11/06/2026
YADDA AKE SALLAR TASBIHI (SALATUL TASBIH) DALLA-DALLA
GABATARWA: MENE NE SALLAR TASBIHI?
Na san ka sha cin karo da bayani na yadda ake sallar Tasbihi… amma yana iya zama ɗan rikitarwa ko rashin fahimta. Wannan bayanin zai warware maka komai. Idan ba ka fahimci wannan bayani ba, akwai yiwuwar ba ka fahimta ne kana buƙatar aure.
Salatul Tasbih sallah ce ta Nafila mai Raka’a Huɗu (4), wacce ake yin ta domin neman gafarar zunubai. Annabi (S.A.W) ya ce wa Abbas bn Abdul-Muṭṭalib (R.A): “Idan ka yi ta, Allah zai gafarta maka zunubanka; na farko da na ƙarshe, na dā da na yanzu, na ganganci da na mantuwa, na ƙanana da manya…”
TASBIHIN DA AKE YI A CIKIN SALLAR TASBIHi
((سُبْحَانَ اللَّهِ، وَالْحَمْدُ لِلَّهِ، وَلَا إِلٰهَ إِلَّا اللَّهُ، وَاللَّهُ أَكْبَرُ))
(Subḥānallāhi, wal-ḥamdu lillāhi, wa lā ilāha illallāhu, wallāhu akbar)
Wannan shi ne tasbihin Sallar Tasbihi, kuma shi ne ake faɗa sau 300 gaba ɗaya:
LURA MUHIMMI:
1. Duk inda aka ce sau 10 ko sau 15, wancan tasbihin ne ake faɗa.
2. Zikirin da ake faɗa a ruku’u da sujjada na yau da kullum (Subḥāna Rabbiyal ʿAẓīm / Aʿlā) ba ya cikin wannan lissafi na 300 da ake buƙata.
Shi kawai zikirin ruku’u da sujjada na yau da kullum ne, sannan bayan ka gama shi ne zaka shiga tasbihin Sallar Tasbihi.
Ina fatan ka fahimta?
YADDA AKE YIN SALLAR (MATAKI-MATAKI):
A kowace raka’a ɗaya, za ka faɗi tasbihi 75 kamar haka:
1. Bayan Kabbarar Harama:
Ka karanta Al-Fātiḥa da surah ka karanta ko wace surah. Kana tsaye (kafin ka tafi ruku’u), sai ka ce:
“Subḥānallāhi, wal-ḥamdu lillāhi, wa lā ilāha illallāhu, wallāhu akbar” sau 15.
2. A Cikin Ruku’u:
Da farko ka ce:
“Subḥāna Rabbiyal ʿAẓīm (sau 1 ko 3 – kamar yadda ake yi a sallah ta yau da kullum)”. Bayan haka, sai ka ce: “Subḥānallāhi, wal-ḥamdu lillāhi, wa lā ilāha illallāhu, wallāhu akbar” sau 10.
3. Bayan Ɗagowa Daga Ruku’u (I‘tidāli): Bayan ka ce “Rabbana walakal hamd”, kana tsaye, sai ka ce:
“Subḥānallāhi, wal-ḥamdu lillāhi, wa lā ilāha illallāhu, wallāhu akbar” sau 10.
4 A Sujjada ta Farko:
Da farko ka ce:
“Subḥāna Rabbiyal Aʿlā (sau 1 ko 3 – kamar yadda ake yi a sallah ta yau da kullum)”. Bayan haka, sai ka ce:
“Subḥānallāhi, wal-ḥamdu lillāhi, wa lā ilāha illallāhu, wallāhu akbar” sau 10.
5. A Zaune Tsakanin Sujjada Biyu:
Kana zaune bayan ka ɗago daga sujjada, sai ka ce:
“Subḥānallāhi, wal-ḥamdu lillāhi, wa lā ilāha illallāhu, wallāhu akbar” sau 10.
6. A Sujjada ta Biyu:
Da farko ka ce:
“Subḥāna Rabbiyal Aʿlā (sau 1 ko 3 – kamar yadda ake yi a sallah ta yau da kullum)”. Bayan haka, sai ka ce:
“Subḥānallāhi, wal-ḥamdu lillāhi, wa lā ilāha illallāhu, wallāhu akbar” sau 10.
6. Zaman Hutu (Jalsatul Istirāḥah):
Bayan ka ɗago daga sujjada ta biyu (kafin ka miƙe zuwa raka’a ta gaba ko kafin ka yi Tahiya), sai ka ce:
“Subḥānallāhi, wal-ḥamdu lillāhi, wa lā ilāha illallāhu, wallāhu akbar” sau 10.
Jimlar raka’a ɗaya = Tasbihi 75
Jimlar raka’a huɗu = Tasbihi 300
AMSOSHIN TAMBAYOYI MASU MUHIMMANCI:
1. Da Rana ake yi ko da Dare?
Amsa: Ana iya yin ta a ko wane lokaci (Rana ko Dare), in ban da lokutan da aka hana Sallah (kamar fitowar rana ko faɗuwarta). Amma yin ta da dare ya fi falala da natsuwa.
2. Raka’a hudu a jere za a yi ko biyu-biyu?
Amsa: Idan Da Rana ne: An fi so a yi Raka'a 4 a jere da sallama ɗaya (kamar Azahar), ko a yi 2-2. Duka ya halatta. Idan Da Dare ne: An fi so a yi Raka'a 2 a yi sallama, sannan a tashi a yi Raka'a 2 (Sallama biyu).
3. Wace Sura ake karantawa?
Amsa: Babu wasu surori na musamman da Hadisi ya kayyade (Dole). Za ka iya karanta Fatiha da duk surar da ta sauƙaƙa gare ka. (Sai dai wasu Malamai sun so a karanta: At-Takathur, Al-Asr, Al-Kafirun, da Al-Ikhlas a jere).
LOKACIN YIN TA:
-Kullum sau ɗaya.
-Idan ba za ka iya ba, sau ɗaya a mako.
-Idan ba za ka iya ba, sau ɗaya a wata.
-Idan ba za ka iya ba, sau ɗaya a shekara.
-Ko kuma a ƙalla sau ɗaya a rayuwarka.
MADOGARA
-Daga Abbas bn Abdul-Muṭṭalib (R.A) — Sunan Abi -Dawud, Lamba 1297
-Daga Abbas bn Abdul-Muṭṭalib (R.A) — Sunan at-Tirmidhi, lamba 482
Daga Abbas bn Abdul-Muṭṭalib (R.A) — Sunan Ibn Mājah, lamba 1387
Allah Ya ba mu ikon aikatawa da dacewa.
Yuzarsif Ibn Abubakrin ✍️
Center for Islamic Propagation
01/06/2026
19/03/2026
21/02/2026
29/01/2026
21/01/2026