13/12/2024
WACECE NANA FATIMAH?
***************************
AN HAIFI SAYYIDAH FATIMAH (A.S) acikin garin Makkah, ranar 20 ga watan Jumaada akhir, ashekara ta biyar bayan Manzanci. Wato shekara 8 kafin hijra. (k**ar yadda yazo acikin "SIYARU A'ALAMIN-NUBALA'I.
Ta taso cikin kyakkyawar tarbiyyah wacce babu k**arta. Kasancewar Mahaifiyarta ita ce Nana Khadeejah bintu Khuwailid (rta) wacce ta zamto Mafificiya acikin Matayen Zamanin da, harma na yanzu.
Mahaifinta kuwa shine Shugaban dukkan Annabawa da Manzanni (saww). Kuma shine mafificin halittu ta wajen kyawun hali da dabi'u.
Nana Fatimah fara ce kyakkyawa mai kyawun diri. Tafi kowa daukar k**annin mahaifinta. Tayi k**a dashi wajen zamansa da tashinsa da tafiyarsa da maganarsa da murmushinsa.
Nana Fatimah ta taso da kaifin hankali da basira wacce ta zarce sauran tsararrakinta. Don babu tamkarta acikin Matayen zamaninta.
Ta kasance tana taimakon mahaifinta wajen isar da sakon Allah, Kuma duk da kasancewarta yarinya Qarama alokacin, takan nuna fushinta akan abinda kafirai suke yiwa mahaifinta.
Tana da kyawu da kwarjini irin na Mahaifinta. Ga kuma yawan ibadah, ga tsoron Allah. Wannan yasa ta haye saman dukkan matayen Halittu awajen daraja da Mukami.
An daura aurenta mai albarka acikin shekara ta 2 bayan hijira. Wato bayan yakin badar. Kuma Allah ne ya aiko Mala'ikah Jibreelu da sakon cewar "Yana umartar Manzonsa (saww) da cewar ya aurar da ita ga Sayyiduna Aliy bn Abi Talib (rta)".
Amma a ruwayar da tafi shahara, ance Sayyiduna Aliyu ne da kansa ya nemi aurenta awajen mahaifinta, kuma ya amince ya bashi ita, bayan wasu daga cikin manyan Sahabbansa sun nema bai basu ba.
Ta haifi 'ya'ya biyar ne arayuwarta :
- Alhasan.
- Alhusain.
- Al Muhsin.
- Zainab.
- Ummu Kulthum.
kuma ta rasu ne agarin Madinah Acikin shekara ta 11 bayan hijira, wato wata 6 bayan wafatin mahaifinta (saww).
Kuma an binne ta ne a Makabartar BAQEE'A, inda aka binne sauran 'Yan uwanta wadanda suke rigata rasuwa.
TA RAYU SHEKARU 28, ko kuma 27 aduniya. (k**ar yadda Imam At-Tabraaniy ya ruwaito acikin "ALKABEER" juzu'i na 22 shafi na 399 hadeeth mai lamba 997.
'Ya'yanta wadanda s**a rayu abayanta, Akwai Alhasan bn Aliy bn Abi Talib (rta) ya rayu lokaci mai tsawo har sai da ya zama Khalifa na biyar daga cikin Halifofi shiryayyu.
Ya hau kujerar Khalifanci bayan Mahaifinsa, kuma watanni shida yayi sannan ya sauka ya bar ma Sayyiduna Mu'awiyah (ra).
Shi kuwa Sayyiduna Al-Husain ya rayu har zuwa shekara ta Sittin da daya (61) bayan Hijira. Yayi shahada ne akusa da garin Karbala, aranar 10 ga Almuharram.
Ita kuma Ummu Kulthum lokacin da ta isa aure, Mahaifinta (Imam Aliyu) ya aurar da ita ga Sarkin Muminai Umar bn Al-Khattab (rta).
Lokacin da Sayyiduna Umar (ra) ya aureta, ya shigo Masallacin Manzon Allah (saww) yana murna, ya tarar da Sahabbai Muhajiruna suna zazzaune, yace musu "Kuyi mun murna. Domin hakika ni na auri Ummu Kulsum 'yar Aliyu bn Abi Talib. Kuma hakika ni naji Manzon Allah (saww) yana cewa :
"KOWACCE NASABA DA DALILI DA SURKUNTA YANA YANKEWA ARANAR ALQIYAMAH SAI DAI ABINDA YA ZAMA DAGA NASABATA DA DALILINA DA SURKUNTANA".
