Tsangayar Malaman Daura

Tsangayar Malaman Daura ASSALAMU ALAIKUM WA RAHMATULLAHI
wannan shafi an ƙirƙire shi ne domin yaɗa Karatuttukan Malamai

30/08/2026

🕊️ SANARWAR RASUWA 🕊️

إِنَّا لِلَّهِ وَإِنَّا إِلَيْهِ رَاجِعُونَ

Cikin alhini da jimami muke sanar da rasuwar LADAN LAWAL YAHAYA, wanda aka fi sani da Ladanin Masallacin Rijiyar Daɗi, wanda Allah Ya yi wa rasuwa a daren jiya.

Za a gudanar da suturar marigayin da misalin ƙarfe 9:00 na safe, in Allah Ya yarda.

Muna roƙon ’yan uwa, abokan arziki da sauran al’umma da su taya mu yin addu’a ga marigayin.

Ya Allah Ka gafarta wa Ladan Lawal Yahaya, Ka jiƙansa da rahama, Ka haskaka masa kabarinsa, Ka sanya kabarinsa ya zama ɗaya daga cikin lambunan Aljanna. Ya Allah Ka ɗaukaka darajarsa, Ka yafe masa kura-kuransa, Ka kuma bai wa iyalansa, ’yan uwa da sauran waɗanda wannan rashi ya shafa haƙurin jure wannan babban rashi.

Allah Ya sa mu cika da imani, Ya kuma ba mu kyakkyawan ƙarshe.

إِنَّا لِلَّهِ وَإِنَّا إِلَيْهِ رَاجِعُونَ

TAYA MARYAM IBRAHIM DAN’AZUMI MURNA — Gwarzon Alƙur’ani na NajeriyaIna miƙa saƙon taya murna na musamman ga Maryam Ibrah...
22/08/2026

TAYA MARYAM IBRAHIM DAN’AZUMI MURNA — Gwarzon Alƙur’ani na Najeriya

Ina miƙa saƙon taya murna na musamman ga Maryam Ibrahim Dan’Azumi bisa gagarumar nasarar da ta samu a Gasar Alƙur’ani ta Ƙasa da Ƙasa ta Sarki Abdulaziz karo na 46, wadda aka gudanar a Masarautar Saudiyya.

Samun nasara a irin wannan gasa, wadda ta ƙunshi mahalarta daga ƙasashe 132 na duniya, babbar nasara ce kuma abin alfahari. Ƙwarewar da Maryam ta nuna wajen haddar Alƙur’ani, karatunsa, Tajwidi da Tafsiri, sakamakon shekaru ne na jajircewa, sadaukarwa, himma da kuma dagewa wajen neman ƙwarewa.

Nasarar Maryam ta sake tunatar da mu irin gagarumin basira da damar da matasan Najeriya suke da ita wajen fafatawa da takwarorinsu na duniya da kuma samun nasara. Abin da ya ƙara ba da kwarin gwiwa shi ne irin abin koyi da iyalinta s**a samar. Babbar ’yar uwarta, Hajara Ibrahim Dan’Azumi, ita ma ta taɓa zama ta farko a wata gasar Alƙur’ani ta ƙasa da ƙasa da aka gudanar a Jordan a shekarar 2024. Nasarorin ’yan’uwan nan biyu sun nuna irin abin da za a iya cimmawa idan aka kula da baiwa, aka gina tarbiyya mai kyau, aka samu ilimi, jagoranci da tallafin iyali.

Ina taya iyayensu, malamansu da masu kula da tarbiyyarsu murna, tare da yaba musu bisa irin sadaukarwa, jagoranci da shawarwarin da s**a bayar, waɗanda s**a taimaka matuƙa wajen wannan gagarumar nasara.

A madadin Ma’aikatar Matasa ta Tarayya, ina taya Maryam murna da wannan nasara da ta kawo wa ƙasarmu Najeriya ɗaukaka da girma. Ina roƙon Allah Ya sanya wannan nasara ta zama abin ƙarfafa wa miliyoyin matasan Najeriya wajen neman ilimi, jajircewa da kuma ƙoƙarin samun nagarta da ƙwarewa.

Allah Ya ƙara wa Maryam ilimi da fahimta, Ya sanya Alƙur’ani Mai Girma ya zama tushen shiriya, rahama da albarka a rayuwarta.

Taya murna, Maryam! Najeriya na alfahari da ke.

Ayodele Olawande
Mai Girma Ministan Matasa

18/08/2026

Hadith
بسم الله الرحمن الرحيم

الحادي عشر‏:‏ عن ابن مسعود رضي الله عنه قال‏:‏ قال النبي صلى الله عليه وسلم‏:‏ ‏"‏ الجنة أقرب إلى أحدكم من شراك نعله، والنار مثل ذلك‏"‏ ‏(‏‏(‏رواه البخاري‏)‏‏)‏‏.‏

(Manzon Allah tsira da aminci su tabbata agareshi yace;
Aljanna kusa take ga kowane daya daga cikinku, fiye da madaurin takalminku
haka ma wuta).

