07/07/2022
Sana'o'in da zaka iya yi da jarin 200K:
1. Gwanjo: za ka iya fara sana'ar gwanjo da kasa da 200k, ana sayar da dila (bale) din gwanjon kayan sakawa 120k, 150k, 200k zuwa sama. Amma kana iya kai abin da ake cewa 'signing' a harkar gwanjo, wato a bude maka dila ka zaba akan farashin sari ka bar musu yama-yamar.
2. Kayan abinci: da 200k har shagon kayan abinci kana iya budewa a location mai kyau kuma kwalliya ta biya kudin sabulu. Yadda ake yi shi ne, zaka k**a shago k**ar na 20k a shekara—ka sayi kayan zubawa da aunawa k**ar na 10k. Sannan ka sayo masara, dawa, gero, dauro shinkafa, dss na 160k din.
3. Belt, wallet, hand bag na mata: da 200k kana iya sayo duk wadannan ka fara saidawa hankali kwance.
4. Maganin kwari: 200k ta isheka sana'ar maganin kwari.
5. Kayan marmari: 100k ta isheka cikakken jalin sana'ar kayan marmari a ko ina a Nigeria. Ka samu guri mai kyau ka k**a shago ko ka buga teburi babba kaita amsar dalolinka kana lumshe ido.
6. Sana'ar Leda: zaka iya sayen baro ka cika shi da leda da sassafe kana rabawa masu shaguna, ko kuma ka rike a hannu kana rabawa a kasuwa, da akwai rufin asiri a harkar.
7. Sana'ar saida dabbobi: idan ka rike 200k zata saya maka raguna biyu ko awaki shida daga kasuwa mai sauki zuwa kasuwar da za ka sayar ka samu riba.
8. Soft drink: za ka iya ka sami junction mai kyau sannan ka ayije irin fridge din nan daya daina dauke wuta, ka zuba masa soft drinks, ka sayo kankara ka dora kana saidawa.
9. Sana'ar kaji: zaka iya daidaitawa da masu gidan gona ko mata masu kiyo a godaje koma ka nake shiga kasuwannin kauye, kana ke sayowa kana saidawa.
10. POS: zaka iya ka samu guri mai kyau ka kafa POS dinka.
A karshe kana iya fara kusan ko wacce sana'a ko baka da ko kwandala, ka shirya da masu saidawa kai kuma kana ke tallatawa da wayar hannunka, idan ka samu mai saye ka amso ka saida ka samu alheri mai tarin yawa.
Haruna Ali Tijjani
mai barde foudation is non governmental institution that offer scholarship to less previlages one's.