Ita kuma Zainab (rta) Sayyiduna Aliyu ya aurar da ita ne ga 'Dan yayansa mai suna Abdullahi bn Ja'afar bn Abi Talib (rta).
Allah shi Qara girma da aminci da daukaka ga Nana Fatima 'Yar Ma'aikin Allah. Matar da ta fifici dukkan matayen Halittu baki daya.
Wannan rubutun sakon gaisuwa ne daga MASOYA IMAM JUNAIDU ABUBAKAR BAUCHI zuwa ga dukkan Shurafa'u 'ya'yan Nana Fatimah, da dukkan masoyanta baki daya.
BUKATATA : Kuyi min shaida agaban Allah cewa ni Masoyinta ne.
13/11/2023
Ga masu bukatar jessey na kwallo ko jessy mai Hoton Shehu
Ku tuntube mu a wannan layin
08106837296
14/07/2021
Allah ya kara mana son Annabi Muhammadu(saw)
15/12/2017
SHEKHUL ISLAM ALHAJI IBRAHEEM NYASS
Haqiqa shehu ibraheem yayi qoqari sosai wajen gyara zuciyoyin Al'umma ,burin sa akullum shine jawo zuciya zuwa ga halarar ALLAH .Ba abinda yafi kiyayewa arayuwarsa k**ar Sallah .Yana fadi adiwani juz'ee na biyar
عليه صلاةالله ثم ثلامه
على صلوة الخمس دهري احافظ
Shehu yace tsira da amincin ALLAH su tabbata akan Ma'aiki .Da wannan salatinne nakeso ALLAH yasa muddin ina raye nadinga kiyaye salloli biyar
Don haka duk mai cewa yayi usuli ba ruwansa da sallah ,haqiqa ya bar hanyar ALLAH ya k**a wata hanya ce da zata kai shi jahannama wal iyazu billahi ,shehu yace ire iren mutanen nan munyi baran baran
انا بريئ منهم وهم بريئ مني
SHEHU kullum aikinsa shine yaga ya kora jama'a zuwaga halarar ALLAH ,Yana fadi adiwani juz'ee ta biyu.
والامة قصدي فيهم ان اسوقهم
الى حضرة البر الحيم الهنا
ka gadai wadannan AL'ummar babbar burina game dasu.Shine na korasu zuwaga halarar mahalicci ubangijinmu
SHEHU yayi yawo wajen jawo matasa zuwaga halarar tsarki halarar ALLAH .yana cewa adiwani juz'ee na takwas(sairul qalbu)
علوت البحار الزاخرات واننى
علوت القرى والمدن بله الجبال
اروم رضى الباري لنصرة دينه وابرز للجيل الجديد مثالا
SHEHU yace na tsallaka teku masu tashin kunfa teku mai yawan ruwa ,na tsallake Alqaryu ajirgin sama da birni da yawa da kuma manyan duwatsu .
