Muryar Talakawa

Muryar Talakawa Wannan dandalin an kirkiro shine domin wayar da kai a talakawan nigeria dan su san yanci su 07066714

Daga Website din Jaridar Premium Times....Sak**akon zabuka suna cigaba da sauka a Website din Premium Times...Kaima zaka...
27/02/2023

Daga Website din Jaridar Premium Times....

Sak**akon zabuka suna cigaba da sauka a Website din Premium Times...

Kaima zaka iya lekawa ka cigaba da gani da idonka ta link dake kasa👇👇👇

https://www.premiumtimesng.com/2023-elections

Zaɓen 2023: Za a rufe iyakokin Najeriya na sa'a 24
24/02/2023

Zaɓen 2023: Za a rufe iyakokin Najeriya na sa'a 24

Yadda 'yan takarar shugabancin Najeriya s**a isa jihohinsu don kaɗa ƙuri'a a zaɓen ranar Asabar.
24/02/2023

Yadda 'yan takarar shugabancin Najeriya s**a isa jihohinsu don kaɗa ƙuri'a a zaɓen ranar Asabar.

Ana ci gaba da raba kayan aikin zabe a jihohi daban-daban na Najeriya.
23/02/2023

Ana ci gaba da raba kayan aikin zabe a jihohi daban-daban na Najeriya.

Masha Allah wannan page din mu Mai suna muryar Talakawa ta dawo Aiki gadan gadan Insha Allah kuci gaba da bibiyan mu mun...
23/02/2023

Masha Allah wannan page din mu Mai suna muryar Talakawa ta dawo Aiki gadan gadan Insha Allah kuci gaba da bibiyan mu mun gode

Hukumomin tsaro a ƙasar Finland sun damƙe fitaccen jagoran 'yan a-ware na Biafra da ke neman ɓallewa daga Najeriya, Simo...
23/02/2023

Hukumomin tsaro a ƙasar Finland sun damƙe fitaccen jagoran 'yan a-ware na Biafra da ke neman ɓallewa daga Najeriya, Simon Ekpa, wanda ya yi kira ga jama'a a yankin kudu maso gabashin Najeriya, da kada su fita zaɓen shugaban ƙasar da za a yi ranar Asabar 25 ga watan nan na Fabarairu.

Bayanai sun nuna cewa kafar yaɗa labarai ta ƙasar ta Finland inda jagoran ke zaune, Helsingin Sanomat ta ce wakiliyarta ta je gidan Ekpa domin yin hira da shi a ranar Alhamis 23 ga watan Fabarairu 2023, k**ar yadda ya amince, sai ta ga jami'an tsaro na ƙoƙarin tafiya da Ekpa daga gidansa.

Bayanai sun nuna cewa jami'an tsaron ba su amsa wa wakiliyar tambayar da ta yi musu ta sanin dalilin k**a shi ba.

A saƙonni da dama da yake sanyawa a shafin Twitter, jagoran 'yan tawayen ya jima yana kira ga jama'a a yankin kudu maso gabashin Najeriya da kada su fita ranar zaɓe, tare da barazana ga duk wanda ya bijire wa kiran, ya fita zaɓe, cewa zai gane kuskurensa.

An k**a ɗan-a-waren ne, 'yan kwanaki bayan da gwamnatin Najeriya ta gayyaci jakadiyar ƙasar ta Finland a Najeriya, Leena Pylvanainen a kan barazanar da Epka ɗin ya yi kan yunƙurin haifar da matsala ga zaɓen na 2023 a yankin kudu maso gabashin ƙasar.

Gwamnatin Najeriya ta ce ba za ta lamunci da yadda É—an-tawayen yake kalamai da barazana a kan harkokin Najeriya ba sakaka, yadda yake so ba tare da gwamnatin Finland ta É—auki mataki a kansa ba.

A kwanan nan ya ayyana dokar zaman-gida ta kwana biyar wadda ya ce za ta fara daga ranar Alhamis 23 ga watan Fabarairu zuwa 28 ga watan na Fabarairu, wanda wannan ne ya sa fargaba a zaukatan mutane a yankin kudu maso gabashin Najeriya kan zaɓukan da za a yi.

