Abukhadeejahcenterforonlineislamicstudies

Abukhadeejahcenterforonlineislamicstudies An Islamic online school

06/09/2026

Assalam alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu

INNĀ LILLĀHI WA INNĀ ILAIHI RĀJI‘ŪN
​إنَّ لِلَّهِ مَا أَخَذَ وَلَهُ مَا أَعْطَى وَكُلُّ شَيْءٍ عِنْدَهُ بِأَجَلٍ مُسَمًّى... فَلْنَصْبِرْ وَلْنَحْتَسِبْ 😭😭
​Cikin alhini, jijjiga, da mika al'amari ga Allah, muke sanar da rasuwar DR. MURTALA (ABU KHADEEJAH).

​Shi ne me wannan page din kuma CEO na Abu-khadeejah Global Ventures

​Hakika rashin Dr. Murtala babban giɓi ne da zai wuya a cike shi. Mun rasa dan uwa, jagora, gani-kashe-nin addini, kuma jajirtaccen mutum wanda ya sadakar da rayuwarsa wajen ciyar da al'amuran Musulunci gaba.
​Addu'armu ga Marigayi:
​Gafara da Rahama: Ya Allah! Ka gafarta wa Dr. Murtala (Abu Khadeejah), Ka jiƙansa, Ka yafe masa kura-kuransa. Ka haskaka kabarinsa, Ka yalwata masa shi, Ka sanya shi ya zama lambu daga cikin lambunan Aljannar Firdausi.
​Sakamako: Ya Allah! Ka sakatara shi tare da bayinka salihai, Ka karbi dukkan ayyukansa na kwarai.
​Rokon Adalci da Kariya:
​Ya Allah! Ka bayyana mana gaskiyar abin da ya faru, Ka tona asirin duk wanda ya aikata wannan ta'addanci ko ya taimaka wajen aikata shi.
​Ya Allah! Ka yi hukunci tsakaninmu da waɗannan azzalumai, Ka rusa makircinsu, Ka tabbatar da adalci, Ka kuma kare sauran 'yan uwanmu da shugabanninmu daga dukkan sharri.
​Muna rokon Allah Maɗaukakin Sarki Ya ba iyalansa, malamansa, dalibansa, da dukkan al'umma hakuri da juriyar jure wannan babban rashi.
​Allahumma a’jurnā fī muṣībatinā wakhluf lanā khayran minhā.
​Rahmatullahi alaihi rahmatan wasi'ah. 🤲😭🤲

18/12/2024

*ABU-KHADEEJAH CENTRE FOR ISLAMIC STUDIES*
*ABU-KHADEEJAH FOUNDATION FOR TA'ALIM DA'AWAH AND CHARITY*
Wannan bangare na sanarda mutane da daliban ilimi sunada damar da zasuzo suyi bajakolin basirar da Allah ya basu wurin amfanarda Al-ummah.
Kuzo mu baku dama kuyi rubuce rubuce na bincike, zamu dauki nauyi InshaAllah. Qofa a bude take ga duk me son bada wannan Gudummawar Kuma muna Kira gareku kuzo kuyi amfani da damar lokacinku.
Muna addua Allah ya karba mana.
Kowa ze iya bada tashi gudummawa Don cigaban addininmu na musulunci.
Idan kana sha'awa zamu qarfafaka ta kowace hanya InshaAllah harma da shawarwari da Hanyoyin samun nasara har ka kammala. Dan bada gudummawar lokacinka, ko rubutunka, ko neman fayyataccen bayani ko bada shawararka, ko Kuma wata gudummawa ta musamman, ko sauqaqemana wata hanya, ko daukar nauyin wasu ababe aciki, ko bada tallafi ga wannan bangare, seka tuntubemu a 08067080655.
Allah ya shigemana gaba...