Bakomai nake nema ba face yardar mahaliccina ,kuma infitar da sababbin jamaa 'a wato matasa dayawa misali misali
Mai zai faru sai SHEHU Ya bar wurarensa da iyalansa da jama'arsa .Yafara yanke daji daji wajen begen ma'aiki .shine yaqara fadi cikin sairul qalbu juz'ee na takwas kenan yake cewa
فغادرت اوطاني واهلي واسرتي
اجوب الفلا لم اشك قط كللا
SHEHU yayi matuqar qoqari sosai wajen sa wa zuciya son ma'aiki
Mezai faru? sai SHEHU wani lokaci ina kaulaha wani lokaci ina airport din kaulaha .wani lokaci ina france gidan fasiqai wadanda suke ragwaye ,duk yada addinin ALLAH yakaishi da kuma soyayyar MA'AIKI shine yake cewa adiwani juz'ee na takwas
بكولخ طورا او بيوف ومرة
بباريس دارالفسقين كسالا
Bayannan SHEHU Yace naje har BALJIK sannan kuma awannan rannan inata yawo agarin misra ina nemar jamal abdunnasir (shugabar qasar misra awannan lokaci)yafi hakane asairul qalbu inda yace
ببلجيك يوما ثم يوما تجولا
بقاهرة ابغي هناك جمالا
SHEHU Yaje ghana ,yaje yada addini da soyyar MA'AIKI shehu yace dare da yayi mutane na bacci amma zuciyata tana mai kafa hema da tuna kasar da MA'AIKI yake yafadi hakane asairul qalbu inda yace
بغانة والا حيا رقود ةولم يزل
فؤادى بترب الحاشمى مخيما
Sai ga shehu Amadina inda yace mana yashiga Aljanna tin bai mutuba ,shine mutane suke inkari akai sun mata gidan ANNABI da munbari dausayine daga dausayoyin Aljannna duk wanda ya shiga wajen yashiga ALJANNA inji ANNABI
SAI Yasa SHEHU Yace
وادخل جنات النعيم ولم امت
بيمني حبيبي ذاكم غاية النعم
Alhamdulillah muma shehu yazomana najeriya .yana cewa har ila yau adiwani sairul qalbu
بازري بكانوا من اكنني لكولخ
naje AZRE bauchi knan da kano da okene daga nan sai kaulaha .kuma yace mu yan africa munason ANNABI
وافريقيا لا ترتجى غير احمد
رسولا هدى النائى له والا اقاربا
Alhamdulillah wannan itace kadan daga cikin garuruwar da SHEHU yaje ALLAH qara kusan tashi Da SAYYADINA RASULALLAH
(SAW) Ameen summa Ameen
30/11/2017
FA AHLAN BI SHAHRIN QAD ATA BIL MUKHASSASI***
'
MUHAMMADI ABDILLAHI SIRRIL MUMAHHASI***
'
LAQAD JALA QABLAL KAUNI FIL GAIBI WAHDAHU***
'
BI IZZIN WA TASHREEFIN WA SIRRIN MUKHASSASI***
'
MA'ANA
"""""""""""""
LALE DA WATAN DA YA ZO DA. ABIN KEBANCEWA***
'
ANNABI MUHAMMADU BAWAN ALLAH SIRRI ABIN BOYEWA***
'
HAKIKA YA BUYAVACIKIN GAIBU SHI KADAI TUN KAFIN BAYYANAR HALITTA***
'
DA GIRMA DA DAUKAKA DA SIRRI ABIN KEBANCEWA***
'
INJI SHEIKHUL ISLAM ALHAJ IBRAHIM INYASS R.T.A
21/11/2017
KADAN DAGA CIKIN LITATTAFAI DA MAULANA
SHEHUL ISLAM R.T.A YA WALLAFA A CIKIN
RAYUWAR SA..
AL-SHEIKH IBRAHIM INYASS
1. Ðiwani
2. Ruhul Adab
3.Kashiful ilbasi
4. Rafa'ul malami
5. Tuhfatul Ahlulharina
6. Irshadus sarina
7. Tabsiratul Anami
8. Sabilus Salamiy..fee ibqa'il maqamiy...
9. Masarratul majami'i
10. Tabsiratul anami fi...
Jawazul ru'uyatul bari...
11. Tuhfatul Adafali
12. Tanbihul Azkiya...
13. Albayanu wattabayin
14. Assarimul Ahmadi
15. Kashiful gummma
16. Ruhul hubbi
17. Ðibal Amfasi
18. Nujumul huda
19. Alhujjatul ßaliga
20. Annurrarrabani fi
madahi sayyidi
Ahmadu tijjani [r.t.a]