Ibn Mas'ud (May Allah be pleased with him) reported:
The Prophet (ﷺ) said, "Jannah is nearer to anyone of you than your shoe-lace, and so is the (Hell) Fire".

[Al- Bukhari].

Riyad as-Salihin, 105

(

18/08/2026

Hadith
بسم الله الرحمت الرحيم

"عَنْ ابْنِ عَبَّاسٍ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُمَا أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صلى الله عليه و سلم قَالَ: "إنَّ اللَّهَ تَجَاوَزَ لِي عَنْ أُمَّتِي الْخَطَأَ وَالنِّسْيَانَ وَمَا اسْتُكْرِهُوا عَلَيْهِ" . حَدِيثٌ حَسَنٌ، رَوَاهُ ابْنُ مَاجَهْ [رقم:2045]، وَالْبَيْهَقِيّ ["السنن" 7 ]."

(Manzon Allah tsira da aminci su tabbata agareshi yace;
Hakika Allah yayi rangwame abisa al'umata ga abinda s**ayi akan kuskure, abinda aka takura musu, da kuma wanda s**ayi da mantuwa.)

Messenger of Allah (peace and blessings of Allah be upon him) said:
Verily Allah has pardoned [or been lenient with] for me my ummah: their mistakes, their forgetfulness, and that which they have been forced to do under duress. A hasan hadeeth related by Ibn Majah, and al-Bayhaqee and others.

Hadith 39, 40 Hadith an-Nawawi

18/08/2026

Hadith
بسم الله الرحمن الرحيم

"وَعَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ ‏- رضى الله عنه ‏- قَالَ: قَالَ رَسُولُ اَللَّهِ ‏- صلى الله عليه وسلم ‏-{ طَهُورُ إِنَاءِ أَحَدِكُمْ إِذْ وَلَغَ فِيهِ اَلْكَلْبُ أَنْ يَغْسِلَهُ سَبْعَ مَرَّاتٍ, أُولَاهُنَّ بِالتُّرَابِ } أَخْرَجَهُ مُسْلِمٌ [1]‏ .‏"

(Manzon Allah tsira da aminci su tabbata agareshi yace;
Tsarkin kwaryar dayanku, idan kare yayi lallagi acikinta , awanketa sau bakwai 7, na farkon da kasa. )

Narrated Abu Huraira (rad):
Narrated by Abu Huraira (rad): Allah’s Messenger (ﷺ) said: “The cleansing of the utensil belonging to one of you, after it has been licked by a dog, is to wash it seven times, and using soil for cleaning at the first time.” [Muslim reported it].

Bulugh al-Maram, 10

ILLAR WAYAR HANUN MU! -"Wannan wayar da kake gani ta hanun ka, lallai fuska biyu gareta a gurinka, akwai fuskar alkhairi...
17/08/2026

ILLAR WAYAR HANUN MU!
-
"Wannan wayar da kake gani ta hanun ka, lallai fuska biyu gareta a gurinka, akwai fuskar alkhairi sannan kuma akwai fuskar sharri a tattare da ita"
-
"Alkhairin ta ko kuma sharrin ta ya ta'allaƙa ne da aikin da zaka aikata da ita, sannan kuma ta ta'allaƙa ne da abinda zata kange ka daga gareshi, misalin ambaton Allah, zikirori, karatun alƙur'ani, da kuma yin ibadah akan lokacin ta"
-
"Wayar hanun mu tana da alkhairai masu yawa sannan kuma tana da sharri masu yawa a garemu, idan ta zamto alkhairi muke aikatawa da ita, kamar sauraron karatun alƙur'ani da hadisai, da kuma yaɗa aiyukan alkhairi a social media da ita, to haƙiƙa ita kanta ta zamto alkhairi a garemu, amma idan ya kasance muna sauraron waƙe-waƙe ne da ita, da kuma kallon videon batsa da kuma dukkanin nau'ukan ababen da zasu rafkanar damu daga ambatõn Allah, to haƙiƙa ita kanta ta zamto sharri a garemu"

WHATSAPP
https://whatsapp.com/channel/0029Va5y54uInlqKRdTL2l1i

*ALƘAWURAN ALLAH GUDA HUƊU:*-"Allah yayi wasu alƙawura acikin Alƙur'ani ga bayinsa, wanda kuma haƙiƙa munsan alƙawarin A...
14/08/2026

