya mu yaɗawa a kafafen sada zumunta wanda har takai ga anyi nasarar wannan aiki.

Charity Foundation Dutsinma yanzu haka tana kulawa da magunguna da abincin wannan baiwar Allah da dressing har Allah yasa ta warke.

Akwai sauran ƙarin bayani.. MUNGODE JAZAKALLAH BI KHAIR!

PRO 1

Alhamdulillah! Bayan sauraren shawararin mabiya wannan shafi namu na Facebook, biyo bayan wani post da ya fita inda rubu...
19/07/2026

Alhamdulillah!

Bayan sauraren shawararin mabiya wannan shafi namu na Facebook, biyo bayan wani post da ya fita inda rubutun ke zargin wani Matashi ɗan gwagwarmaya Abubakar Sadeeqi da amfani da hoto da aikin Charity wurin yin post akan neman gudunmawar Balaraba a Tiktok din shi.

Alhamdulillah mun zauna a matakin EXCO tun a safiyar ranar. Mun nuna damuwa tare da nuna rashin gamsuwa da hanyar da aka bi wurin tunkarar alamarin Sadeeqi.

A tsawon shekarun da Charity Foundation Dutsinma tayi yau muna cikin shekara ta 24 da kafuwa. Muna aiki kan Marayu, makabartu, ziyarar asibitoci da taimakon maras sa lafiya da Yan gidan gyaran hali. Charity Foundation bata taɓa aibata wani ba a shafin ta ba, ko kokarin cin zarafin wani ba.

Gaba ɗaya mun ɗauki wannan a matsayin sharrin shaiɗan da saɓanin fahimta tun daga farko.

Mun zauna da Sadeeqi a jiya kuma yaji daga gare mu munji daga gare shi, mun samu daidaito.

Muna amfani da wannan kafa wurin ƙara ba alumma da duk wanda rubutun mu na baya baiyi ma dadi ba ayi HAKURI.

Mu yan adam ne zamu iya samun kuskure. muna kyautata zaton ba za'a sake jin irin haka ba daga Charity.

Muna godiya da irin gudunmawa da goyon baya da FAHIMTAR mu da ake mungode..

PRO 1

Alhamdulillah! Likitoci sunyi ma Balaraba aiki sun raba ta da wannan raɗaɗi da take fama dashi tsawon shekaru.Godiya ga ...
17/07/2026

Alhamdulillah!

Likitoci sunyi ma Balaraba aiki sun raba ta da wannan raɗaɗi da take fama dashi tsawon shekaru.

Godiya ga Allah da yasa akayi aiki lafiya.

Muna godiya ga alumma da s**a bada gudummawa wurin ganin wannan baiwar Allah ta samu sauki, Allah ya saka da alheri ya saka a mizani Amin.

Yanzu haka tana kwance a WELLNESS SPECIALTY HOSPITAL da ke Katsina tana karɓar kulawa.

Muna addua Allah ya bata lafiya Amin.

PRO 1

Yau 16/July/2026 Charity Foundation Dutsinma ta kai Malama Balaraba asibiti a Katsina domin samun kulawar da ta dace.Bay...
16/07/2026

Yau 16/July/2026 Charity Foundation Dutsinma ta kai Malama Balaraba asibiti a Katsina domin samun kulawar da ta dace.

Bayan samun gudunmawar yanuwa dalilin shelanta halin da wannan baiwar Allah ta samu kanta ciki, Gidauniyar Charity a yau ta kai ta asibiti yau.

Zuwa gobe zamu saurari bayanin da likitoci zasu bamu In sha Allah.

Allah ya bata lafiya Amin

PRO 1

Address

No. 2, Kankia Bye-Pass/Opp. Dutsin-ma Motors
Dutsin-Ma

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Charity Foundation Dutsin-Ma posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The School

Send a message to Charity Foundation Dutsin-Ma:

Shortcuts

Share

Category