05/03/2020
ABUBUWA GUDA SHIDA SUNA KARE MUTUM DAGA TALAUCIN DUNIYA DA LAHIRA.
Saka taka sadakar kaima ta hanyin yin turawa don wasu su karu
1. BIN IYAYE : Allah ya bamu labarin cewa Annabi Eisa (as) yace "Allah ya sanyani mai biyayya ne ga mahaifiyata, bai sanyani azzalumi, mai ta'bewa ba".
2. YAWAITA ADDU'A : Annabi Zakariyya (as) yace : "Kuma Ya Ubangiji ban zamanto mai tabewa ba game da rokonka".
3. RIKO DA ALQUR'ANI : Allah yace wa Manzonsa (saww) : "BAMU SAUKAR MAKA DA ALQUR'ANI DON KASHA WAHALA BA".
4. BIN SHIRIYA : Allah yace "Duk wanda yabi shiriyata ba zai bacecba, kuma ba zai tsiyata ba".
5. TSORON ALLAH : Allah yace "Wanda yaji tsoron Allah shi zai wa'azantu (da shiriyar Alqur'ani). Wanda ya tsiyata kuma shi zai nisanceta".
6. KIYAYE DOKOKIN ALLAH : "Ina yin muku gargadin wata wuta mai huruwa, babu mai shigarta sai wanda ya ta'be. Shine wanda ya karyata (ayoyin Allah) kuna ya juya baya. Amma Wanda ya kiyaye dokokin Allah shi zai nisanceta (ita wutar).
Tabbas duk wanda ya siffantu da wadannan siffofin zai samu tsira daga tsiyatuwar duniya da ta lahira. Allah zai kiyayeshi daga kowacce irin tawaya ko Qunci a rayuwar duniya da ta lahira. Allah shi taimakemu.