Jibwis Nhq Jos-Bauchi State

Jibwis Nhq Jos-Bauchi State

Share

Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Jibwis Nhq Jos-Bauchi State, Education, Bauchi.

03/04/2026

Walh Malam yasan kuskuren da ake yi a ƙasar nan, kuma ba ya tare da shi_Sheikh Sani Yahaya Jingir

03/04/2026

Daga cikin wa'azin Juma'a na Yau

08/09/2022

ALHAMDULILLAH YANXU YANXU SHEIKH MUHAMMAD SANI YAHYA JINGIR YA SAUKA A FILIN SAUKAN JIRAGE NA MALAM AMINU KANO DAKE JAHAR KANO

Alhamdulillah Asheikh Jingre Shugaban Majalisar Malamai na JIBWIS NHQ JOS na Kasa da shugaban kungiya na kasa Sheikh Nasir Abdulmuhyi Allah Ya sauwake su lafiya da Tawagar su a Aminu kano international airport bayan kammala Aikin Umrah da s**a gabatar a kasa mai tsarki.

Sun sami tarba ga majalisar kungiyar izala na jaha karkashin jagorancin Sheikh Dr.Sani Sharif umar Bichi da mataimakansa.

8/9/22
Al Maliki Tv

28/04/2022

TAHAJJUD, TARAWIHI: A GIDA KO A MASALLACI?

بسم الله الرحمان الرحيم

Da farko ba zan tsawaita wannan rubutu ba, saboda kusan gaba ɗaya abubuwan da zan rubuta, sanannu ne. Sannan wannan rubutu martani ne zuwa ga masu kawo nassosi wurin tabbatar da cewa sallan tahajjud a masallaci cikin jam'i yafi lada, da kuma masu karkatacciyar zuciya da suke nasabta sallan dare a gida zuwa wata ƙungiya, da ganan kuma su aibata ƙungiyar da magabata na ƙwarai.

Menene Ƙiyamul lail, Ƙiyamu Ramadan, Tarawih da Tahajjud? Kamar yanda kowa ya sani, ƘIYAMUL LAIL (sallan dare) sanannen abu ne a musulunci cikin watan Ramalana( ƙiyamu Ramadan) da wajensa. Sallan TARAWIHI kuma wani yanki ne daga cikin sallolin dare a watan Ramalana kaɗai, wanda ake gabatarwa a farkon dare k**ar yanda manzon Allah (SAW) da sahabbai s**a aikata. Sallan TAHAJJUD kuma malamai suna cewa sallah ce ta dare wacce ake gabatarwa cikin dare bayan tashi daga barci, a cikin Ramalana da wajensa. Kamar yanda Imamun Nawawy ya kawo cikin Riyadussaliheen 'التهجد: الصلاة في اليل وقراءة القرءان بعد النوم' ' Tahajjud: sallah a cikin dare da karatun Alqur'ani bayan tashi daga barci'. Ibnu Jaririɗ Ɗabary ma ya kawo kwatankwacin wannan bayani acikin tafsirinsa ƙarƙashin tafsirin aya ta 79 na cikin suratul Isra'a. Littattafan tafsirai da hadisai da dama sun kawo wannan bayni. A taƙaice, tarawihi da tahajjud suna da manyan banbanci guda biyu k**ar haka;
1. Tarawihi ya Kaɗaita da watan Ramalana ne kaɗai, tahajjud kuma cikin watan Ramalana da wajensa
2. Ana tarawihi ne a farkon dare bayan sallan Isha'i, ana tahajjud kuma cikin dare bayan tashi daga barci.

A taƙaice, dukkan hujjojin da masu fita sallan tahajjud suke kawowa, nassosi ne da suke magana akan sallan tarawihi. Hujjar su ta farko wacce ta fi ƙarfi ingantaccen hadisi ne, wanda shine marubucin Doctonnnan ya fara rubuta wa, hadisin Abu Zarr wanda Imamun Nasa'i (Sahihun Nasa'i: 1363) ya kawo da wanin sa, lokacin da Manzon Allah ya jagoranci sahabbai sallan dare a goman ƙarshe, tana magana ne akan tarawihi ba tahajjud. Menene dalilina?

