An-Noor Media TV

An-Noor Media TV Mun bude wannan channel ne domin kawo muku sahihan labarai masu inganci, tare da nishaɗan tarwa, faɗakarwa, ilmantarwa.

🌹🌺 SANARWA TA MUSAMMAN 🌺🌹✨ Babban Albishir Ga Al'ummar Musulmi! ✨Ana gayyatar ɗaukacin al'ummar Musulmi maza da mata zuw...
15/06/2026

🌹🌺 SANARWA TA MUSAMMAN 🌺🌹

✨ Babban Albishir Ga Al'ummar Musulmi! ✨

Ana gayyatar ɗaukacin al'ummar Musulmi maza da mata zuwa wani muhimmin Karatun Daura da za a gabatar kan Rayuwa da Gudunmawar Sheikh Dahiru Usman Bauchi (RTA).

🌷 Ranakun Gudanarwa: 🌷

🌸 Laraba, 17/06/2026
🌸 Asabar, 20/06/2026
🌸 Lahadi, 21/06/2026

🕙 Lokaci: 10:00 na safe zuwa 11:00 na safe.

🌼 Wurin Taro:
📍 Sheikh Dahiru Usman Bauchi Islamic Center
🎙️ Mai Gabatarwa:

🌹 Dr. Fatihu Sheikh Dahiru Usman

💐 Wannan wata dama ce ta ƙara sani game da tarihin rayuwa, ayyuka da gudunmawar wannan babban malami mai albarka. Kada a bari a ba da labari, ku zo ku amfana kai tsaye.

🤲 Allah Ya ba mu ikon halarta, Ya sanya albarka da amfanin abin da za a koya. Ameen Ya Rabbal Alameen. 🤲

🌷🌹 Kowa ya gayyaci ɗan'uwa, aboki da maƙwabci domin samun wannan babban alkhairi. 🌹🌷

✍️ Sautul-Faidha Media (Safsom-Media) 🌺📚🌺

🌙✨ JADAWALIN KARATUTTUKAN MALAM TIJJANIYYA – RAMADAN TAFSEER 2026 ✨🌙🌸 Cikin haɗin gwiwar 🌸🎙 Kamfanin Sautul-Faidha (SAFS...
11/02/2026

🌙✨ JADAWALIN KARATUTTUKAN MALAM TIJJANIYYA – RAMADAN TAFSEER 2026 ✨🌙

🌸 Cikin haɗin gwiwar 🌸
🎙 Kamfanin Sautul-Faidha (SAFSOM)
🤝 tare da
📺 An-Noor Media TV

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin ƙai.
Muna farin cikin sanar da al’umma baki ɗaya jadawalin Karatuttukan Malam Tijjaniyya na wannan shekarar Ramadan Tafseer 2026, waɗanda za a rika gabatarwa a kullum In Sha Allah.

🌺 GA MALAMAN DA ZA A SAMU: 🌺

001. Maulana Sheikh Ibrahim Inyass — Old

002. Maulana Sheikh Taheer Usman Bauchi — Old

003. Maulana Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al-Hussaimin — New

004. Chief Imam National Mosque Abuja, Prof. Ibrahim Ahmad Maqari Sa’id — New

005. Prof. Nasidi Gwauron Dutse Kano — New

006. Prof. Umar Sani Fagge Kano — New

007. Prof. Halliru Maraya Kaduna — New

008. Dr. Kabeer Sheikh Aliyu Tsafe Bauchi — New

009. Dr. Basheer Sheikh Dahiru Usman — New

010. Amb. Dr. Fatihu Sheikh Dahiru Usman — New

011. Dr. Basheer Barhama Gombe — New

012. Sheikh Tijjani Yaya Malam Sheikh Dahiru Usman — New

013. Sheikh Kabeer Ya’aqub Al-Arabi — New

014. Sheikh Masur Imam Kaduna — New

015. Sheikh Sabi’u Gommaja Kano — Old

016. Sheikh Alramma Isma’il Muhammad Bajoga Bauchi — New

017. Sheikh Nazifi Al’ƙarmawy Kano — New

018. Sheikh Haris Salihu Jos — New

019. Sheikh Mubashshir Sheikh Dahiru Usman Bauchi — New

020. Sheikh Hassan Sheikh Dahiru Usman — New

021. Sheikh Junaidu Abubakar Siddiq — New

022. Sheikh Amb. Naseer Sheikh Ado Musa T/Balewa — New

023. Sheikh Burhanuddeen Sheikh Al’Ameen Malam Goje — New

024. Sheikh Abul-Fathi Sani Attijany (Zakin Faidha) — New

025. Sheikh Alramma Sun-Sunusi Adam Bauchi — New

026. Sheikh Sunusi Dan Malam Godal Zamfara — New

027. Sheikh Mustapha Adinga Abuja — New

028. Sheikh Muneer Adam Koza — New

029. Sheikh Al’abbas Sadaukin Faidha Kano — New

030. Sayyed Akilu Abubakar Siddiq Bauchi

🌷 Za ku iya samun mu a:
Facebook | WhatsApp | Instagram | Telegram Channel | TikTok

🤲 Allah Ya ba mu sa’a, Ya nuna mana Ramadan muna cikin koshin lafiya da tsawon kwana, Ya kuma saka mu cikin bayinsa na gaskiya masu cin albarkar Annabi ﷺ. Ameen.

