Dutse Students Association DUSA National Body.

Dutse Students Association DUSA National Body.

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Dutse Students Association DUSA National Body., Elementary School, Dutse.

17/01/2025

With Sulaiman SP – I just got recognized as one of their top fans!

18/08/2023

*DUTSE STUDENTS ASSOCIATION (DUSA NATIONAL BODY)*

ZIYARA GA DAN MAJALISSAR JAHA MAI WAKILTAR KARAMAR HUKUMAR DUTSE HON. TASI'U ISHAQ SOJA.

Shugabancin daliban karamar hukumar Dutse sun kai ziyara ga dan majalissar jaha mai wakiltar karamar hukumar Dutse a gidansa dake nan Dutse. Ziyarar da sakataren kungiyar, Usman Gwadabe Dutse ya jagoranta, ta samu rakiyar mataimakin sakatare, kakakin kungiya (PRO) da kuma sauran wakilan kungiyar.
Shugaban ya nuna jin dadinsa matuka da wannan ziyara, kuma yayi alwashin aiki da wannan kungiya wajen tallafawa dalibai a wannan karamar hukuma. Haka kuma yace "akwai shiri mai gwabi da yayiwa dalibai a kusan nan, lokaci kawai muke jira".
Muna fatan Allah ya bashi ikon sauke wannan nauyi daya rayata a kansa dama sauran al'umma baki daya.

✍🏼
*Usman Gwadabe Dutse*
_Sec Gen DUSA National Body_.
18/08/2023

12/07/2023

*DUTSE STUDENTS ASSOCIATION (DUSA NATIONAL BODY*)

_PRESS RELEASE_

The above named association wishes to call on the attention of the students of Dutse local government studying in Bayero University Kano (BUK) to submit the following details to supervisory councilor on Education Hon. Abdullahi Solvetor in his office @ Dutse local government Secretariat.

The details are as follows;

1. Photocopy of admission letter

2. Photocopy of indigene certificate

3. Central registration Remita (RRR)

For more information contact the number below:
08067323407

✍🏼 _USMAN GWADABE DUTSE_
*SECRETARY GENERAL DUSA NATIONAL BODY.*

Photos from Dutse Students Association DUSA National Body.'s post 12/05/2023

*DUTSE STUDENTS ASSOCIATION (DUSA)*

_JINJINA DA GODIYA GA HON. BALA USMAN CHAMO_

Wannan kungiya na mika sakon jinjina/godiya ga shugaban karamar hukumar Dutse Mal. Bala Usman Chamo bisa bada tallafin karatu ga wasu daga cikin daliban dake karatu a makarantun dake nan karamar hukumar Dutse wato Federal University Dutse FUD da kuma jigawa state polytechnic Dutse na kudi naira 20,000 da kuma 10,000 domin rage dawainiyar makaranta da kuma bukatu na yau da kullum.

Haka zalika ya kara da yiwa sababbin dalibai albishir din cewa tallafin karatu (scholarship) na nan tafe kamar yadda aka saba yi a kowacce shekara.

Muna masu addu'ar Allah ya sakawa Mai girma chairman da mafificin alkhairi, ameen.
Allah ya karo mana irinsu da yawa a wannan karamar hukuma tamu mai albarka, wadanda zasu tallafawa dalibai da ma sauran al'umma baki daya.

✍🏼 USMAN GWADABE DUTSE
SECRETARY GENERAL.
DUSA NATIONAL BODY.

Photos from Dutse Students Association DUSA National Body.'s post 19/04/2023

*DUTSE STUDENTS ASSOCIATION (DUSA)*

_Gayyata! Gayyata!! Gayyata!!!_

Wannan kungiya mai suna a sama, na farin cikin gayyatar daliban da shugaban karamar hukumar Dutse, Malam Bala Usman Chamo ya biyawa jamb, izuwa horaswa domin tunkarar jarabawar.
Horon zai fara gudana ne a :

Gobe Alhamis 20th of April, 2023.

Da karfe 7:30am na safe

Horaswar zata gudana ne a Dutse Computer Center

Za a fara da makarantun da suke cikin gari, kamar makarantar Zai, Limawa, Gadadin, Galamawa, Dr. Nuhu (Dambe), Fagoji, Marabusawa, Dan masara, Jigawar Tsada, da dai sauransu.

Da fatan za a samu halarta a kan lokaci.

Sanarwa daga ofishin sakatare na wannan kungiya.
*Usman-Gwadabe-Dutse*

Want your school to be the top-listed School/college in Dutse?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Website

Address


Dutse