1. Manzon Allah a farkon dare ya jagoranci sallan, duk da ya tsawaita. A rana na farko, ya jagorance su daga farkon dare zuwa ɗaya bisa ukun dare, rana na biyu kuma zuwa rabin dare, har sahabbai s**a ce masa da sun sallaci daren gaba ɗaya, sai yake ce musu إن الرجل إذا صلى مع الإمام حتى ينصرف حسب' له قيام ليلة' 'abun sani wanda ya tsaya tare da limaminsa, har limamin ya kammala, za'a rubuta masa ladan tsayuwan daren gaba ɗaya' rana na uku kuma ya sallaci daren gaba ɗaya tare da iyalansa da sahabbansa' Malamai suna kafa hujja da wannan hadisi ne wurin sallan tarawihi, wanda Imamu Albani (R) ma ya kawo a cikin littafinsa na 'Salatut Tarawih'

2. Bayan rasuwar Manzon Allah (SAW) mutane suna sallolin dare a gidajensu har lokacin Sayyiduna Umar (RA), ya haɗa mutane a ƙarƙashin limami guda, Ubayy Bn Ka'ab, a ƙarshe yake cewa ' والتي ينامون عنها أفضل من التي يقومون يريد آخر اليل وكان الناس يقومون أوله' ' madallah da wannan bid'ah kuma lokacin da suke barci yafi lokacin da suke tsayuwa, yana nufin ƙarshen dare yafi farkon dare, mutane kuma sun kasance suna tsayuwa a farkon dare' (Sahihul Bukhari: 1906)

Wannan dalili ne cewa, sallan tarawihi Sayyiduna Umar (RA) yake nufi, don a farkon dare suke gabatar da sallan kuma malamai sun kawo wannan hadisi dalili na sallan tarawihi. Shi yasa Imamul Bukhari ya kawo wannan hadisi da kuma hadisin Nana Aisha wanda manzon Allah (SAW) ya jagoranci sallar dare na kwana uku (Bukhari: 1908) ƙarƙashin 'كتاب التراويح' 'littafin tarawihi'

3. An tambayi Hasanul Basary (R) : shin bayan mun sallaci sallar Isha'i zamu koma gidajen mu muyi barci sannan mu dawo bayan haka? sai yaƙi yace 'لا، صلاة العشاء ثم القيام' ' a'a, sallan Isha'i sannan tsayuwan dare' yana nufin daga sallan Isha'i sai tarawihi, ba sake dawowa kuma.

4. Sannan in dai mutum yace dukka waɗannan hadisai suna magana ne akan sallan tahajjud, to a kawo mana hujjojin sallan tarawihi, in kuma kace tahajjud da tarawihi ma'anar su ɗaya, to mai yasa zaka fito sau biyu masallaci a dare ɗaya, ko kana da wani magabaci akan haka?

5. A ƙarshe, na ƙalubalan ci duk wanda yake ganin sallan tahajjud a masallaci yafi gida, ya kawo hujja inganciya da ta tabbatar da cewa Manzon Allah (SAW) ko ɗaya daga cikin sahabban sa daya gabatar da sallan tarawihi farkon dare cikin jam'i sannan ya sake fitowa karo na biyu don sallan tahajjud. Hatta sallar tarawihi ma bata kuɓuta daga saɓanin malamai cewa a gida ko masallaci ina yafi? wasu malamai sun tafi akan a gida yafi kuma suna da gamsassun hujjoji cikin su harda Imam Malik (R) b***e kuma sallan tahajjud.

Wannan taƙaitaccen rubutu ne kuma matshiya kafun ɗauraya in buƙatan hakan ya samu. Sannan muna ƙira zuwa ga malaman mu da suyi haƙuri su bar mu da duk wani mai surutu, muna daidai dasu, su ƙure mu kafun su koma kan malaman mu.

Hujjoji muke buƙata ba hauragiya da zage-zage ba, don tarbiyyar karatu malaman mu da shuwagabannin mu s**a koya mana. Insha Allah ba zamu kula mai s**a ko zagi ba, duk wanda yake da ja sai ya warware hujjojin mu sannan ya amsa tambayoyin da muka yi kafun mu saurare shi. Bissalam.

