Misau Online Tv

Misau Online Tv "Muryar al'umma, madubin ci gaba."

Misau Online TV kafar yaɗa labarai ce ta zamani wadda ke kawo sahihan labarai, shirye-shirye, ilimantarwa, nishaɗi da abubuwan da s**a shafi al'umma cikin sauri da inganci.

25/09/2026
Alhamdulillah Ina Sake Mika Sakon Godiya Ta Ga Allah Mai Kowa Kuma Mai Komai Daya Bani Ikon Kasancewa Tareda Wannan Comp...
14/09/2026

Alhamdulillah Ina Sake Mika Sakon Godiya Ta Ga Allah Mai Kowa Kuma Mai Komai Daya Bani Ikon Kasancewa Tareda Wannan Company Mai Albarka Na Dahir Spices Ubangiji Ya Cigaba Da Daukaka Darajar Wanann Company Mai Tarin Albarka Dahir Curry Karshen Zanche

Musa Jibrin Silver

Alhmdllh Ruwan Sama Mai Karfin Gaske Ya Sauka A Garin Misau Bayan Shafe Kwanaki Uku Ana Fita Rokon Ruwa A Garin Misau
14/09/2026

Alhmdllh

Ruwan Sama Mai Karfin Gaske Ya Sauka A Garin Misau Bayan Shafe Kwanaki Uku Ana Fita Rokon Ruwa A Garin Misau

Mafi rinjayen lakcarorin Arewacin Nijeriya sun goyi bayan tazarcen Tinubu in ji wani rahoton jaridar Daily TrustFiye da ...
14/09/2026

Mafi rinjayen lakcarorin Arewacin Nijeriya sun goyi bayan tazarcen Tinubu in ji wani rahoton jaridar Daily Trust

Fiye da manyan malaman jami’a 600 daga dukkan jami’o’in gwamnati da ke Arewacin Nijeriya sun bayyana goyon bayansu ga takarar Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu na neman wa’adi na biyu.

Goyon bayan ya kasance babban abin da taron da Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Siyasa, Ibrahim Masari, ya shirya ya mayar da hankali a kai. An kira taron ne domin bai wa malaman jami’o’in damar tattaunawa kan makomar siyasar Nijeriya.

Tawagar Shehu Kawai Karkashin State Coordinator Yusuf Inuwa Barrister Yayi Ganawa Ta Musamman Tare da Jagororin Kungiyar...
13/09/2026

Tawagar Shehu Kawai Karkashin State Coordinator Yusuf Inuwa Barrister Yayi Ganawa Ta Musamman Tare da Jagororin Kungiyar Na 20LGA Yau A Bauchi Yayin Taron Jam'iyyar PRP.

Hon. Musa Dokaji ya koma jam’iyyar APC bayan ficewarsa daga jam’iyyar PRP, tare da ɗaruruwan magoya bayansa.Komawarsa AP...
13/09/2026

Hon. Musa Dokaji ya koma jam’iyyar APC bayan ficewarsa daga jam’iyyar PRP, tare da ɗaruruwan magoya bayansa.

Komawarsa APC na zuwa ne a daidai lokacin da ake ƙara samun sauye-sauyen siyasa gabanin zaɓen 2027.

BASKO GIDA GIDA MEDICAL OUTREACH DA MOBILIZATION A AJILIA yau, 12 ga Satumba, 2026, ƙungiyar Basko Gida Gida Medical Out...
13/09/2026

BASKO GIDA GIDA MEDICAL OUTREACH DA MOBILIZATION A AJILI

A yau, 12 ga Satumba, 2026, ƙungiyar Basko Gida Gida Medical Outreach and Mobilization ta gudanar da rabon magunguna, gwaje-gwaje da duba marasa lafiya kyauta a garin Ajili, ƙarƙashin jagorancin Haj. Binta Abba Garo, mai ɗakin Hon. Basko Mangari.

A jawabinsa, Shugaban ƙungiyar, Mal. Nazeef, ya yaba matuƙa ga Hon. Abba Garo, ɗan takarar Majalisar Dokokin Jihar Bauchi mai wakiltar Chiroma District a ƙarƙashin jam’iyyar APC, tare da mai ɗakinsa Haj. Binta Abba Garo, bisa wannan kyakkyawan aikin alheri da suke gudanarwa domin tallafawa al’umma.

Shi ma Alh. Zagi Mohammed CNA, wanda ya yi jawabi a madadin amininsa Hon. Abba Garo, ya bayyana wa al’ummar Ajili cewa, “Ku ’yan gida ne tun kafin siyasa.” Ya ƙara da cewa bayan Mangari, Ajili ita ce second home dinsu, kuma dangantakarsu da al’ummar Ajili ba ta fara da siyasa ba.

Alh. Zagi ya kuma roƙi al’ummar Ajili da su ci gaba da ba su goyon baya, tare da neman alfarmar ƙuri’unsu a ranar zaɓe, idan Allah Ya kai su wannan rana.

