12/08/2026
Cigaba Da Ziyarori Wajaje Masu Tsarki Markadin A'immah Da Iyalan Su Dama Annabawan Allah, Yau Shugaban Makaranta Alaramma Malam Aliyu Yusuf Darazo, Ya Samu Damar Ziyartar Zuwa Garin Hillah Dake Birnin Babilon Dake Kasar Iraqi, Wanda Birni Ne Me Tarihi Kuma Yanada Daga Cikin Wajajen Da Ake Ziyarta.
Malam Ya Samu Ziyartar Kabarin Imran Dan Imam Aliy (As) Wanda Yayi Shahada A Yakin Nahrawan Wanda Ya Faru Tsakanin Mahaifin Sa Imam Aliy (As) Da Kawarijawa Tare Dashi Akwai Shahidan Wannan Yakin, Sannan Ya Mun Ziyarci Makwancin Annabi Ayub Wanda Shima Yake A Garin Hillah, Da Kuma Sayyida Sharifa Yar Imam Hassan Dan Imam Aliy Da Sayyida Zahra (As) Wacce Akewa Laqabi Da Dabibatu Ahli Muhammad, Marasa Lafiya Daga Sassa Daban Daban Na Duniya Suna Zuwa Yin Tawassuli Da Ita Anan Marqadinta Kuma Ana Ganin Ijaba Wasu Ma Take Suke Warkewa, Sannan Daga Karshe Sun Ziyarci 'Yan Hassan Al Musannah Dan Imam Hassan (As) Sayyida Fatima Da Sayyid Rukayyah (As) Duk Suma A Garin Hillah Dake Babilon Wacce Aka Fi Sani Babil A Yanzu.
Muna Addu'a Allah Ya Amsa Addu'o'in Da Akayi Ya Kuma Maimaita Irin Wannan Ziyari Din, Ya Biya Bukatun Mu Ya Kare Jagoran Mu Allamah Al Mujaheed Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) Ya Kara Masa Lafiya Da Nisan Kwana.
✍️ Abdullahi Dauda Darazo
12/08/2026