🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
*DELAY IN MARRIAGE.*
📍Girls at the age of *18-24 years* always attract serious men who are fully ready to marry them, but at this age most of our *girls/sisters* never wish to hear anything about marriage.
1. *I'm too young for that*
2. *Who cares about marriage*
3. *I'm focused on my books*
4. *I want to gather some money first*
5. *Marriage is full of problems*
These are some of few statements ladies talk of at their youth age.
📍But these girls will be having *serious & series of s*x relationship with small boys of their age,* because at that age, they always have high rate of boys, guys and men coming for them, but they will prefer to choose those boys rather than the real men who want to marry them. They are still young to marry right, but they are not young to have s*x with boys.
*No problem, God is watching you*
📍At age of *25-27,* parents will start asking them the following questions;
1. *How far?*
2. *Don't you have any one yet ?*
3. *Are you not planning to get married ?*
4. *Are you seeing that all your mates are getting married ?*
5. *Don't you know you are getting old?*
But mind you, parents only see the outside of their daughters, not knowing there is nothing left inside.
📍With all these questions by her own parents, she will now be thinking and asking herself things like: My mates are marrying,
1. *Does it mean am old enough to marry?*
2. *Hmmm, how should I go about it*
3. *My boyfriends are not serious about asking my hand in marriage*
4. *They are not even ready to marry yet*
5. *Well, God knows the best. I believe in God.*
*See oooh...!,* she has started putting her blame on God. *"God's time is the best"* OK, I agree for argument sake.
📍At age *27-30* they now start looking for men to marry not boys to have s*x and play with again.
They will start looking for serious relationship that will lead to marriage, but unfortunately, at this age of *27-30* not all men will be asking their hand in marriage.
You will see them forcing themselves to marry a man who don't want to marry them. *Please we beg you, leave us alone.*
No single man at age *27-30* will like to marry a lady of *30-35.* Now you hear the sisters say age does not matter.
*My sister, it matters a lot.*
Imagine buying a rotten tomato for $10 and your friend buys a fresh one for $7. Yes, that's how it feels like in marriage too.
📍Remember you rejected men because you think you were too young. What makes you think your old age does not matter to us?
That's why some men go back to their villages to find young girl to marry when the city ones are not serious about marriage and those that are serious happen to be old for them.
📍At age *30-35,* her friends will ask her:
1. *Why are you not married yet by this age of yours?*
2. *Is it not getting too late for you ?*
You will hear her asking you some silly questions like...
1. *Are you God?*
2. *Or do you want to marry me?*
3. *Is it a crime to be single at 30 or 35?*
4. *Did I see a man willing to marry me but I refused?*
5. *God knows the best for everyone please.*
📍At age *30-35* they will start praying like never before, moving from one church to another. If she's a Muslim, she will start praying night prayers, fasting and dressing modestly.
If you ask her for dating, she would burst out to say
1. *My brother, I'm not like them.*
2. *Am looking for a serious man, a husband not dating.*
3. *If you truly love me go and see my parents for marriage.*
4. *I can't do anything with you without my parents concern.*
Dear parents, they have started knowing your worth. When she was *18-24,* she was doing everything without considering you as parents.
📍You don't expect a young man of *27-30* to marry you of *30-35* as his house wife when there are younger pretty girls out there.
Even if he chooses to ignore your age and marry you, his family and friends will discriminate you.
Men that will be interested to marry you will be of *45 yrs and above* and mind you, those men are married with kids except you wanna be second or third wife.
📍Everything in life has its own season and time.
There's no lady at age *30-35* seeking for marriage who haven't been approached during *18-24.* But by then, they were busily jumping from clubs/parties to hotel rooms looking for *FUN* not *MARRIAGE*
Not everything is about prayer. God who created you has made a plan for you. But when you change the plan or miss the road, please don't disturb the peace of God. Cos, He will be busy planning for your younger sister.
📍Why do we have high rate of single mothers and single ladies? Does it mean there no men but only boys?
