Asalin Sakon Ahlul-bait

Asalin Sakon Ahlul-bait MUN BUDE WANNAN SHAFI NE DOMIN YADA KOYARWAR SAHIHIN ADDINI DA FIKIRA TA AHLUL-BAIT A.S.

Tasirin Juyin Juya Halin Imam Husaini (A.S) a Tarihin Musulunci. Juyin juya halin da Imam Husaini (A.S) ya yi a Karbala ...
22/01/2026

Tasirin Juyin Juya Halin Imam Husaini (A.S) a Tarihin Musulunci.

Juyin juya halin da Imam Husaini (A.S) ya yi a Karbala bai tsaya a kan lokaci ko wuri guda ba, sai dai ya zama juyin da ya girgiza tarihin Musulunci baki ɗaya har zuwa yau. Shahadar Imam Husaini (A.S) ta bar babban tasiri a zukatan Musulmi da al’ummar duniya gaba ɗaya.

1. Farkar da lamirin al’umma
Bayan shahadar Imam Husaini (A.S), mutane da dama sun fara fahimtar girman kuskuren da aka aikata na kashe jikan Manzon Allah (S.A.W). Wannan lamari ya tayar da lamirin al’umma, ya sa mutane s**a fara yin nadama da tuba, musamman mutanen Kufa da s**a gaza taimaka masa.

2. Karyewar martabar mulkin zalunci
Kodayake Yazidu ya samu nasara ta soja, amma ya sha kaye ta fuskar ɗabi’a da tarihi. Mulkinsa ya rasa martaba a idon mutane, domin an bayyana shi a matsayin mulkin zalunci da tauye addini. Wannan ya nuna cewa iko ba ya dawwama idan an gina shi bisa zalunci.

3. Haifar da tawayen adawa da zalunci
Shahadar Imam Husaini (A.S) ta haifar da tawayen adawa da zalunci da dama, kamar:

*Tawayen Tawwabun.
*Tawayen Mukhtar al-Thaqafi.

Waɗannan tawayen sun nuna cewa jinin Imam Husaini bai zube a banza ba, sai dai ya zama tushen gwagwarmayar adalci.

4. Kare Musulunci daga karkacewa
Idan Imam Husaini (A.S) ya amince da Yazidu, da hakan zai halatta fasadi da zalunci a matsayin Musulunci. Tsayuwarsa ta hana a karkatar da Musulunci, ta kuma bayyana bambanci tsakanin gaskiya da ƙarya.

5. Gado na sadaukarwa da shahada
Imam Husaini (A.S) ya kafa darasin cewa sadaukar da rai domin gaskiya ita ce mafi girman nasara. Wannan darasi ya zama gado ga al’ummar Musulmi, yana ƙarfafa su su tsaya tsayin daka a duk lokacin da aka fuskanci zalunci.

6. Tasiri har zuwa zamani na yau
Har yau, ana tunawa da Imam Husaini (A.S) a duk faɗin duniya, musamman a watan Muharram. Wannan tunawa ba kawai kuka ba ne, illa makaranta

~Auwalu Abdulaziz (Masana).

28/11/2025

Yan uwa masu albarka, ku yi Following wannan shafin na mu mai albarka domin samun Ingattaciyar koyarwar Annabi da iyalan sa masu daraja.

14/11/2025

Wannan shafi na mu mai albarka zai soma aiki daga gobe insha Allah, muna fatan zaku bibiye mu tare da yin sharing don amfanar sauran yan uwa.

جمعة مباركة!!An karɓe daga Manzon Allah (s.a.w.w) yace: Wadda ya mini salati dubu ranar juma'a bazai mutu ba har sai ya ...
18/11/2022

جمعة مباركة!!
An karɓe daga Manzon Allah (s.a.w.w) yace: Wadda ya mini salati dubu ranar juma'a bazai mutu ba har sai ya ga mazauninsu a aljanna.
اللهم صل على محمد وآل محمد وعجل فرجهم ياكريم.

Insha Allah zamu ke kawowa yan masu albarka darussa masu amfani daban-daban acikin wannan shafi namu mai albarka, kuma d...
17/11/2022

Insha Allah zamu ke kawowa yan masu albarka darussa masu amfani daban-daban acikin wannan shafi namu mai albarka, kuma duk karkashin koyarwar ahlulbait a.s.

Address

Matsango Azare
Azare

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Asalin Sakon Ahlul-bait posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The School

Send a message to Asalin Sakon Ahlul-bait:

Shortcuts

Share