Darul Qur'ani Was Sunnah Merawa Argungu

Darul Qur'ani Was Sunnah Merawa Argungu DARUL QUR'AN WAS SUNNAH MERAWA LUNGUN MARINAR KAURA ARGUNGU IS A MARKAZ ADDINI SUNNI SECTS

26/09/2026
26/09/2026

Shirin Goron Juma'a na DARUL QUR'AN WAS SUNNAH da yake zuwa muku sati sati Karo na (29) Mai Gabatarwa KAMILU KABIRU tare da Ibrahim Usman Giro Argungu

Muna godiya da goyon bayan da kuke bamu Allah ya saka muku da Alkhairi, Allah ya Albarkaci wannan institute tamu 5/July /2026

✍️Ibrahim Giro

LOKACIN TSORO (YAJUJU DA MAJUJU) – ADDU'ARMU TA YAU (40)Idan ka samu kanka cikin firgici, tsoro ko razana, akwai wata ga...
26/09/2026

LOKACIN TSORO (YAJUJU DA MAJUJU) – ADDU'ARMU TA YAU (40)

Idan ka samu kanka cikin firgici, tsoro ko razana, akwai wata gajeriyar addu'a wadda Annabi saw ya furta a irin wannan yanayi.

Ga ta:
لا إله إلا الله
"La ilaha illal Lah".

Annabi SAW ya furta wannan addu'a da kansa lokacin da ya shiga wajen matarsa, Zainab bintu Jahshin (RA) cikin firgici.

Yana cewa: "La ilaha illal Lah! Kaicon Larabawa daga wani sharri wanda ya matso kusa. A yau an buɗe wani rame daga katangar Yajuju da Majuju" [Bukhari: 3346; Muslim: 2880].

Kun ji yadda Annabi SAW ke firgita saboda wani sharri na nesa da yake ganin ya tunkaro al'ummarsa. Lalle Allah Ya yi gaskiya da ya siffanta Annabi saw da cewa: "abinda zai wahalar da ku yana damunsa" [Tauba: 128]. Ina ma shugabanninmu su zama haka.

Darasi: kada tsoro ya sa ka manta da Allah.

TUNA NI'IMAR ALLAH – KOYARWAR MUSULUNCIA yanzun nan da kuke karanta wannan rubutu, na fahimci Allah Ya yi muku wasu ni'i...
26/09/2026

TUNA NI'IMAR ALLAH – KOYARWAR MUSULUNCI

A yanzun nan da kuke karanta wannan rubutu, na fahimci Allah Ya yi muku wasu ni'imomi guda 4 ko fiye. (1) Allah Ya ba ku ni'imar idanu, makaho ba zai iya karanta wannan rubutu ba. (2) Allah Ya ba ku ni'imar ilimi, jahili bai iya karatu ba. (3) Allah Ya ba ku ni'imar hankali, mahaukaci ba zai fahimci wannan rubutu ba. (4) Allah Ya yi muku ni'imar Musulunci, shi ya sa ba ku wuce wannan shafi ba. (5) Allah Ya yi muku ni'imar mallakar wayar hannu, marar waya ba zai ga rubutun ba. (6) Allah Ya ba ku ni'imar rayuwa, na ƙabari bai san anyi wannan rubutu ba.

Kun ga waɗannan ni'imomi da aka ambata? Misalai ne kawai aka bayar. Amma inda za mu ƙirga ɗimbin ni'imomin Allah da Ya saukar muna ta ƙasa da sama, to ba za mu iya ƙididdige su ba saboda yawan su [Ibrahim: 34]. Kun gane mu nan, kewaye muke ta ko ina da ni'imomin Allah, waɗanda s**a shafi addininmu da rayuwarmu ta duniya. Wata ni'ima kai kanka Allah Ya yi wa, wata ni'ima ƙabilarka Allah Ya yi wa, wata ni'ima na kusa da kai Allah Ya yi wa (iyaye, ko ɗiya, ko ƴan'uwa, ko miji, ko mata, ko abokai); kuma duk ni'imominka ne, domin dole sai amfaninsu ya shafe ka.

Allah Yana son mu riƙa tuna waɗannan ni'imomi duka, kuma mu riƙa godiya gare shi. Allah Ya cewa Annabi Isa: "Ya kai Isa ɗan Maryamu, ka tuna ni'imata da Na yi maka kai da mahaifiyarka." [Ma'ida: 110]. Ya ce wa Bani Isra'ila: "Ya ku ƴaƴan Isra'ila, ku tuna ni'imata da na yi muku" [Baƙara: 40, 47 & 122]. Ya ce wa masu imani: "Ya ku waɗanda s**a yi imani, ku tuna ni'imar Allah da Ya yi muku" [Ma'ida: 11, Ali-Imran: 103]. Ya kuma cewa mutanen duniya duka: "Ya ku mutane, ku tuna ni'imar Allah a gare ku. Yanzu akwai wani mahalicci ban da Allah wanda zai azurta ku daga sama da ƙasa?" [Faɗir: 3].