Thousands of *working class ladies* are out there confirmed single. Your Master's of PhD is *ZERO* without a husband.
Yes, *Education is key* but don't neglect a marriage proposal all in the name of your studies. Both of you are matured enough to wait if you're serious of getting married.
📍It's never too late to ask for forgiveness or have a second thought of mind. For our God is a merciful and gracious Lord.
*Change your mindset and turn to Him now, before it's too late*
AURE Bautar Ubangiji - taskar Lamido
DOMIN FADAKARWA DA TATTAUNAWA AKAN MATSALOLIN DA RAYUWAR AURE KE FUSKATA A WANNAN KARNI
*HAKURI A ZAMAN AURE (YAN'UWA MATA)*
*AURE BAUTAR UBANGIJI NE* Duk abun da kuma aka ce bauta ne,(bin umarnin Allah da nisantar haninsa) to akwai wahala a cikinsa, amma kada ki damu ko saka a ranki cewa kin shigo cikin wata rayuwa ne wacce take kamar na'ura ce a hannun ki, (duk yanda kika sarrafata haka zata kasance) (in aljannah k**e so a mu'amalar da kika yi a gidan auranki zaki samu aljannah) daga zarar an kaiki gidan mijinki toh akwai bukatar ki nutsu ki fiskanci sabuwar rayuwar da take gaban ki, ki zama jaruma, me hakuri, mace ta gari, me addini domin,
*JIGON SAMUN RIBAR RAYUWAN NAN SHINE HAKURI DA AMBATON ALLAH* ki kyautata aiki zaki samu ribar rayuwa duniya da lahira, duk yawan dangin ki da tarin soyayyar da suke miki wallahi bazasu amfane ki da komai ba a ranar da za'a tsayar dake da mijin ki kan mu'amalar da kuka yi da juna, kuma zasu ci gaba da ganin kima da mutuncin ki a yayin da kika zauna da mijin ki da yan uwanshi lafia.
*KOWACCE MACE* akwai kalubalen da take fuskanta a gidanta wata ta bangaren shi kanshi mijin, wata yaran shi, wata kishiya, wata yan uwan miji, a kowane yanayi kika samu kanki toh ki riqe Allah shi kadai, idan kina ganin ke kina cikin matsala toh wallahi idan kika ji na wata sai kiga kamar ke a aljannah k**e, kar ki damu da halin da k**e ciki ke dai ki rinqa mika al'amarin ki ga Allah ki sani shine ya dora miki domin ya jarrabaki kiyi hakuri ki zama me jarumta a cikin gidanki, kada ki damu da mutane ke dai kiji da kanki idan har kika ce sai kinyi abun da zaki burge mutane toh wallahi bazaki taba burge su ba karshe ma garin neman ki burge su din zaki sabi ubangijin ki domin,
*_Dabi'ah ce ta dan adam bai cika gane ni'imar da Allah ya masa ba sai a lokacin data gushe masa, kamar yadda yake da halayyar kushe abin kirki matukar bana kashin kansa bane._*
*KI SANI CEWA* shi akasi cikin rayuwar dan adam ashirin (20) cikin dari (100) ke samuwa cikin kuskure, ashirin (20) cikin mantuwa, amma sittin (60) kan samu ne dalilin kawar da kai cikin abun da aka sani a cikin son zuciya, babu ilimi gurin wanda baya aiki dashi. Allah kuma ba mutum bane b***e kice,zaki nuna masa, sai dai ya jarrabaki cikin abun da k**e wa matsakaicin so, hakurin nan dai shi *_Ameenatu_
GYARAN MAGUDANAR SOYAYYA
Assalamu alaikum wa rahmatullah, barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili, da fatan Allah SWT Ya amfanar da mu dukkan bayyanan da za su zo cikinsa, amin. A yau insha Allah za mu yi bayani kan hanyoyin da ma’aurata za su bi don gyara magudanar soyayyar auratayyarsu; da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
Yanayin Soyayya
Da farko, yana da kyau ma’aurata su fahimci cewa soyayya ita ce babban makasudin kasancewarsu ma’auratan juna, ita ce muhallin auratayya; in ba soyayya a cikin rayuwar aure, to auren nan zai zama fanko ba rahma a cikinsa; haka kuma soyayya ita ce dadin auratayya, auren da ba soyayya a cikinsa za ka same shi lami ba dandano a cikinsa, ko kuma a samu dandanonsa me daci ko hamami.