21. Tuhfatu Adayibil Amfasi
22. Kibrifil Ahmad
23. Nawadurul Adayibil hirami
24. Rihilatul hijaziyya
25. Rihilatul kwanakiyya
26. Ittihafus sami'i
27. Risalatul tauba
28. Muqamatiddinil Salasa
29. Jawahirirrasa ili...
30. Ziyadatu jauharatu
31 Nurul ßasari
32 Iksiris sa'adafi
33. Taisiril wusuli...
34. Humurul halali fi
madahi sayyidir Rijal
35. Kibriful Ahmarfi madahi shafi'il yaumal
mahashar
36. Ausikul ura
37. Nurul haqqi
38. Siwatusshu jani
39. Shafa'ul Asqami
40. Manasiku Anlal
41. Kabril kasri
42. Sirril kqalbi
43. Sa'Aatuddaraini
44. Kanzul Arifina
45. Rafa'ul malami
46. Sulsa
47 Kashiful Irfam
48. Najamul huda
49. Irshadussarina
50. Sa'Adatul Anaam
ALLAH YA KARAWA SHEHU KUSANCHI
20/11/2017
SHEIKH SHARIFF SALEH AL-HUSSAINY Yana Cewa;
"Maganar Cewa: Duk Sabon Da 'Dan 'Darikar Tijjaniya Ya Aikata, Ba Zai Cutar Da Shi Da Komai Ba, Lallai Wannan Maganar Banza Ce, Sa'bo Yana Cutar Da Duk Wanda Ya Aikata Shi, Sai Dai Idan Ya Tuba, Tuba Ta Gaskiya...
Tijjanawa Ba Su Da Bambanci Da Sauran Musulmai, Idan S**a Aikata Sa'bo, Ko Kuma S**a Fada a Cikin Sabo, Hakan Zai Zutar Da Su Matukar Ba Su Tuba Ba...
Wannan Magana 'Karya Ce Aka Yi Ma Shehu Tijani (R.A), 'Karya Ce Aka Yi Ma 'Yan Tijjaniya, Koda Kuwa An Same Ta a Cikin Littattafan 'Darika, To Lallai Magana Ce Ta Banza Kuma Batacciya, An Dangata Ta Ne Da SHEHU Ba Tare Da Bincike Da Tabbatar Da Hakan Ba...".
ALLAH YA QARA KIYAYE MANA WANNAN 'DARIQAR TA MU DAGA DUKKAN WANI GAURAYE, DASSI, DA KARYA, KA TABBATAR DA DUGA-DUGANMU AKAN WANNAN 'DARIQA TA TIJJANIYA MAI CIKE DA DANDAZON ALKHAIRAI BIJAHI S.A.W. AMEEEEEEEEEEN
18/10/2017
MAI DA'DIN SUNAYE (SAWW) - 03.
**********************************
Ga ma'anonin wasu daga cikin sunayen Manzon Allah (saww) a takaice, k**ar yadda mukayi alkawari acikin darasin Zauren Fiqhu na wancan karon :
1. MUHAMMADUN :
********************
Wannan suna ne Maf'uli inji Maluman ilimin nahwu. Sun ce an tsago sunan ne daga kalmar "HAMDU" wato Yabo ko godiya.
An kirashi "MUHAMMADU" ne (Sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam) saboda shine Allah ya bama mafiya yawan halaye da dabi'u wadanda za'a yabeshi agode masa akansu.
Shi wannan suna shi yafi cikar Ma'anonin yabo fiye da "MAHMUD". Domin shi MAHMUD an tsagoshi ne daga thulathi mujarradi. Shi kuwa MUHAMMAD daga Mudha'afi ne na Mubalagah aka tsagoshi.
Ma'anar Muhammad (sallal lahu alaihi wa aalihi wa sallam) Shine Sha-Yabo, wanda ake yabonsa fiye da yadda ake yabon waninsa daga cikin jinsin Bil Adama.
Malamai s**a ce Watakil saboda wannan dalilin ne koda acikin Attaurah aka ambaceshi da wannan sunan saboda yawaitar dabi'u da halaye ababen yabo dake tare dashi, wadanda aka siffantashi dasu, dashi da addininsa da al'ummarsa (sallal Laahu alaihi wa aalihi wa sallam).
Saboda yawan wadannan siffofin yabon da Annabi Musa (alaihis salam) ya gani game da al'ummar wannan Annabin namu (saww) acikin Attaurar shi yasa yayi burin ya kasance 'daya daga cikinmu.
2. AHMADUN (SAWW)
**********************
Amma sunansa na biyu wato Ahmad, Malaman Nahwu sun ce sunan yana kan Ma'aunin "Af'alu" ne. Kuma sun ce sunan yana bayanin fifiko ne. Kuma shima an tsagoshi ne daga kalmar "HAMDU" wato godiya.
Sai dai Malamai sunyi sa'bani game da shin wannan sunan "FA'ILI" ne ko "MAF'ULI" ne?.