*ALƘAWURAN ALLAH GUDA HUƊU:*
-
"Allah yayi wasu alƙawura acikin Alƙur'ani ga bayinsa, wanda kuma haƙiƙa munsan alƙawarin Allah baya tashi, kuma Allah bai kasance yana saɓa alƙawari ba"
-
*ALLAH BUWAYI YACE:*
-
💧"Sabõda haka, ku tuna Ni, nima sai In tunã ku"
Quran-2:152
-
💧"Kuma lallai ne, idan kun gõde ina ƙara muku"
Quran-14:7
-
💧"Kuma Ubangijinku ya ce: "Ku kira Ni in karɓa muku"
Quran-40:60
-
💧"kuma lallai Allah bai kasance Mai yi musu azãba ba alhãli kuwa sunã yin istigfãri."
Quran-8:33
-
-
"Dukkanin waɗannan, wasu alƙawura ne waɗanda Allah maɗaukakin sarki ya ɗaukarwa kansa su matuƙar muma mun cika namu gareshi"

WHATSAPP
https://whatsapp.com/channel/0029Va5y54uInlqKRdTL2l1i

TELEGRAM
https://t.me/hausaislamicpicturesquotes

*MU YAWAITA SALATI A GARESHI SAW A DAREN JUMAA DA RANAR JUMA'A*-Sheikh Uthaimin (Rh) Yace: "Ya kai ɗan'uwana ka yawaita ...
10/08/2026

*MU YAWAITA SALATI A GARESHI SAW A DAREN JUMAA DA RANAR JUMA'A*
-
Sheikh Uthaimin (Rh) Yace: "Ya kai ɗan'uwana ka yawaita yima Annabi salati sai imaninka ya ƙaru al'amuranka kuma suyi maka sauki".

[رياض الصالحين ٥/٤٧١]

WHATSAPP
https://whatsapp.com/channel/0029Va5y54uInlqKRdTL2l1i

KUNYA ADON MUMINI.-"A matsayinka na musulmi, duk inda kaje ka siffantu da siffa ta kunya, domin ita kunya wata kyakkyawa...
08/08/2026

KUNYA ADON MUMINI.
-
"A matsayinka na musulmi, duk inda kaje ka siffantu da siffa ta kunya, domin ita kunya wata kyakkyawar gaɓace a cikin gaɓoɓin musulunci. Kada a matsayinka na musulmi duk inda kaje ka dinga nuna rashin kunya, haƙiƙa ba a san musulmin ƙwarai da nuna fitsara ko rashin kunya ba"
-
"Kada ka yarda bayyanar da fitsara ta zamto itace ɗabi'arka a cikin jama'a, domin haƙiƙa babu alkhairi a cikin yin hakan, kuma duk mumini na ƙwarai an sanshi da kunya"
-
"Me cece ribarka idan ka kasance marar kunya? Me cece ribarka don mutane sun fahimci rashin kungiyarka a duniya? Yaya za kayi idan Allah ya cire tausayinsa a kanka a dalilin wannan rashin kunyar taka da kake bayyanarwa ga jama'a?"
-
WhatsApp channel
https://whatsapp.com/channel/0029Va5y54uInlqKRdTL2l1i
-
Telegram channel
https://t.me/hausaislamicpicturesquotes
-
Biyo Instagram ɗinmu
https://instagram.com/hausa.islamic.pictures.quotes?igshid=11g6c9k6

ZIKIRIN SAFIYA DA MARAICE.-"Kada ka rafkana daga zikirori a rayuwarka, musamman ma irin zikirorin safiya da maraice, da ...
08/08/2026

ZIKIRIN SAFIYA DA MARAICE.
-
"Kada ka rafkana daga zikirori a rayuwarka, musamman ma irin zikirorin safiya da maraice, da makamantansu, domin haƙiƙa shaiɗan yakanyi galaba kan duk wanda yake gafala daga yin addu'oi a rayuwarsa"
-
"Sau nawa wata musiba take shirin afkuwa gareka amma a dalilin addu'oin da ka kasance kana yi yau da kullum sai Allah ta'ala ya karkatar da wannan musibar izuwa wani gurin, sau nawa wani bala'in yake tunkaroka amma dalilin zikirorin da ka kasance kana yi sai Allah ya taƙaita wannan bala'i ya sauka a kan kayanka a maimakon ya sauka a karan-kanka"
-
"Haƙiƙa akwai falala a cikin yin zikirori a rayuwa, domin haƙiƙa shi zikiri kariya ne kuma garkuwa ne ga bawa, sannan kuma haƙiƙa Allah yana bawa bawansa lada idan ya kasance yana kiyaye yin zikiri musamman irin zikirin da ya tabbata a sunnah"
-
❝Duk wanda yace SubhanAllahi Wa bi Hamdi سبحان الله وبحمده Sau ɗari a rana, za a kankare masa zunubansa koda kuwa sun kai misalin yawan kumfar kogi❞

WHATSAPP
https://whatsapp.com/channel/0029Va5y54uInlqKRdTL2l1i
-
TELEGRAM
https://t.me/hausaislamicpicturesquotes
-
INSTAGRAM
https://instagram.com/hausa.islamic.pictures.quotes?igshid=11g6c9k6

Address

Muhammad Bashar Street
Daura

Telephone

+2348035792663

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Tsangayar Malaman Daura posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category