Soyayya kuwa kalma ce ta aiki mai gudana wadda ake cikin yin ta a kodayaushe ba dakatawa; haka ma manyan sinadaran da s**a gina soyayya; kaunatayya da kulawa dukkansu aikatau ne masu gudana. Al’amura da dama na faruwa cikin rayuwar aure, wadanda a hankali suna taruwa har su yi yawa su lullude soyayya kuma su cushe magudanarta, sai ta tsaya cak ba ta gudana; duk soyayyar da ba ta gudana kuwa to kamar babu ita ne, domin ma’aurata ba su amfana da ita. Don haka sai ma’aurata su bi wadannan hanyoyin don gano matsalolin da s**a taushe soyayyarsu har ya zamana ba ta gudana.
1. Bincike
Ba a iya maganin matsala har sai an gano yanayinta da abin da ke haifar da ita; don samun saukin gyara magudanar soyayya, sai ma’auarata su binciki kansu game da soyayyarsu kuma su yi kyakkyawan nazari kan wasu al’amura da s**a shafi soyayyarsu da kuma gano hanyoyin magance wadannan matsalolin.
Ga wasu jerin tambayoyi da ma’aurata za su amsa don gane inda soyayyarsu ke da tangarda da kuma abin da ya haifar da wannan tangardar:
1. Ina son Mijina/Matata kuwa?
2. Me Ya sa nake son shi/ta?
3. Yaushe na fara son shi/ta?
4. Shin son yana karuwa ne ko raguwa?
5. Me ya sa shi karuwa/raguwa?
6. Akwai wani laifi da ya sa na rage son shi/ta?
7. Ina ganin kima da darajarsa/ta kuwa?
8. Akwai wani laifi da ya yi/ta yi min da ya sa ba na ganin kimarsa/ta kamar da?
9. In na gan shi/ta ya nake ji, dadi da murna; bakinciki da haushi; ko bani jin komi?
10. Ina bayyanar da soyayya ta gare shi/ta kuwa: In amsar ‘I’ ne; ta wadanne irin hanyoyi ne; in kuma a’a, me ya sa?
11. Shin mijina/matata na sona kuwa?
12. Ta wadanne hanyoyi nake gane yana/tana sona?
13. In kuwa ba ya sona/ba ta sona, me ya sa?
14. Yaushe nake jin ya/ta daina sona?
15. Wani laifi na yi da ya sa ya/ta daina sona?
16. Ya zan ji yau a wayi gari a ce mijina/matata ba ya/ba ta duniya?
Ma’aurata na iya kara wasu tambayoyin da s**a dace da yanayinsu.
2. Gyaran Fuska
Amsa wadancan tambayoyi da ke sama zai ba ma’aurata hoton irin yanayin da soyayyarsu take, zai sa su fahimci matsalolin da s**a cushe magudanar soyayyarsu; don haka sai su sami takarda su rubuta dukkan inda suke ganin akwai wata matsala, su binciko abin da ke haifar da wannan matsala sannan su yi nazarin hanyar da suke ganin zai kawar masu da wannan matsala; in matsalar daya daga cikinsu ke haifar da ita, sai ya yi aniyar yin dukkan kokari don ganin ya kawar da wannan matsala; in kuwa dukansu ne ke da hannu cikin matsalar, sai su yi dukkan kokarin magance wannan matsala.
