18/08/2026
Thank you Premier Radio
Jami’ar Tarayya ta Dutse (FUD) ta samu tallafin bincike guda biyu da s**a kai Naira miliyan 53 daga Asusun Kula da Ilimin Manyan Makarantu (TETFund) domin nemo hanyoyin magance matsalar rashin tsaro da kuma yaduwar sauro a Najeriya.
Farfesa Ado Garba Jangargari ya samu tallafin Naira miliyan 25 domin gudanar da binciken mai taken “Tech for Peace: Engaging Northern Pastoralists Non-Agricultural Livelihoods to Counter Banditry and Kidnapping”, wanda ya mayar da hankali kan hanyoyin shigar da makiyaya a ayyukan da ba na noma ba domin dakile yan bindiga da masu garkuwa da mutane.
Shi kuwa Farfesa Joshua Balogun ya samu Naira miliyan 28 domin binciken “Development of Indoor Carbon Dioxide Sequestration Machine (iCor-SeMa) for Diversionary Control of Mosquitoes in Nigeria”, wanda ke neman samar da na’ura ta musamman domin sarrafa sauro a cikin gidaje.
Za a gudanar da binciken guda biyu cikin tsawon watanni 24.
Shugaban Jami’ar, Farfesa Ahmad Muhammed Gumel, ya taya malaman murnar samun tallafin, tare da bukatar su kammala ayyukan cikin lokacin da aka tsara.
Ya kuma ce jami’ar na sa ran samun karin tallafin bincike, bayan da aka wayar da kan malaman jami’ar kan hanyoyin neman tallafi da sauran tallafin bincike daga sassan duniya.