17/05/2026
DA'AWAR KAWO CANJI
Mafiya yawan masu neman mulki a tsarin demokiraɗiyya, musamman ƴan hamayya, kan shaida wa mabiyansu cewa ba su da wata manufa ta neman mulkin illa domin kawo canji a fannonin da s**a shafi rayuwar al'umma, kamar:
1. Ilimi.
2. Lafiya.
3. Ruwan sha.
4. Tsaro da zaman lafiya.
5. Samar da aikin yi ga matasa.
A tawa fahimtar, wannan ikirarin ba dukansa ne gaskiya yake ba. Domin kuwa fannoni biyar ɗinnan dama can akwai su a ƙasa, kuma ma'aikatu ne na gwamnati (Ministries) kamar haka:
1. Fannin Ilimi: Akwai Ministry of Education.
2. Fannin Lafiya: Akwai Ministry of Health.
3. Fannin Ruwan Sha: Akwai Ministry of Water Resources.
4. Fannin Tsaro da Zaman Lafiya: Akwai Ministry of Defence da Ministry of Police Affairs.
5. Fannin samar da aikin yi ga matasa: Akwai Ministry of Youth Development.
Idan har ka ce za ka kawo canji ko sauyi a waɗannan ɓangarorin, hakan madalla; amma fa yana buƙatar ka sami gungun masana da ƙwararru (team), ka ba su aikin yin bincike na tsanaki daki-daki, sannan su gabatar maka da sakamakon binciken a matsayin tsarin aiki, wato blueprint (kundin tsarin kawo canji).
Wannan zai sa mu gamsu cewa da gaske, bilhakki ka zo da niyyar kawo canji mai ma'ana.
Amma idan ka fito kana cewa babu abu kaza da kaza, alhalin ba ka da wani sakamako na binciken ilimi a kan abubuwan da kake s**a, ai duk wanda ke sauraron gidajen rediyo na BBC Hausa ko DW Hausa ya san da waɗannan matsalolin.
Don haka, mene ne banbancin ka da mai sauraron rediyon? Ina ga lokaci ya yi da masu neman mulki a ƙarƙashin tsarin demokiraɗiyya, musamman ƴan hamayya, za su yi wa kansu da al'umma adalci wajen tallata sahihin tsarin da suke da shi ga al'umma ƴan ƙasa.
Kuma wani rashin adalcin na ƴan hamayya shi ne, ba sa faɗar nasarori da ci gaban da gwamnati mai ci ta kawo, don gudun kada al'umma su amince da ita. Wannan ma wani ɓangare ne na zalunci.
Gwamnati tana iya gazawa ba don tana son cutar da al’ummar da take mulka ba, sai dai don wasu dalilai na daban. Ya kamata ƴan hamayya a karon fari su ja hankalin gwamnatin domin ta gyara kura-kuranta; idan kuwa ta kasa, sai su yi amfani da wannan gazawar wajen tallata kansu da sunan kawo canji yadda suke muradi, amma ba batanci zalla ba.
Koma dai menene, canji na gari yana farawa ne daga kan kowannen mu; ta hanyar inganta imanin mu ga Allāh Maɗaukakin Sarki a matsayinmu na al'umma Musulmi, tare da yin aiki na gari ba tare da yin ƙasa a gwiwa ba.
Yan daga cikin kamalar hankalin bawa yaje yayi abinda zai iya yi na rufama kansa da iyalan sa asiri ta hanyar da Allāh ya yassare masa, ba sai ya jira wani yabashi ko ya hana shi ba. Ilimi ya cimmana Allāh ne mai wadatarwa ba waninsa ba, Mutane sababi ne kurum.
Imam Adam M. Mustapha (Jatkawy),
Mai rajin ayiwa kowa ĀDALCI.
29th Zul-Qa'da 1447AH,
17/05/2026.