05/05/2025
RAYUWA KENAN
Har zuwa yanzu gani nake kamar Malamina kuma Masoyina Sheikh Dr Idris Abdul-Aziz Bauchi bai mutu ba saboda irin shakuwar da nayi da Malam
Allahu Akbar, Duniya ba gurin zama ba
Na sha zagi da tsinuwa a dalilin kariyar da nake bawa Malam Idris Abdulaziz, akwai da yawa daga cikin Malamai da muka samu sabani dasu saboda Malam Idris, na ga wadanda suke zagin Malam har a cikin 'yan uwana matasa Ahlussunnah, amma bayan da ya mutu duk sun fahimci gaskiya kuma sukayi nadama
Mutuwar Malam Idris tana daga cikin mutuwa mafi girma da aka min a rayuwana, har a lokacin da Malam yake jinyar ajali bai fita hayyacinsa ba, kuma bai manta dani ba, ya kan kirani a waya muyi magana ko ya tura min sako
Insha Allah ina dab da fara wallafa muku bayani akan sanadin haduwata da Malam Idris Abdul-Aziz Bauchi da alakar sirri da sarari da nayi dashi, da matsayin da ya bani a cikin al'amuransa, da darasin da na koya a tare da shi
Yaa Allah Ka jikan Limamin jaddada Tauhidi na Afirka🙏
Daga: Datti Assalafiy