Sautul haq islamiyya wattahafiz

Sautul haq islamiyya wattahafiz

Share

Manzon Allah S.A.W Yace : "Ban Bar Wata Fitina A Bayanaba, Wadda Take Cutar Da Mazaba, Kamar Mata ba

07/07/2026

Wani mai bibiyar shafin Eagle Radio Bauchi, Yusuf Isa Abul Ihsan, ya bayyana hakan ne a sashen sharhi ƙarƙashin wasu hotuna da shafin ya wallafa, waɗanda s**a nuna yadda ƴan ƙungiyar Triple R ke ci gaba da gudanar da taruka domin nuna goyon baya ga jam'iyyar APC.

A cewarsa, lokaci ya yi da mutane za su fara tantance bambanci tsakanin hidimar al'umma da siyasa. Ya yi ikirarin cewa wasu daga cikin fitattun ƴan Kannywood da ake ganin suna tare da jama'a a baya, a yanzu sun koma kusantar masu mulki domin biyan bukatunsu.

Ya ƙara da cewa kowa na da ƴancin bayyana ra'ayinsa da kuma goyon bayan wanda yake so, amma bai kamata a ɗauka cewa duk abin da ake yi saboda al'umma ne ba.

Yusuf Isa ya kuma buƙaci jama'a su kasance masu buɗaɗɗen ido, su rika kallon aiki da sakamakonsa, maimakon hotuna da tarukan siyasa kaɗai.

A ƙarshen sakonsa, ya ce, "Baya ganin laifinsu (Ƴan Kannywood) neman na tuwo sukeyi. Al'umma kuma ba don su ake yi ba.

20/06/2026

Wani mai bibiyar shafin Eagle Radio, Yusuf Isah Abul Ihsan, ya bayyana cewa a ganinsa, mafita mai ɗorewa ga matsalar garkuwa da mutane tana buƙatar haɗa matakan hukunta masu aikata laifi da kuma sasanta waɗanda s**a nuna shirye-shiryen ajiye makami bisa ƙa’ida.

Ya bayyana hakan ne a shashen sharhi karkashin tambayar da Eagle Radio ta gabatar mai taken: "Sulhu ko Murƙushe Masu Garkuwa Da Mutane: Wane Mataki Ya Fi Dacewa Domin Kawo Ƙarshen Matsalar a Najeriya?"

A cewarsa, inganta tsaro, samar da ayyukan yi ga matasa da tabbatar da adalci za su taimaka wajen rage tushen matsalar, yana mai jaddada cewa, abu mafi muhimmanci shi ne kare rayuka da dukiyoyin al’umma tare da gina zaman lafiya mai ɗorewa.

10/05/2026

🕌✨ 𝐌𝐀𝐃𝐑𝐀𝐒𝐀𝐓𝐔𝐋 𝐒𝐀𝐔𝐓𝐈𝐋 𝐇𝐀𝐐 𝐈𝐒𝐋𝐀𝐌𝐈𝐘𝐘𝐀 𝐖𝐀𝐓𝐓𝐀𝐇 𝐅𝐈𝐙 ✨🕌
Tudun Wadan Dan Amar B Kandahar, Bauchi
╔════════════════════╗
🌸 INVITATION CARD 🌸
╚════════════════════╝
🤝 AMDADIN OFFICIAL NA MAKARANTA
Na farin cikin gayyatar dukkan tsoffin ɗalibai da malamai zuwa wajen babban taron sada zumunta da makaranta ta shirya.
📌 Taron:
🎓 Haɗuwar Tsofaffin Ɗalibai da Malamai
📅 Rana:
Lahadi, 31 May 2026
📍 Wurin Taro:
🕌 Masjid Sautil Haq
(Masallacin dake harabar makaranta)
⏰ Lokaci: 9:00am
In Sha Allah da safe
💫 Hakika zuwanku yana da matuƙar muhimmanci wajen ƙarfafa zumunci da haɗin kai tsakanin iyalan makaranta.
🤲 Allah Ya bada ikon halarta tare da sanya albarka a cikin taron.
━━━━━━━━━━━━━━━━━━
✍️ Sanarwa Daga:
Yusuf Isah Abul Ihsan
━━━━━━━━━━━━━━━━━━
🕋🌙 “Maraba da Zuwa” 🌙🕋
Yusuf Isah Abul Ihsan

08/05/2026
Want your school to be the top-listed School/college in Bauchi?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Address


Kofar Dumi Bayan Ganuwa Unguwan Kandahar Bauchi
Bauchi
ABULIHSAN