3. Hadaka Soyayya
Bayan ma’aurata sun gano matsalolin da s**a cushe magudanar soyayyarsu kuma sun magance wannan matsala, daga nan sai su yi kokarin yin abubuwan da za su hadaka soyayyarsu; ta kara yawa da inganci. Ta hanyar gano sababbin hanyoyin dadadawa da faranta wa juna rai; ta hanyar yin kokarin kara yawan lokacin kasancewa tare ba wai dole sai lokacin barci kadai ba; ta hanyar yin sabon dashen kauna cikin zuciyar juna; ta hanyar yawan sabunta kaunatayyarsu da soyayyarsu a-kai-a-kai; ta hanyar cakuda so da kauna da romansiyya cikin ibadar aurensu; da duk wasu hanyoyin da suke ganin za su hadaka tare da kara rayar da soyayyarsu cikin zuciyar juna; insha Allah bayani na zuwa kan kyawawan hanyoyin da ma’aurata za su bi wajen bayyanar da soyayya ga junansu.
Ma’aurata sai a mike tsaye, a kuma dage a yi dukkan kokarin da ya kamata don yin gyara ga muhallin auratayya; kar a yi ta zaman hakuri ana rayuwar auratayya kamar ba soyayya; duk wani abu da ke hana bayyanar da soyayyar ga juna ya kamata a yi fatali da shi domin ba amfanin da yake ga rayauwar aurensu, kuma ko da yana yi din, tabbas bayyanar da soyayyar ga juna tafi zama alfanu. Ku tuna, rayukanmu duka ba a hannunmu suke ba, ba wanda ya san ranar mutuwarsa, mutuwa na iya dauke abokin aurenku, sannan ne za ku rika da na sani na yi masa kaza ko na ce mata kaza? Da fatan Allah, wanda zuciyoyin dukkan mai rai ke karkashin ikonSa, wanda ke shamakancewa tsakanin mutum da zuciyarsa, ya cika zuciyar dukkanin ma’aurata da so, kauna, kulawa da sha’awar juna, amin.
Zan dakata a nan, sai sati na gaba insha Allah. Da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koda yaushe, amin.
💞 DOMINKI NE DA MIJINKI 👫 // 9
(Kashi na Tara):
ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ
ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﻭﺳﻠﻢ
Allah sarki, yaudin nan muke tsallake mace ta gari zuwa miji na qwarai,kwance-tashi ba wahala, sai dai shawarata da ke,
ki sani ba zai ta6a yiwuwa ki yi addini da jahilci ba, mace mai addini tana tare da iliminta ba jahila ba ce, duk yadda mijinki ya kai da ilimi ba zai sa ki shiga aljanna ba sai in kin yi aikin da zai kai ki aljannar.
Kamar yadda shi ma yake yi, kowa ta kansa yake yi a lahira, wannan ne ma ya sa matar Annabi Lutu AS ta shiga wuta ، matar Fir'auna LA ta shiga aljanna, kenan
duk ilimin mijinki na sa ne ke ma ki nemi na ki, in Allah ya qaddara rasuwarsa kina da saninki, haka duk ibadarsa ta sa ce kema ki yi ta ki.
Tabbas Annabi (S.A.W) ya saka wa mata rana guda da ya riqa koyar da su, kuma
Allah (S.W.T) da KanSa ya ce:
ﻭﺍﺫﻛﺮﻥ ﻣﺎ ﻳﺘﻠﻰ ﻓﻲ ﺑﻴﻮﺗﻜﻦ ﻣﻦ ﺁﻳﺎﺕ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺍﻟﺤﻜﻤﺔ
Ku (mata ku) yi darasin abin da ake karantawa a dakunanku na ayoyin Allah
da hikima (hadisi).
Ahzab 34.
Wajibin mace ne ta nemi ilimin da zai kai ta aljanna, namiji bai da hujjar da zai ajiye ta cikin jahilci, ko dai ya koyar da ita, ko ya kawo wanda zai koya mata ko ya bar ta ta tafi in da za ta koya,idan Allah ya so bawansa namiji ko mace yakan sanar da shi addininsa ne, don haka Allah (S.W.T) ya yi tambaya:
ﻗﻞ ﻫﻞ ﻳﺴﺘﻮﻱ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻳﻌﻠﻤﻮﻥ ﻭﺍﻟﺬﻳﻦ ﻻ ﻳﻌﻠﻤﻮﻥ
"Ka ce shin wadan da suke da ilimi za su yi dai dai da marasa ilimi?
