Masallacin Umar bin Khaddab - Tanki, Dutsin-ma

Masallacin Umar bin Khaddab - Tanki, Dutsin-ma Wannan shi ne shafin da za a rika bi domin samun bayanai game da wannan Masallaci.

MASALLACIN UMAR BIN KHADDAB (TANKI) DUTSIN-MA YA CIRI TUTA šŸŽ¤Masallacin Tanki Dutsin-ma yana tsakiyar garin Dutsin-ma aka...
26/04/2025

MASALLACIN UMAR BIN KHADDAB (TANKI) DUTSIN-MA YA CIRI TUTA šŸŽ¤

Masallacin Tanki Dutsin-ma yana tsakiyar garin Dutsin-ma akan titin Dayyabu Road kusa da Danrimi.
Wannan Masallacin ya ciri tuta wajen gabatar da karatuttuka da mahadorori a dukkan ranaku bakwai na sati wanda Maluma daban-daban ke Gabatarwa.

Ga jerin ranaku da kuma Maluman dake gabatar da Darussa a Masallacin kamar haka :-
1 - Asabar da Lahadi - Sheikh Ilyasu Imam Radda (Tafsirin Al Qur'ani mai girma cikin Raddul azhan ila ma'anil Qur'ani)
2 - Litinin - Ustaz Sanusi Muhammad Shara (Al-Aqidatu)
3 - Talata - Ustaz Muhsin Abdullahi (Al-aqida)
4 - Laraba - Ustaz Isyaku Ahmad Habibu (Kitabu Al-Ahdary) Ahlary/Lahallari.
5 - Ustaz Bashir Aliyu Zakariyya (Tarihin Sahabbai)
6 - Juma'a - Ustaz/Alaramma Alhafiz Abdullahi Adamu (Kira'atul Qur'anil kaeem)

Duka wadannan karatuttuka ana gabatar dasu ne a Tsakanin Sallar Magrib da Isha'i.

Allah Ya saka ma Maluman mu da alheri, Ya kara masu lafiya da hazaka da juriyar karantar da al'umma addinin Allah amin.

Jibwis Social Media
Dutsin-ma Local Government
Katsina State, Nigeria.

Maraba lale da Sheikh Musa Muhammad Dankwano.
01/03/2025

Maraba lale da Sheikh Musa Muhammad Dankwano.

WA ZAI BA ALLAH RANCE, RANCE MAI KYAWO.....? Masallacin Umar bin Khaddab Dutsin-ma wanda aka fi sani da Masallacin Tanki...
27/02/2025

WA ZAI BA ALLAH RANCE, RANCE MAI KYAWO.....?

Masallacin Umar bin Khaddab Dutsin-ma wanda aka fi sani da Masallacin Tanki dake tsakiyar garin Dutsin-ma na bumatar Shimfida (CARPET) da kuma fenti (PAINT).
Jama'ar Annabi a taimaka fisabilillahi ganin azumi ya zo.
Ana iya tuntu6ar Ladanin Masallacin Malam Ibrahim Akawu ta wannan lambar 0802 677 7370 domin samun karin bayani.

Allah Ya bada ikon taimakawa amin.

NUQDA TA FARKO A CIKIN KARATUN FIQHU LITTAFIN AL-AHDHARIY.A yau Laraba 8-3-1446h/11-09-2024m Allah Ya bada ikon fara kar...
11/09/2024

NUQDA TA FARKO A CIKIN KARATUN FIQHU LITTAFIN AL-AHDHARIY.

A yau Laraba 8-3-1446h/11-09-2024m Allah Ya bada ikon fara karatun fiqhu, inda a ka fara da karatun da Littafin Al-Akhdari (Ahlari) tare da matashin Malami Malam Ishaq Ahmad Habibu kuma za a cigaba da karatun a kowace ranar Laraba tsakanin Magrib da Isha'i.

