Mujamma'u As'habul Kahfi Warraqeem Bauchi

Mujamma'u As'habul Kahfi Warraqeem Bauchi Ina alfahari da Shaykh Dr. Abduljabbar Kabara.

14/08/2026

Lale marhaba da watan watanni🥰😍🙏🎊

Duk wanda suke ganin cewa wannan ɓacin ran da nake yi game da wasu Hadisai bai dace ba, da sun ga abinda na gani, da fus...
13/08/2026

Duk wanda suke ganin cewa wannan ɓacin ran da nake yi game da wasu Hadisai bai dace ba, da sun ga abinda na gani, da fushinsu ya fi nawa yawa.

—Sheikh Abduljabbar Kabara

Ana Neman Taimakon Al’umma Wajen Gano ’Yan Uwan Wannan Dattijo da Aka Tsinci a Bauchi.Daga Albarka RadioAn tsinci wani d...
09/08/2026

Ana Neman Taimakon Al’umma Wajen Gano ’Yan Uwan Wannan Dattijo da Aka Tsinci a Bauchi.

Daga Albarka Radio

An tsinci wani dattijo mai suna Adamu a cikin garin Bauchi, inda mambobin ƙungiyar tsaron sa-kai s**a same shi a ranar Asabar, 8 ga watan Agusta, 2026.

A halin yanzu, dattijon yana cikin ɗimuwa, kuma yana ambaton sunayen garuruwa daban-daban, ciki har da Kano da Maiduguri.

Ana roƙon duk wanda ya gane shi ko ya san ’yan uwansa da ya tuntubi lambar wayar da za mu saka a sashen sharhi (comment section), domin samun ƙarin bayani.

Allah yasa a dace ameen thumma Ameen.

Ministan Al'adu na Syria, Muh'd Yasin Saleh, Ya Karrama Imam Sheikh Nasir Al-MalikiMinistan Al'adu na ƙasar Syria, Muh'd...
08/08/2026

Ministan Al'adu na Syria, Muh'd Yasin Saleh, Ya Karrama Imam Sheikh Nasir Al-Maliki

Ministan Al'adu na ƙasar Syria, Muh'd Yasin Saleh, ya karrama ɗaya daga cikin matasan malaman Ɗariƙa, Imam Sheikh Nasir Al-Maliki, da lambar girmamawa.

An gudanar da bikin karramawar ne a yayin wani babban taron masana Adabin Larabci na Duniya, wanda gwamnatin ƙasar Syria ta shirya, tare da halartar masana da manyan baƙi daga sassa daban-daban.

Wannan karramawa na nuna irin girmamawa da ake bai wa gudummawar malamai da masana wajen bunƙasa ilimi da Adabin Larabci, tare da ƙarfafa hulɗa tsakanin masana daga ƙasashe daban-daban.

Allah Ya ƙara masa nasara da ɗaukaka, Ya shirya masa dukkan lamuransa, Ya kuma dawo mana da shi gida lafiya da aminci, saboda girman Shugabanmu Annabi Muhammad (SAW). Āmīn.

View: Tijjaniyya Media Team.

Soyayyar Manzon Allah (SAW) ita ce fitilar da ke haskaka zukatan muminai.—Sheikh Dahiru Usman Bauchi (rh).
05/08/2026

Soyayyar Manzon Allah (SAW) ita ce fitilar da ke haskaka zukatan muminai.

—Sheikh Dahiru Usman Bauchi (rh).

Duk abinda aka gina a kan Hujja, ba na jin tsoron abinda za'a kira ni da shi. Saboda haka, ba wani dalili da zai sa a ri...
03/08/2026

Duk abinda aka gina a kan Hujja, ba na jin tsoron abinda za'a kira ni da shi. Saboda haka, ba wani dalili da zai sa a riƙa tsorata ni da kalmar Shi'anci.

—Sheikh Abduljabbar H.

Allah ya baka lafiya ya kiyaye gaba.
02/08/2026

Allah ya baka lafiya ya kiyaye gaba.

Innalillahi wainnailihi rajiun Usman Aljabbari nagamu da hatsari a wannan Daren Amma da sau qai ina baran addu'o'in ku 😭😭😭🙏
Usman Aljabbari Algwambawi

Duk malamin da kuka ji yana cewa ina rusa addini, to abincin sa na rusa. KO WAYE—Sheikh Abduljabbar Kabara
02/08/2026

Duk malamin da kuka ji yana cewa ina rusa addini, to abincin sa na rusa. KO WAYE

—Sheikh Abduljabbar Kabara

A da ina cewa ni ba ɗan Shi'a ba ne. Amma bayan na yi bincike mai zurfi, sai na gano shi'a tafi Sunnah yawan hujjoji. Tu...
02/08/2026

A da ina cewa ni ba ɗan Shi'a ba ne. Amma bayan na yi bincike mai zurfi, sai na gano shi'a tafi Sunnah yawan hujjoji. Tun daga lokacin, na daina cewa ni ba ɗan Shi'a ba ne.

—Sheikh Abduljabbar Kabara

Idan kuka ce lamarin Imam Husaini (AS) na 'yan Shi'a ne, to kuna nuna Ahlul Bayt 'yan Shi'a ne, har Husaini (AS).—Malam ...
01/08/2026

Idan kuka ce lamarin Imam Husaini (AS) na 'yan Shi'a ne, to kuna nuna Ahlul Bayt 'yan Shi'a ne, har Husaini (AS).

—Malam Uzairu Badamasi

Address

Railwey Road
Bauchi
RAHAMA

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Mujamma'u As'habul Kahfi Warraqeem Bauchi posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category