A nata jawabin, jagorar ƙungiyar, Haj. Binta Abba Garo, ta gode wa ma’aikatan ƙungiyar bisa jajircewarsu, tare da miƙa godiya ta musamman ga al’ummar Ajili bisa kyakkyawan haɗin kai da s**a bai wa ma’aikatan, da kuma yadda s**a fito kwansu da kwarkwatarsu domin amfana da shirin.

Ta kuma roƙi al’ummar Ajili da su ma, a ranar zaɓe, su fito kwansu da kwarkwatarsu domin zaɓar jam’iyyar APC.

An kammala taron da addu’ar fatan alheri, tare da roƙon Allah Ya saka wa dukkan waɗanda s**a bayar da gudummawa da alheri, Ya kuma ƙara haɗa kan al’umma.

SANARWAR MANEMA LABARAIYAN Bauchi Ta Yi Kira da A Gudanar da Bincike Mai Zaman Kansa Kan Zarge-Zargen da S**a Shafi Sana...
13/09/2026

SANARWAR MANEMA LABARAI

YAN Bauchi Ta Yi Kira da A Gudanar da Bincike Mai Zaman Kansa Kan Zarge-Zargen da S**a Shafi Sanata Shehu Buba Umar

Ƙungiyar Youth Assembly of Nigeria (YAN), Reshen Jihar Bauchi, Ta Yi Kira ga Shugaba Tinubu da Hukumomin Tsaro da Su Tabbatar da Gaskiyar Lamarin

Ƙungiyar Youth Assembly of Nigeria (YAN), Reshen Jihar Bauchi, ƙarƙashin jagorancin Rt. Hon. Alhassan Adamu, tana kira ga Shugaban Ƙasa kuma Babban Kwamandan Rundunar Sojojin Najeriya, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, da dukkan hukumomin tsaro da bincike da abin ya shafa, da su gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa, na gaskiya da bayyane kan zarge-zargen da ake yadawa game da alaƙar Sanata Shehu Buba Umar, Sanatan da ke wakiltar Bauchi ta Kudu kuma ɗan takarar gwamnan Jihar Bauchi a zaɓen 2027 ƙarƙashin jam’iyyar Peoples Redemption Party (PRP), da matsalolin tsaro.

YAN Bauchi na ganin cewa batutuwan da s**a shafi tsaron ƙasa suna da matuƙar muhimmanci, kuma bai kamata a mayar da su batun siyasa, hasashe ko farfaganda ta kafafen yaɗa labarai ba. Ya kamata al’ummar Najeriya su san gaskiyar lamari, kuma bai kamata a hukunta ko a ayyana wani mutum a matsayin mai laifi bisa zargi kawai ba.

Saboda haka, muna yin kira cikin girmamawa ga hukumomin tsaro da bincike da s**a dace da su gudanar da cikakken bincike kan waɗannan zarge-zarge, sannan su bayyana sakamakon binciken ga al’ummar Najeriya.

Matsayinmu a bayyane yake, kuma yana bisa ƙa’idojin adalci da daidaito:

Idan bincike ya tabbatar da cewa Sanata Shehu Buba Umar ya aikata wani laifi, to ya kamata a bar shi ya fuskanci cikakken hukunci na doka, bisa tsarin shari’a da bin ƙa’idojin da s**a dace.

Idan kuma binciken ya tabbatar da cewa ba shi da wata alaƙa da laifin ko kuma ba shi da abin da zai amsa, to ya kamata a bayyana hakan ga jama’a tare da wanke sunansa.

YAN Bauchi ta yi imanin cewa bayyananniyar gaskiya da riƙon amana suna da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da amincewar jama’a ga hukumomin tsaro da tsarin dimokuraɗiyya. Barin al’umma cikin duhu game da manyan zarge-zarge na iya haifar da shakku, tashin hankali da yaɗuwar bayanan ƙarya.

Ba muna kira ne da a tsananta wa Sanata Shehu Buba ba, kuma ba mu yanke hukunci kan sakamakon wani bincike ba. Abin da kawai muke kira shi ne a tabbatar da gaskiyar lamarin ta hanyar bincike mai inganci, adalci da rashin son kai.

Saboda haka, muna kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Rundunar ’Yan Sandan Najeriya (Nigeria Police Force), Hukumar DSS, da sauran hukumomin tsaro da bincike da abin ya shafa, da su ɗauki wannan batu da muhimmanci tare da samar wa al’ummar Najeriya da sahihin sakamakon bincike mai gamsarwa.

Al’ummar Jihar Bauchi da ’yan Najeriya baki ɗaya sun cancanci gaskiya, adalci, bayyananniyar hanya da riƙon amana.

YAN Bauchi State Chapter za ta ci gaba da kasancewa mai kishin zaman lafiya, tattaunawar dimokuraɗiyya, bin doka da oda, haɗin kan ƙasa, da kare haƙƙin dimokuraɗiyya na kowane ɗan Najeriya.

Sa hannu:

Rt. Hon. Alhassan Adamu

Ambassador Youth Assembly of Nigeria (YAN)
Bauchi State Chapter

Ranar: 14 ga Satumba, 2026

Address

Bakin Kasuwa Misau LG
Bauchi

Telephone

+2349029996916

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Misau Online Tv posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category