ZANCEN GASKIYA DAGA BAKUNAN MUTANEN KIRKI 'YAN MAZAN JIYA-Marigayi Firimiyan Arewa Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto yac...
05/05/2021

ZANCEN GASKIYA DAGA BAKUNAN MUTANEN KIRKI 'YAN MAZAN JIYA

-Marigayi Firimiyan Arewa Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto yace: Idan mutanen arewa s**ayi wasa sai mun zama bayi a kasarmu ta haihuwa

-Sheikh Abubakar Mahmud Gumi yace: Idan bamuyi karatu ba za'a dinga binmu har gidajen mu ana kashemu

-Shahidi Insha Allah Sheikh Ja'afar Mahmud Adamu Kano yace: matsalarmu mutanen Arewa shine zaman munafurci, son-kai da son mulki, kowa ya samu yaci shi da 'ya'yanshi da matanshi da kannen matansa.

-Shugaban 'yan gwagwarmaya, babban Kwamandan Askarawan Salafiyyah a Nigeria Shahidi Insha Allah Sheikh Albaniy Zaria yace: Babban matsalar Musulmin Arewa shine rashin hadin kai, da gayya makiya s**a zuba kudi s**a farraka hadin kan musulmi saboda ta nan ne za'a samu ikon cin nasara akan mu.

Zamu iya yarda da magabatan s**a fada idan mukayi la'akari da abubuwan da suke faruwa yanzu a Arewa tsakanin 'yan uwa Musulmi

Muna fatan Allah Yaa jikansu, Ya bamu mafita na alheri
Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum

Via Datti Assalafiy

SANSANIN KIDNAPPERSWannan shine sansanin masu garkuwa da mutane a cikin jeji yadda  suke rayuwa, jama'a ku dubi iriin mi...
05/05/2021

SANSANIN KIDNAPPERS

Wannan shine sansanin masu garkuwa da mutane a cikin jeji yadda suke rayuwa, jama'a ku dubi iriin miyagun mak**ai dake hannunsa, gaskiya za'a jima ana fafatawa da 'yan ta'adda a Nigeria

Ina yawan fadin cewa matsalar tsaron kasar Nigeria za'a taka masa burki idan Gwamnati ta yaki hanyar da 'yan ta'adda suke samun makami da man fetur, domin idan 'yan ta'adda ba su samu makami da fetur ba Wallahi su ba komai bane

Cikin satin nan ance shugaba Buhari ya amince da kafa wata hukuma da zata yaki bazuwar kananan mak**ai, madadin a kafa hukumar da zata yaki manyan mak**ai sai akace wai kananan mak**ai, wato suna yin abu k**ar ba su san menene halin da Kasar take ciki ba

Yaa Allah Ka nunawa shugaba Buhari zahirin gaskiyar abinda yake faruwa Ka bashi ikon daukar mataki
Allah Ka kare mu daga fadawa tarkon 'yan ta'adda

Via Datti Assalafiy

03/05/2021

A sanadin 'Abaya' wasu za su bar baya da ƙura.

• Lallai ya k**ata Iyaye su saka ido sosai a kan ƴaƴayensu mata; don a irin wannan matakin ba sa ji, ba sa gani.

• Sannan ba abin mamaki bane, mace budurwa ta je tana roƙon sauarayi ko saurayinta a kan ya siya mata 'Abaya' — saboda kar ayi yayin ya wuce ban da ita. Wannan lamari ba fa ƙarami bane...wata musifa ce ke shirin tunkarar al'umma.

Akwai Ƴammata masu rawar kai sosai, wanɗanda daga son Abaya kuma idan ba ta yi sa'a ba, to, daga nan ta faɗa tarkon yanayi mai mummunan makoma a rayuwarta.

• Duk wani shaiɗanci yanzu kusan ana fara tattauna shi ne daga SOCIAL MEDIA kan kace kobo, abu ya watsu, shi ke nan kuma shaiɗan shi ma sai ya yi amfani da wannan damar wajen ƙarfafa zukatan masu raunin imani.

NASIHA CE !!!

®Uthman Ibrahim Khalil

01/05/2021

Ni da ku Allah Ya kara albarka a rayuwar mu, Ya tsaremu daga dukkan fitina da abin cutarwa, Ya kyautata karshen mu a Musulunci
Amin

🖋....... A I Y. Darazo

Address

Muryar Talakawa
Darazo

Telephone

07066714004

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Muryar Talakawa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category