01/08/2024
Assalamu alaykum wa rahmatullahi wa barakatuhu
Saboda yamutsi wanda ake ciki a qasa baki ɗaya
Mun ɗaga dawo daga hutun makaranta, har sai wani sati 09/08/2024 In sha Allah 🙏🏼
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Abdullahi bin Mas'ud Tahfeezul Qur'an, Damaturu, Education, Damaturu.
01/08/2024
Assalamu alaykum wa rahmatullahi wa barakatuhu
Saboda yamutsi wanda ake ciki a qasa baki ɗaya
Mun ɗaga dawo daga hutun makaranta, har sai wani sati 09/08/2024 In sha Allah 🙏🏼
Hukumar wannan makaranta tana gayyatan ɗaukacin al'ummar musulmi zuwa wajen bikin yaye ɗaliban guda 99 waɗanda s**ayi sauqan Al'qurani mai girma, wanda zai gudana in sha Allahu kamar haka
Rana: Lahadi (24/09/2023)
Lokaci: Qarfe goma na safe (10am)
Wuri: Harabar makaranta, Sabon pegi Damaturu.
Allah ya bada ikon halarta. Ameen 🙏
18/03/2023
MUHIMMIN SANARWA!!!
MAKARANTAR ABDULLAHI BIN MAS'UD LITAHFIZIL QUR'AN, DAMATURU. na sanar da Dukkan Iyayen Dalibai na dukkanin ressan ta guda 10 baki daya JANYE SAKON HUTU DA BAYYANA TSARIN KARATU CIKIN WATAN RAMADAN.
Da dukkanin girmamawa muna masu baiwa Iyayen dalibai hakuri, ganin cewa; a karon Farko mun bada Hutu har zuwa bayan zabe, sai kuma daga baya Hukumar zabe mai Zaman kanta (INEC) ta dage zaben Gwamnoni zuwa gobe (18/03/2023) kamar yadda Kuka sani.
Hukumar makarantar tayi zama a ranar 12/03/2023 domin duba muhimman abubuwa da s**a shafi makarantar kai tsaye da kuma dakatawar karatun dalibai na tsawon lokaci idan hutun yaci gaba. Bayan dogon nazari akan matsaloli da zasu iya aukuwa Idan muka cigaba da hutun, mun tsaida matsayar cewa; za'a yi karatu a Ramadan Insha-Allah.
Ranakun Karatu: Asabar da Lahadi
Lokaci: 8:00am - 1:00pm
Ranar fara karatu: 25th/03/2023.
Daga karshen Director yana mai baiwa iyaye hakurin wannan sauyi da aka samu, ya kuma sake jaddada kaunarsa gareku baki daya da kuma cigaban Karatun yayammu (Allah ya kara musu albarka) sannan yana Kira gareku (Iyaye) da kuci gaba da bamu hadin kai kamar yadda kuka saba.
Allah yasa mu dace Ameen 🙏
Sanarwa daga Offishin; Assistant Director.
Al-Hafiz Muhammad Zaji Makinta.✍🏽
A Madadin Director na Makarantar; Al-Hafiz Engr. Yahaya Alh. Liman.
17/03/2023.
15/05/2021
Karatun Al'qurani ya gudana daga bakin Muhammad Uthman Biriri
Sai kuma sharhin littafin tuhfatul Aɗfal daga bakin mai girma director Mallam Yahaya Alhaji Liman.
15/05/2021
Assalamu alaykum wa rahmatullahi wa barakatuhu!
Hukumar wannan makaranta tana gabatar da taron qarawa juna sani tsakanin mallaman ta na dukkan rassan ta guda shida da suke cikin wannan gari na Damaturu tare kuma da walimar goron sallah bayan gama azumin Watan Ramadhana mai alfarma. Qarqashin kulawar jagororinta
1. Mallam Yahaya Alhaji Liman - Director
2. Mallam Muhammad Sulaiman Gana - Deputy Director
3. Mallam Hashimu Saleh Gashinge - Secretary General
4. Mallam Muhammad Zaji Makinta - Assistant Director
5. Mallam Magaji Gambo Husseini - Assistant Secretary.
Allah ya bada Nasara. Ameen!!!