Hasken Musulunci

Hasken Musulunci Plx

AZUMIN ‘ARAFAH RANAR JUMU’AH.قال الرسول صلى الله عليه وآله وسلم : «صيام يوم عرفة أحتسب علَى الله أن يكفّر السنة الَّتي ق...
07/07/2022

AZUMIN ‘ARAFAH RANAR JUMU’AH.

قال الرسول صلى الله عليه وآله وسلم :

«صيام يوم عرفة أحتسب علَى الله أن يكفّر السنة الَّتي قبله، والسنة التي بعده»

رواه مسلم، ١١٦٢ عن أبي قتادة الحرث بن
ربعي-رضي الله عنه

Fassara:

Manzon Allah صلى الله عليه وآله وسلم ya ce:

“Azumin ranar ‘Arafah, Ina fata gun Allah cewa zai kankare (zunuban) shekarar da ta wuce da kuma shekara mai zuwa”

Tirkashi!!
Zunuban watanni 24 rigis Allah zai wanke maka a dalilin azumtar wannan rana.
Dan haka, idan wannan azumin ya dace da ranar Jumu’ah ba abinda zai hana yin wannan azumin. Ta yaya Musulmi zai haramta ma kanshi wannan gagarumin alkhairi haka?!
Hadisin da ke hana yin azumin ranar Jumu’ah ko Asabar a daidaikunsu yana nufin kebe kowane daya daga cikin wadannan rankun ne da azumi. Dole kayi ranar Alhamis sannan kuma sai ka kawo Jumu’ah, ko kuma kayi ranar Jumu’ah sannan ka kawo Asabar.
Amma a nan BA JUMU’AH ce a ke kallo ba. RANAR ‘ARAFAH ce a ke kallo a nan.
Dan haka ina kira ga dukkanin Musulmi- wadanda ba su samu zuwa aikin Hajji ba, cewa kowa ya azumci wannan rana Jumu’ah mai zuwa.
Wannan ita ce fahimtar Jumhuur na Malamai, Allah Ya rahamshe su.

SHAYKH MUH'D BIN UTHMAN HAFIZAHULLAH✍🏾

WhatsApp

WhatsApp Group Invite

06/07/2022
30/06/2022
30/06/2022

Address

Damaturu

Telephone

+2347042630309

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hasken Musulunci posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The School

Send a message to Hasken Musulunci:

Shortcuts

Share

Category