Allah Ya amsa, Ya ba mu ikon sauraro tare da yin amfani da abin da za mu saurara amin.

Jibwis Social Media
Dutsin-ma L.G Branch.

SANARWA!      SANARWA!!     SANARWA!!!A NA BA JAMA'A HAKURI A KAN SANARWAR DA TA GABATA TA MUHADARA DA ZA A YI YAU A NAN...
10/01/2024

SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!

A NA BA JAMA'A HAKURI A KAN SANARWAR DA TA GABATA TA MUHADARA DA ZA A YI YAU A NAN MASALLACIN BAYAN SALLAR MAGRIB WANDA A KA SHIRYA SHEIKH ADAM YAHAYA KANO ZAI GABATAR CEWAR AN DAGA KARATUN SAI WANI LOKACI NA GABA IS SHA ALLAH.

DA FATAN ZA A BA MU UZURI, ALLAH YA SA HAKAN YA ZAMA ALHERI AMIN.

BISSALAM.

Sanarwa daga :-

Tanimu Bala Dutsin-ma
PRO na Masallaci.

SANARWAR!   SANARWA!!   SANARWA!!!A na sanar da al'ummar Musulmi cewar in sha Allahu akwai MUHADARA da za a gabatar a wa...
09/01/2024

SANARWAR! SANARWA!! SANARWA!!!

A na sanar da al'ummar Musulmi cewar in sha Allahu akwai MUHADARA da za a gabatar a wannan Masallaci kamar haka

RANA :- Gobe LARABA 10-01-2024.
LOKACI :- Bayan Sallar MAGRIBA.
WURI :- Masallacin Umar bin Khaddab (Tanki) nan cikin garin Dutsin-ma.

MAI GABATARWA :- Sheikh Adam Yahya Kano.

Sanarwa daga :-
Malam Sanusi Muhammad Shara.

Ta hannun.....

Tanimu Bala Dutsin-ma
(PRO) na Masallaci.

Karatun littafin zammud dunya tare da Dr Ahmad Ahmad Kura daga Masallacin Umar bin Khaddab (Tanki)Domin bin karatun kai ...
05/01/2024

Karatun littafin zammud dunya tare da Dr Ahmad Ahmad Kura daga Masallacin Umar bin Khaddab (Tanki)

Domin bin karatun kai tsaye sai a nemi shafin ALKITABU WASSUNNAH DUTSIN-MA.

Tafsirin Alqur'ani mai girma daga Majalisin Shugaban Majalissar Malamai na Jibwis reshen karamar hukumar Dutsin-ma Sheik...
10/12/2023

Tafsirin Alqur'ani mai girma daga Majalisin Shugaban Majalissar Malamai na Jibwis reshen karamar hukumar Dutsin-ma Sheikh Ilyasu Imam tare da Alaramma Abdullahi Adamu da ke gudana duk ranakun Asabar da Lahadi na kowane sati a wannan Masallaci na Umar bin Khaddab (Tanki) a nan tsakiyar garin Dutsin-ma jihar Katsina tarayyar Nigeria.

29/11/2023

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Bara'u Murjana Gidajedtm, Abdulkadir Aliyu RA I

Assalamu alaikum. Ana sanar sa al'ummar Musulmi baki daya cewa in sha Allahu gobe ALHAMIS Sheikh Adam Yahaya Kano zai ci...
29/11/2023

Assalamu alaikum.

Ana sanar sa al'ummar Musulmi baki daya cewa in sha Allahu gobe ALHAMIS Sheikh Adam Yahaya Kano zai cigaba da Lakcar da ya fara yau a wannan Masallaci da zaran an gama Sallar LA'ASAR.

Allah Ya bada ikon halarta amin.

Tanimu Bala Dutsin-ma
(PRO)

Address

Dutsin-Ma

Telephone

+2348026777370

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Masallacin Umar bin Khaddab - Tanki, Dutsin-ma posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category