Zumur 9.
Don buga misali Annabi ya bar mu da mu kar6i rabin addininmu a wajen iyalinsa, da a ce ba ta da shi da hakan bai faru ba, Subhanallah!
A yau matan malamai sun fi kowa jahilci sai dai Allah ya gyara, an ce: "Makarantar mata haramun ce, kai ba ka koyar da ita ba, ba ka bar ta ta je ta koya ba, ba ka kawo mata mai koyar da ita ba, kuma kana son biyayya irin ta addini, da ibada irin ta masana, tana da hakki a kanka yalla6ai ka ji tsoron Allah ka sanar da ita addininta.
Ke kuma ki riqi 'ya'yanki, ki koya musu fadin gaskiya da ikhlasi a cikin ayyukansu, kar ki yi sakaci in kika ga danki ya fara cin abinci bai ce bismillahi ba, ko shiga daki ba sallama, ko daukan abin da ba ai masa izini ba koda kuwa 'yan uwansa sun gaya masa cewa na sa ne, ki koya musu tsafta.
'Yar ki ta koyi ayyukan gida tun tana qarama har girmanta, kar ki yarda mata
da barcin rana bayan akwai aiki a gida, banda zagi a gaban yaranki, ko mummunar magana, in kika ji a bakin wani cikinsu ko da sau Daya ne ki dauki
mataki, ki koya musu yi wa iyayensu addu'a kowanne lokaci, ki nuna musu
darajar babansu da matsayinsa.
Ki koya wa 'yarki mace tun tana qarama son aikin gida, ki sabar mata da kwalliya, ki ladabtar da ita bisa tafarki, ki koya
mata rufe kwalliya a waje da dadin magana, ki riqa nuna mata yadda k**e yi wa maigidanki don ya zama mata darasi.
Ki riqa gaya wa danki kyawawan halayen mahaifinsa tare da fatar cewa zai fishi a nan gaba, duk wanda ya yi abin qwarai a yaba masa wanda ya yi kuskure a ladabtar da shi.
Ki koya musu son addini da kamewa, da wadatar zuci, ki nunawa 'ya'yanki son addini, mace ta tsaya a matsayinta namiji shi ma haka, ki koyar da su son karatun addini da riqo dashi, da matsayin imani
da Ikhlasi.
INA TAYA KI MURNAR ZAMA MACE TA GARI.
Zamu ci gaba insha Allah.
Rubutawa: Baban Manar.
Gabatarwa: Abu-Unaisa.
TAMBAYA TA GA SAMARIN ZAMANI MASU GURIN YIN AURE
Dan uwa mai gurin yin auren farin ma.ana (saurayi) ko ka taba yin nazarin waddanan tambayoyi gabanin ka samu kan ka gaban yariyar da kake muradin aura domin shifa aure rayuwa ce abadiya wadda babu ranar rabuwa in kowa hakane toh Dan samari akwai bukatar kayi la,akari ko kuma nazarin wadanan tambayoyi :
1.minene aure?
2.minene ya kamata na mallaka gabanin na nemi mata?
3.wace mace ce zan nema matsayin mata ta?
