27/02/2021
AWAJEN TARON MAULUDIN MAULANMU SHEKH IBRAHIM KAULAHA AN KARRMA MAULANA SHEKH TAHIR USMAN BAUCHI A MATSAYIN AMBASADAN AMBASADODIN ZAMAN LAFIYA NA DUNIYA.
• Wannan babban abin alkairi ne ga Duniyar Musulunci baki daya.
Gamayyar manyan kungiyoyi daga Kasaahen Bangladesh, Britain da kuma kasar India, karkashin jagorancin wakikin su Amb. Prof. Buhari Isah, sun karrama Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi (R.T.A) da lambobin girmanawa har kala 4 a fannoni mabambanta kamar haka:-
1- An bashi lamba na zabar sa a matsayin jakadan duka jakadun zaman lafiya na Duniya reshen Nahiyar Africa.
2- Da lambar girmamawa akan tsarkakuwa daga dukkanin nau'ukan cin hanci da rashawa da dangogin sa daga sashen dake kuka da cin hanci da rashawa na Majalisar dinkin Duniya.
3- Lambar girmama akan Zaman lafiya, da da'awa cikin masalaha da salama ba tare da tayar da hankali ko jawo husuma ba tsakanin Al'umma..
4- Lambar girmamawa ta yarda da alfarma cikin kebantattun jagororin Al'umma mafiya yawan mabiya a Duniya, daga majalisar dinkin Duniya.
Wannan dai ba shine karo na farko ba da Maulana Shehu ke karbar irin wannan kambu , domin ko a shekarar da ta gabata sai da wata gagrumar Gidauniya daga kasar India mai suna "Cholan book of world record" ta karramashi da kambun Duniya a fannin da yake a matsayin shine daya tilo.
Babu shakka wannan babban ci gaba ne, kuma abin murna ne da farin ciki ga dukkan al'umman Musulmi, kuma karamci ne daga ALLAH da bayin sa s**a tabbatar dashi.
ALLAH YA KARAWA SHEHU LAFIYA, HAKURI DA JURIYA ALFARMAR MANZON ALLAH (S.A.W).
Muhammad Usman Gashua.
ALHAMDULILLAH.