08/03/2026
Lantarko!
Mai magana da yawun shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Daniel Bwala ya bayyana cewa, duk da rashin cika alkawuran da su ka kasa yi a kasar nan, talakawa ne ya rage su yanke da kansu, ko za su sake zabar Tinubu ko a'a.
Daniel ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawar keke da keke mai taken 'Head to Head' a tashan Aljazeera, daidai lokacin da yake amsa tambayar wata matashiya kan kalaman shugaba Tinubu ya yi bayan lashe zaben 2023, cewa "Idan ban samar da tsayayyiyar wutar lantarki ba, kar ku zabe ni a karo na biyu".