✨🌹 Ku kasance tare da mu a Ramadan 2026 🌹✨

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN:Allah Ya yi wa fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, rasuw...
27/11/2025

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN:

Allah Ya yi wa fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, rasuwa. Marigayin ya kasance ɗaya daga cikin sanannun malamai masu zurfin ilimi, hikima da tasiri a fadin Najeriya da ma wasu ƙasashen waje.

Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya yi fice wajen yaɗa ilimin addini, gyaran tarbiyya, da jawo hankalin al’umma zuwa zaman lafiya, adalci da tsoron Allah. Kalamansa sun kasance cike da nasihohi masu taushi da faɗakarwa, tare da bin sahihin tafarkin Annabi (SAW) wajen isar da sakon addini.

Marigayin ya rayu da sadaukarwa wajen gina al’umma, ya ilmantar da dubban dalibai waɗanda s**a yada iliminsa a sassa daban-daban na duniya.

Allah Ya jikansa, Ya gafarta masa, Ya sanya kabarinsa cikin fadawar Aljanna.
Allah Ya ba iyalansa, almajiransa, mabiyansa da dukkan al’ummar Musulmi hakurin jure wannan babban rashi. Amin.

DA DUMI-DUMI:Sheikh Usman Dahiru Bauchi Ya Yi Kira Ga Yin Addu’o’i Kan Barazanar da Amurka Ta Yi wa NajeriyaAn samu raho...
22/11/2025

DA DUMI-DUMI:

Sheikh Usman Dahiru Bauchi Ya Yi Kira Ga Yin Addu’o’i Kan Barazanar da Amurka Ta Yi wa Najeriya

An samu rahoton cewa Maulana Sheikh Usman Dahiru Bauchi (RTA), ta bakin wani daga cikin wakilansa, ya yi kira ga Musulmin Najeriya da su tsunduma cikin addu’o’i, bayan jita-jitar barazanar da ake dangantawa da tsohon Shugaban Amurka, Donald Trump, kan Najeriya.

A cikin sakon, an bukaci Musulmi su yi dogon istighfari da addu’o’i domin neman kariya da sauƙi ga kasa. Daga cikin abin da aka sanar akwai:

Karatun Suratul Fātiha sau ɗaya

Istighfari 1000

Salatul Fātihi 1000

“Ya Latīfu” 1000

Haka kuma, an bukaci manyan Zawiyoyi da Tsangayu a fadin ƙasar su gudanar da addu’o’i masu yawa, ciki har da:

Istighfari 1,000,000

Salatul Fātihi 1,000,000

“Ya Latīfu” 1,000,000

An ce manufar wannan kira ita ce neman tsare kasa, da rokon Allah ya kawar da duk wata fitina ko barazana, tare da sauƙaƙa al’amuran Najeriya da al’ummar ta.

Sakon ya fito ne a matsayin gargadi da jan hankali kan halin da ake ciki, tare da kira ga musulmi su kara dagewa a ibada da yin addu’a domin zaman lafiya.

DA ƊUMI-ƊUMI: Sama da Mutane Miliyan Uku Sun Halarci Yaumul Rasul a BauchiRahotanni daga Bauchi sun tabbatar da cewa sam...
15/11/2025

DA ƊUMI-ƊUMI: Sama da Mutane Miliyan Uku Sun Halarci Yaumul Rasul a Bauchi

Rahotanni daga Bauchi sun tabbatar da cewa sama da mutane miliyan uku sun halarci zagayen Yaumul Rasul na bana. Masu shirya taron sun ce jama’a sun fito daga sassa daban-daban na Najeriya da ƙasashen makwabta. An gudanar da wa’azi, salati da addu’o’i domin neman rahamar Allah da zaman lafiya a ƙasa.

24/10/2025

🟢🕋 AN-NOOR MEDIA TV (Hasken Al’umma)
Gidan Talabijin Mai Albarka Da Ke Haske Al’umma Da Gaskiya!

A wannan zamani da labarai suke yaduwa cikin sauri, An-Noor Media TV ya taso domin kawo sahihan da ingantattun labarai, tare da fadakarwa, ilmantarwa, da nishaɗantarwa ga al’umma.

Mun buɗe wannan gidan talabijin ne domin gina al’umma bisa gaskiya da adalci, tare da ba ku damar samun bayanai na gaskiya ba tare da son rai ba.

🕊️ Ku kasance tare damu koda yaushe!
Domin kada ku rasa sabbin shirye-shiryenmu, ku bi mu a:

📺 page: 👇👇
https://www.facebook.com/share/1S8dsH6Gvf/

📱 WhatsApp Channel: 👇👇
https://whatsapp.com/channel/0029Vb6LM6HJpe8ijPFMLA3Z

💬 Telegram Channel: 👇👇
https://t.me/annoormediatv

▶️ YouTube Channel: 👇👇
https://www.youtube.com/

Kuyi Like 👍, Follow 💚, Subscribe 🔔, da Share 🔄 domin yada hasken gaskiya zuwa ga kowa da kowa.

An-Noor Media TV — Hasken Al’umma, Murya ta Gaskiya.
“Kuɗin gaskiya baya ƙarewa, amma haskenta yana yawaita.” ✨

Address

Bauchi
740102

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when An-Noor Media TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share