Maluman da s**a ce ai fa'ili ne, sun ce Ma'anarsa shine "Ai godiyarsa ga Allah tafi dukkan godiyar da waninsa yayi ma Allah din. Wato shine Mafi godiyar masu godiya ga Ubangijinsa.
Maluman da s**a ce "Maf'uli" ne, sun ce Ma'anarsa ita ce "Shine mafi chanchantar dukkan mutane da samun yabo da godiya. Wato anan Ma'anarsa ta kusan zuwa 'daya da ta "MUHAMMAD" kenan. Sai dai bambancinsu shine shi "Muhammad" shine Mamallakin Siffofi masu yawa da ake yabonsa dasu. Shi kuwa "AHMAD" shine wanda aka fi yabonsa fiye da kowa daga cikin halittu, ko kuma wanda ya zarce dukkan halittu wajen yabo da godiyar Ubangijinsa.
Shine mafi chanchantar samun yabo fiye da dukkan halittu baki daya. Don haka shima yake yabo da godiyar Ubangijinsa fiye da yadda waninsa yakeyi daga cikin halittu baki daya.
A takaice dai wadannan sunaye guda biyu dukkansu an tsagosu ne daga halayensa da dabi'unsa da khasa'isu nasa (sallal Laahu alaihi wa aalihi wa sallam).
Anan zamu tsaya sai a darasi na gaba. Da fatan Allah shi Qara mana Qarfin riko da Annabinmu (sallal Laahu alaihi wa aalihi wa sallam) don matsayinsa gareshi.
An gabatar da karatun a Zauren Fiqhu Whatsapp ranar (17/10/2017 27/01/1439).
Domin tambayoyi ko Qarin bayani zaku iya tuntubar Zauren Fiqhu akan wannan lambar 07064213990.
10/09/2017
AKWAI DARASIN 'DAUKA A CIKIN WANNAN LABARIN;
;
A Zamanin Da Ya Shud'e An Yi Wani Sarkin Wata Al-Qarya Yana Da Wasu Karnuka Guda Goma(10) Wanda Ya Basu Horo Na Halaka Bani Adam, Yana Amfani Da Wadannan Karnukan Wajen Azabtar Da Duk Wani Daga Cikin Talakawansa Ko Muqarrabansa Da S**a Yi Masa Laifi.
;
Wata Rana Wani Daga Cikin Talakawan Sarki Ya Bada Wata Shawara Wacce Sarki Bai Ji Dadinta Ba, Sai Sarkin Ya Bada Umarnin Akai Shi Can a Jefa Shi Ga Wadannnan Karnukan Su Gama Da Shi.
;
Sai Wannan Takakan Ya Ce:"Yalla6ai! Na Yi Maka Hidima Na Tsawon Shekaru 10, Shi Ne Zaka Saka Min Da Haka, Ranka Shi Dad'e???
;
Ina Rokon Alfarma Guda 'Daya Rak, Ina So Ka Bani Kwanaki Goma Nan Gaba Kafin Ka Zartar Min Wannan Hukuncin, Sarkin Ya Amince Da Hakan.
;
A Cikin Wadannan Kwanaki 10, Wannan Mutumin Sai Ya Je Ya Samu Mai Gadin Karnukan Ya Ce Masa:"Don ALLAH Ina Son Na Hutar Da Kai Na Tsawon Kwanaki 10 Domin Ina Son Ina Kulawa Da Wadannan Karnukan a 'Dan Wannan Lokacin". Mai Gadin Karnukan Daga Farko Kamar Zai Nuna Tirjiya, Amma Daga Bisani Ya Amince Masa.
;
Mutumin Nan Sai Ya Fara Kulawa Da Su Yana Musu Wanka, Yana Tsefe Musu Gashinsu, Yana Musu Wankin Hakora Da Dai Duk Wasu Abubuwan Jin Dadin Rayuwarsu Yana Aiwatar Musu.
;
Lokacin Da Kwanaki Goman S**a 'Kare, Sai Sarkin Nan Ya Bada Umarnin a Jefa Wannan Mutumin Ga Karnukan Nan Su Cinye Shi.
;
A Lokacin Da Aka Jefa Wannan Mutumin Ga Karnukan Nan, Sai Masu Kallo S**a Cika Da Mamaki Domin Sun Ga Karnukan Maimakon Su Fara Yagalgala Wannan Mutumin Sai S**a Ga Kawai Sunata Lasar 'Kafafuwan Shi Suna Nuna Alamar Girmamawa a Gare Shi.
