MALAM ABU INANI TV

MALAM ABU INANI TV

Share

Karantarwa fadakarwa tinatarwa karfafawa akan kulawa da addeenin musulumci koyida hadisin manzon Alla

Photos from MALAM ABU INANI TV's post 14/04/2024

JAKADAN HADIN KAI TSAKANIN MUSULMI.

Idan ka killace zuciyarka daga cewa, duk wanda ya cutar da mu, duk wani da ya zalince mu, duk wanda ya aibata mu, duk wanda ya yanke alaka da mu, to ba zamu bashi wani gurbi na maslaha da sulhu ba cikin zukatanmu ba, to lallai babu shakka wannan tunani ba Musulmar tunani ba ce face akasinta.

Dayawa wadanda s**a cutar, s**a zalinta da kuma aibata Musulmi da farko (Zamanin ANNABI S.A.W), sun dawo sun taimaki Musulmi da Musulunci wasun su ma sun kasance wadanda ALLAH ya danka fatahin bude biranen Kaf*rci a hannunsu, domin shi ALLAH shi yake jujjuya zukatan bayinsa, yakan mayar da makiyi ya dawo masoyi, kuma ya kan mayar da masoyi ya dawo makiyi. Ba mamaki shi yasa a Hadisin Tirmizi da Abu-Hurairata ya ruwato ANNABI (S.A.W) ke cewa:

أَحْبِبْ حَبِيبَكَ هَوْنًا مَا عَسَى أَنْ يَكُونَ بَغِيضَكَ يَوْمًا مَا وَأَبْغِضْ بَغِيضَكَ هَوْنًا مَا عَسَى أَنْ يَكُونَ حَبِيبَكَ يَوْمًا مَا.

Ma'ana: Ka so Masoyinka tsakatsakiya, domin mai yiwuwa ne wata rana ya zamo makiyinka, hakanan ka ki makiyinka tsaka-tsakyiya, mai yiwuwa ne wata rana ya zamo masoyinka.

Babu shakka wannan aikin Tajdidi ne salon yadda Maulanmu Sheikh Ibrahim Inyass (R.T.A) ya tafiyar da rayuwarsa, haka ya kasance mai mu'amalantar masoya da makiya cikin kyautatawa, karshe har ya ribato dubban zukata zuwa soyayya.

ALLAH YA KARA DAFAWA YA IMAM YA KULA DA AL'AMARINKA.

Prof. Ibrahim Maqari (H)

ALHAMDULILLAH.

08/04/2024
Want your school to be the top-listed School/college in Birnin-Kebbi?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Telephone

Website

Address


Dukku Road Birnin Kebbi
Birnin-Kebbi
3322