*Dr. Abu-khadeejah,*
*Director.*
18/12/2024

02/03/2024

*ABU-KHADEEJAH COMPANY*

*Gudummawar Mu ga Al-ummah ta Ramadan*
1. Mun sauqaqa magungunanmu na Ulcer da Hijaamah
2. Zamu baku dama ku dingayin tambayoyi muna baku amsa akan abunda ya shafi kowace rashin lapiya, musamman matsalar ulcer wacce ke hana mutane dayawa daukan azumi tareda baku shawarwari dakuma hanyoyin hada maganinku da kanku a gida maras illa natural.
3. Zamufi baiwa wanda s**a shiga group fifiko da muhimmanci kuma wanda suke participating acikin group din.
4. Yi magana da Lambar centre dan shiga group din, kyauta ne 08067080655.
5. ku yada wannan aikin Alkhairi danyin tarayya damu acikin Lada.
*Daukar Nauyi:*
Murtala Muhammad Imam (Dr. Abu-khadeejah), _Shugaban cibiyar;_
*ABU-KHADEEJAH CENTRE FOR HERBAL MEDICAL STUDY AND THERAPHY*
08067080655-0808 577 2041

_*Treat urself with the cure of nature*_

"Operation Feed the Poor" An opportunity to earn immense rewards from Allah by helping those in need. Join us in this no...
31/08/2023

"Operation Feed the Poor" An opportunity to earn immense rewards from Allah by helping those in need. Join us in this noble cause and experience the joy of giving.

Every day, countless individuals go to bed hungry, but together, we can change that. With "Operation Feed the Poor," your contributions will directly support food programs for those who need it most.

By donating to "Operation Feed the Poor," you not only alleviate hunger but also earn blessings and rewards from Allah. This is your chance to make a real impact and be a source of hope for the less fortunate.

Remember, charity is not just about giving money; it's about making a difference in someone's life. Join us today and let's work together to create a world where no one goes to bed hungry.

06/08/2023

*MADARASATU MARKAZIL KADI LADAN ISLAMIYYAH*
Ke gabatarda: 1. DAURAH
Littafi: *Takaitaccen bayani da tsokaci akan jinin mata guda 3.*
Wallafar: *Murtala Muhammad Imam.* 2. MUHADARAH
A. *Cutar sanyi ko infection, Abubuwanda ke kawo cutar, matsalolinda take haddasawa dakuma maganinta.*
B. *ciwon maara ga mata, Abubuwanda ke kawo cutar dakuma hanyoyin magance su duka inshaAllah*
Mai Gabatarwa: *Dr. Abu-khadeejah, Murtala Muhammad Imam; CEO ABU-KHADEEJAH COMPANY(08063053652).*
*Ta'aliyqi:* Ustaz Mubarak.
*Rana:* Lahadi 05/08/2023 InshaAllah.
*Lokaci:* 10:10am
*Wuri:* Harabar makarantar dake bayan Mobile Area, Birnin-kebbi.
Wannan karatu ne na mata zallah, kowace mace zata iya zuwa domin ta amfana. Allah ya mana Jagorah.
Assalamu Alaikum

An Islamic online school

24/07/2023

*ABU-KHADEEJAH CENTRE FOR ONLINE ISLAMIC STUDIES(AKCOIS) 08067080655*
*Fara karatun littafin Aqeedatul Islamiyyah minal kitaabi was-sunnatis-saheehah, Juz'i na 3*
Assalamu Alaikum.
Muna sanarda daliban makaranta cewa karatun littafin ze soma kamar yadda muka bada sanarwa abaya.
Karatunku ze dinga zuwa ranar Alhamis ta kowane sati inshaAllah. Zaku fara Alhamis me zuwa inshaAllah qarfe 9pm.

Dr. Abu-khadeejah,
*Director*
08063053652
Mon, 24/7/2023

An Islamic online school

28/06/2023

Allahu Akbar, Allahu Akbar, La Ilaha Illal Lahu, Allahu Akbar, Allahu Akbar, Wa LilLahil Hamd.
Allahu Akbar Kabira, Walhamdu LilLahi Kathira, Wa Subhanillah Bukratau Wa Asila.

I wish you and your family a joyous Sallah celebration.

TAQABBALALLAHU MINNA WA MINKUM

31/05/2023

Address

Birnin Kebbi
Birnin-Kebbi
860101

Telephone

+2349078687922

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Abukhadeejahcenterforonlineislamicstudies posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share