4. Ya ya yakamata nayi zamatakewa da matar aure na?
Hakika amsar waddanan tambayoyin Nada matukar muhimmaci ga matasa masu gurin aure bawai ga matasa maza kawai ba ne kawai manufata ba har ga matasa mata Allah yayi mana rabon da abukai auratayya na kirki a gidaje auren mu
30/11/2014
Wannan shine namiji na hakika hadimi ga iyalan sa a kowane irin hali
Don Allah ka/ki taimaka da fadi wasu abubuwa uku wadda indo matar aure tayiwa mijin ta su darajar ta zai daga a wurin miji ba don komai ba sai don su zamo maka ko maki sadaka domin Annabi rahama s.a.w yace kyaukyawan zance ma sadaka ne .Allah ka taimake mu ka raya mana rayuwar da zamantakewar auren MU
lokaci yayi da ya kamata mu natsu muyi amfani da kaifin basira muyi tunani irin matsalolin da rayuwar aure ki fuskata a wannan zamani a tsakanin matasa ma aurata da yawa zaka ga ayi aure cikin nishadi da masha,a da kuma gamsashiyar soyaya a tsakanin samari da yan mata amma cikin dan kakkane lokaci zaga an rabu uwa kutuwar kaka manya ko kuma a gaban hukuma cikin barazana da cin mutunci juna sabanin iyayen mu na da da keyin aure bada soyayya ba da fahimta juna kamar mu ba amma sai suyi rayuwar aure fiye da shekara talatin lafiya lau in ma Allah ya kawo rabuwa za,a rabu ne sallaman sallaman ba cin mutunci ko zuwa gaban hukuma.batare da tsawaitawa ba yan uwa matasa maza da mata don Allah Ina neman ku bani hannun taimako a wannan dandali domin murika zakulo matsalolin nan daya bayan daya domin mu nemi mafita akan su domin hanya rahama tana iya fitowa ko ina
AMSA TAMBAYAR NAN DOMIN MU LURANDA WASU AKAN MATSALAR
1.Meye ya burgeka/ki da matar/mijin da zaku aure ko kuma kuka aura?
2.mutuwar aure sai kara yaw a yake yi musamman a kasar Hausa a tunanin Ku me ye mafita?
3.meye yan mace ya kamata ta lura da shi kamin ta amince wani ya aure ta
Domin niman shawara ko bada shawara ko neman makamar wata matsala da ta shafi aure ko neman aure sai a ayi add din ADMIN akan whatsapp chat da wannan number 08082121789 ga masu amfani da whatsapp
INA MAFITA IDAN KECE MATAR YAYA ZAKI YI?Hamida ta shiga bandaki da zummar yin bayan gida ta jiyo muryar mijinta daga kofar gida, ta tagar bandakin suna hira da abokinsa yana fadin."Kasan Allah Sale talauci kawai ya sanya nake zaune da Hamida amman duk randa nayi kudi na rantse da Allah saki uku cas zan mata."Sale ya fashe da dariya yana fadin "Kai kasimu duk irin biyayyar da Hamida ke maka, da jure talaucin nan naka kamar beran masallaci kace idan kai kudi sakin ta zaka yi'Kasimu ya fashe da dariya yana fadin " Ato ai akwai matan kudi na sanyawa a gaban mota, farare kalar labarawa, kai idan nai kudi naci gaba da zama da ita ai motsi kadan gori zata yi mini, gwara ta tafi can naci arzikina cikin kwanciyar hankali.''To yaran fa yaya zaka yi da su?'Haba malam ana maka maganar nayi kudi kana zancen banza baka san masu aiki zan daukar wa kowa ba....Hamida data yunkura zata hau kan shadda sai taji bayan gidan gabadaya ya koma, ta futo a fusace ta fara tattara kaya.Kasimu ya shigo gida yaga Hamida na tattara kaya ya fara binta yana magiya da tambayar abin da yayi ta masa banza, sai da ta kammala hada kayanta ta nufi kofa tace."Kai sai kayi kudi zaka sake ni, ni kuwa ina da damar auran mai kudi don haka idan ka shirya sai ka bini da takaddata gidan mu, yaran kuma ka samar musu masu aiki.' kasimu ya dafe kai cike da fargaba ashe taji hirar su, cikin tashin hankali yake fadin "Na shiga uku yanzu yaya zan yi da wannan baranbaramar da nayi??
Click here to claim your Sponsored Listing.
Location
Category
Contact the school
Website
Address
Birnin Kebbi
Birnin-Kebbi
23401