Abu Isma'il Almaliky
27th Ramadan, 1443AH
28th April, 2022

Photos from Jibwis Nhq Jos-Bauchi State's post 02/02/2021

SAKON TA'AZIYYA

Shugaban majalisar malamai na JIBWIS NHQ Jos, reshen Jihar Bauchi, Sheikh Salihu Sulaiman Ningi, a madadin daukacin alhlussunnah na Jihar Bauchi, yana mika sakon ta'aziyya zuwa daukacin kungiyar JIBWIS, reshen Jihar Pilato da iyalan marigayi Sheikh Ardo Bello Usman, aminin Sheikh Isma'il Idris, shugaban Jange dure na kasa, kuma shugaban majalisar malamai na karamar hukumar Riyom.

Allah ya jikansa, ya kyautata makoncinsa, ya kuma albarkaci abunda ya bari! Ameen.

06/10/2020

Copied.
INNA LILLAHI WA INA ILAIHI RAJI'UN!
Allah yayi rasuwa wa Alkali Abubakar Usman Wailo rasuwa, ubanmu kuma malamin mu, sanadiyar jinya da yayi fama da ita. Kafun rasuwarsa shine vice principal na SHIS Bakaro, kuma mataimakin shugaban majalisar malamai na JIBWIS Ganjuwa LGA, kana kuma alkali a kotun shari'ar musulunci na Jihar Bauchi.
Za'ayi jana'izar sa gobe talata in Allah ya kaimu 6/10/2020 da misalin karfe 10:00 na safe a babbar masallacin Juma'a na Gwallaga, Bauchi.
Muna rokon Allah ya jikansa, ya masa rahama, ya albarkaci abunda ya bari, yaba wa iyalansa hakurin rashi! Ameen.

06/05/2020

INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN!

Allah yayi rasuwa wa M***i As-Sheikh Ya'akub Muhammad Jama'are, mataimakin shugaban majalisar malamai na biyu na kungiyar JIBWIS NHQ Jos, reshen Jihar Bauchi.

Allah ya dauki rayuwarsa a garin Azare, karamar hukumar Katagum inda yake gabatar da tafsirin Al-Qur'ani mai girma.

Allah ya gafarta masa, ya masa rahama, yasa Al-jannna ne makomarsa da mu baki daya! Ameen.

17/04/2020

1441/2020 JIBWIS ANNUAL NATIONAL SEMINAR

Assalamu Alaikum!

Muna farancikin sanar da alumma cewa akwai seminar da JIBWIS NHQ JOS ta shirya gabatarwa gobe Asabat, 18/04/2020 da Misalin Karfe 10:00am (na Safe)

Za a gabatar ne a Kafafen Sadarwa Kamar haka:-

1. Izalah online Radio
2. Izala Online Tv (YouTube channel)
3. Facebook Live streaming

Ana iya k**a ta hanyoyi k**ar haka:-

1. Izalah Radio Android App Zaku iya sauke shi a wayoyin ku na android daga play store, ko kuma ta wannan hanyar dake kasa:

>>>https://goo.gl/78s686

2. Tunein Radio:
Zaku iya sauke shi a wayar Android, Blackberry, iphone, ipad, da kuma window phone.
Masu amfani da android zasu samu wannan ta daya daga cikin wadannan hanyoyin:

>>>https://goo.gl/t1EZmv

>>>http://goo.gl/zA8c8m

Sauran kuma kowa zai samu a app store din sa.

3. Web Player and Mobile Radio Player: kawai dannan link din dake kasa don sauraro ba tare da ka sauke kowane irin app ba:

>>>http://goo.gl/g65M6g

4. Hausa Radio Stations Android App:
Zaku iya sauke shi a android phones ta wannan link din:

>>>https://goo.gl/qHb8kp

5. Mouse Radio:
Za'a samu wannan a wannan link din:

>>>http://goo.gl/SJRyus

6. Online Radio Stations Directory:
Wanda zaku samu ta wannan link din:

>>>http://goo.gl/bVyY2r

https://goo.gl/78s686

Mun Samu Sanarwa daga:
Hon. Ahmad Muhd Ashir (National PRO)

Ta hanndun Alhaji Hamza M Sani (Org. Sec. JIBWIS INTERNET MEDIA COMMITTEE)

Want your school to be the top-listed School/college in Bauchi?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Category

Website

Address


Bauchi