;
Hakan Da Sarki Ya Gani Sai Ya Rikice Ya Ce:"Menene Ya Samu Karnukana Haka???"
:
Sai Wannan Mutumin Ya Ce:"Babu Abin Da Ya Same Su, Su Ba Su Zamto Masu BUTULCI Ga Alheri Ba, Na Yi Musu Hidima Na Kwanaki 10 Kacal, Amma Ba Su Manta Da Hakan Ba. Amma Yalla6oi Kai Kuma Na Yi Maka Hidima Har Na Tsawon Shekaru 10, Sai Ka Mance Abin Da Na Yi Maka Akan Wani Kuskure Da Na Yi 'Kwalli 'Daya".
;
A Dai Wannan Lokacin Ne Sarkin Ya Gane Kuskuren Shi, Take Yasa Aka Saki Wannan Mutumin Ya Tafi Abunsa.
;
*. TSOKACI; 'Yan'uwa Masu Hankali Da Tunani, Wannan Sako Ne Ga Dukkan Mutane Masu Mance ALHERI Da Ake Yi Musu, a Lokacin Da Wanda Yayi Musu Alherin Nan Ya Aikata Wani Kuskure. Ka Da Mu Zamto Masu 'Bata Tarihin Dake Cike Da Kyawawan Abubuwa Akan Wani Kuskure 'Kwalli 'Daya.
:
ALLAH KA TSARE MU DA SANYA RIGAR BUTULCI, YA SANYA MU CIKIN MASU YAWAITA SAKA ALHERI DA ALHERI AMEEEEEEEN.
03/09/2017
NADAMA;
:
SHEHU IBRAHIM NYASS(R.A) Ya Ce;
:
"NADAMA Ta Kasu Kashi Hudu(4);
:
*1. Nadamar Rana 'Daya
*2. Nadamar Shekara Guda
*3. Nadamar Rayuwa Gaba 'Daya
*4. Nadamar Har Abada(Bata Gyaruwa),
;
*1 - Matafiyin Da Ya Tashi Zai Yi Tafiya Sai Ya Ce Ba Zai Ci Abincin Safe Ba Sai Ya Isa Inda Zai Je, Da Ya Isa Sai Ya Je Ya Tarar Abinci Ya Qare a Inda Ya Sauka. A Wajen Abin Da Zai Fada Shi Ne Dana Sani Tun a Gida Na Ci Abinci(Wannan Ita Ce; Nadamar Rana 'Daya),
;
*2 - Sai Kuma Manomin Da Bai Yi Shuka Da Kyau Ba Lokacin Da Ruwa Ya Zuba... Bayan Amfanin Gona Ya Fito Sai Yaga Duk Na Sauran 'Yan'uwansa Manoma Yayi Kyau Banda Nashi Shi Kadai a Wannan Lokacin Zai Yi Nadama Ya Ce Da Ya Sani Ya Tsaya Yayi Shuka Da Kyau(Wannan Ita Ce Nadamar Shekara Guda).
;
*3 - Sai Kuma Mutumin Da Ya Auri Mata Marar Kirki Duk Lokacin Data Sa6a Masa Zai Yi Nadama Ya Ce Da Ya Sani Bai Aureta Ba(Wannan Ita Ce Nadamar Cikin Rayuwa Gaba 'Daya),
;
*4 - Sai Kuma Mutumin Da Zai Gamu Da ALLAH(S.W.T). Bashi Da Wani Kyakkyawan Aiki Da Zai Tsirar Da Shi Daga Azaba a Wannan Ranar Zai Yi Nadama Har Ya So Dama Ya Dawo Duniya Domin Ya Aikata Kyakkyawan Aiki(Wannan Shi Ne Nadamar Har Abada Wannan Ba Zai Ta6a Gyaruwa Ba)".
:
ALLAH YA KIYAYE MU DAGA WADANNAN NAU'O'I NA NADAMA(Musamman Na 'Karshen(Na; 4) DON ALBARKAR SHEHU IBRAHIM NYASS(R.T.A) AMEEEEEN.
Via By Sayyadi Othman Muhammad.