Masjid Khalid bn Al-Walid Baraya Quarters

Masjid Khalid  bn Al-Walid Baraya Quarters

Share

KHALID BIN WALID MOSQUE WUNTIN DADA BARAYA QUARTERS BAUCHI, BAUCHI STATE NIGERIA.

21/01/2024
10/10/2023

Assalamualaikum warahmatullahi wabarakatuhu

Muna Masu Farin Cikin Gayyatar Al'ummar Musulmi Zuwa wajen Muhadara, Wadda Malamimnu Imam Mukhtar Aliyu Muhammad zai Gabatar Yau Talata 10-10-2023 Amasallacin Khalid Bin Bin Walid baraya Quarters Wuntin Dada.

👉Maudui: Wajibcin Neman Halal.

👉 Lokaci: Bayan Sallan Magriba zuwa Ishai.

Allah Ya bada Ikon Halarta da Amfanuwa da Abunda za'a Saurara.

22/09/2023

HADISIN YAU (NA 16)

MANZON ALLAH SAW YACE: HAƘIƘA ƘABARI SHI NE MASAUKIN FARKO NA LAHIRA,
IDAN MUTUM YA TSIRA DAGA ƘABARI TOH DUK ABINDA ZAI BIYO BAYA MAI SAUƘI NE, IDAN KUWA BAI TSIRA DAGA ƘABARI BA, TOH ABINDA YAKE BAYAN SA YA FI TSANANI DAGA GARE SHI,
SANNAN SAI YACE : BAN TAƁA GANIN WANI ABU MAI BAN TSORO BA FACE ƘABARI YAFI SHI BAN TSORO.

FA'IDA.
ABUBUWAN DA SU KE JAWO AZABAR ƘABARI
1. SHIRKA
2. MUNAFINCI
3 RASHIN AMBATON ALLAH
4. ƘARYA
5. CIN KUƊIN RUWA
6 AIKATA ZINA
7. RASHIN KULAWA DA SALLA.
8. ƘAURACEWA KARATUN ALKUR'ANI.
9. JAN TUFAFI A ƘASA DA TAƘAMA
10. AZABTAR DA DABBOBI
11. RASHIN BIYAN BASHI.
12. AIKATA LIWAƊI
13. YI KURURUWA DA IHO A LAKOCIN MUTUWA.
14 SATAR KUƊIN BAITUL MALI.
15. ANNAMIMANCI
16. BAYYANA TSIRAICI.
17. RASHIN TSARKAKA DAGA FITSARI.
18. GULMA DA TSURKU.
19 KAULIN BILA AMALIN (FAƊA BA AIKI.)
20. KARYA AZUMI DA GANGAN.
DUBA littafin
اسباب عذاب القبر وأسباب النجاة منه. الشيخ ندا ابو احمد
YA ALLAH KA SA ƘABARIN MU YA ZAMA DAUSAYI DAGA DAUSAYIN GIDAN ALJANNAH, KA DA KA SA YA ZAMA RAMI DAGA RAMIN GIDAN WUTA.

Want your school to be the top-listed School/college in Bauchi?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Website

Address


Baraya Quarters Jos Road Bauchi
Bauchi