26/09/2026

Karatun Hadisin da ke gudana duk sati
Na "DARUL QUR'ANI WAS SUNNAH"
Mai gabatarwa Mal. Kwaido
Narba 25/09/2026M
D/Alhamis 13/04/1448H
Darasi na 295
Ayi kallo lafiya Allah ya bamu ikon aiki
Ya saka ma Malam da alkhairi
PART B

ƘUL HUWAL LAHU – ILMOMIN ALƘUR'ANI (68)Suratul IKHLAS ita ce sura ta 112 a jerin surorin Alƙur'ani. Ayoyinta 4 ne. Tana ...
26/09/2026

ƘUL HUWAL LAHU – ILMOMIN ALƘUR'ANI (68)

Suratul IKHLAS ita ce sura ta 112 a jerin surorin Alƙur'ani. Ayoyinta 4 ne.

Tana da sunaye:
(1) Asās,
(2) Ƙul huwal lahu,
(3) Attauhid,
(4) Annajati,
(5) Almu'awwizati,
(6) Asswamad,
(7) Almani'a,
(8) Albara'a.

Manzon Allah SAW ya ce: duk wanda ya karanta "ƙul huwal lahu ahad", haƙiƙa ya karanta kashi ɗaya cikin kashi 3 na Alƙur'ani. Ma'ana, duk wanda ya karanta ta sau 3 ya karanta Alƙur'ani duka.

25/09/2026

Karatun Hadisin da ke gudana duk sati
Na "DARUL QUR'ANI WAS SUNNAH"
Mai gabatarwa Mal. Kwaido
Narba 25/09/2026M
D/Alhamis 13/04/1448H
Darasi na 295
Ayi kallo lafiya Allah ya bamu ikon aiki
Ya saka ma Malam da alkhairi
PART A

YANKA DON ALLAH – HADISI NA 7; ARBA'UNA HADISI (81)Halittawa, azurtawa, mallakar mulki da tsara al'amura, duka "ayyuka n...
25/09/2026

YANKA DON ALLAH – HADISI NA 7; ARBA'UNA HADISI (81)

Halittawa, azurtawa, mallakar mulki da tsara al'amura, duka "ayyuka ne da Allah Yake yi". Idan bawa ya yarda Allah kaɗai ke aikata su, to ya yi nasiha ga Allah.

To akwai kuma ayyuka waɗanda bayi kaɗai ke aikata su, ban da Allah. Misali: sallah, azumi, yanka, addu'a da sauransu.

Yana daga cikin nasiha ga Allah, bawa ya aikata waɗannan ayyuka domin Allah Shi kaɗai, kuma zuwa ga Allah Shi kaɗai.

Yanka don Allah shi kaɗai, sallah don Allah Shi kaɗai, addu'a zuwa ga Allah Shi kaɗai. Duk wanda ya yi haka, to ya yi nasiha ga Allah SWT.

Allah Ya fi kowa sani.

ZUWAN ALƘIYAMA – ALAMOMIN TASHIN ALƘIYAMA (1)Lallai Alƙiyama za ta zo, ko shakka babu. Yin imani da zuwanta yana daga ci...
25/09/2026

ZUWAN ALƘIYAMA – ALAMOMIN TASHIN ALƘIYAMA (1)

Lallai Alƙiyama za ta zo, ko shakka babu. Yin imani da zuwanta yana daga cikin shika-shikan Imani, kuma Imanin mutum bai cika sai ya yi imani da ranar Alƙiyama [Baƙara: 177; Nisa'i: 162].

Ga wasu ayoyi da Allah Ya tabbatar muna Alƙiyama za ta zo:

–Allah ne Yake fara halitta sannan Ya dawo da ita (bayan mutuwa), sannan kuma gare Shi za a komar da ku [Rum: 11].
–Kuma lalle Alƙiyama tabbas mai zuwa ce [Hijr: 85].
–Lalle Alƙiyama za ta zo [Ɗa-Ha: 15].
–Lalle Alƙiyama tabbas za ta zo babu kokwanto a cikinta, sai dai kuma yawancin mutane ba sa yin imani [Ghafir: 59].
–to lalle lokacin (haɗuwa da) Allah tabbas mai zuwa ne [Ankabut: 5].

–Allah, babu wani abin bautawa da gaskiya sai Shi. Lalle zai tattara ku a ranar Alƙiyama, wadda babu kokwanto a cikinsa [Nisa'i: 87].
–Lalle abin da ake yi muku alƙawarinsa tabbas gaskiya ne. Kuma lalle sakamako tabbas mai afkuwa ne [Zariyat: 5-6].
–Lalle azabar UbangijinKa tabbas mai aukuwa ce. Ba wani mai ingije ta [Ɗur: 7-8].

–Suna kuma tambayar ka cewa: "Yanzu (batun azabar nan) gaskiya ne kuwa?" Ka ce: "I mana, na ko rantse da Allah lalle shi gaskiya ne; ba kuma za ku kuɓuce ba." [Yunus: 53].
–Kuma waɗanda s**a kafirta s**a ce: "Ranar Alƙiyama ba za ta zo muna ba". Ka ce: "a'a, na rantse da Ubangijina, tabbas za ta zo muku [Saba'i: 3].
–Lalle alƙawarin Allah gaskiya ne, to kada rayuwar duniya ta ruɗe ku [Luƙman: 33].

Allah Ya fi kowa sani.

Address

Merawa
Argungu

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Darul Qur'ani Was Sunnah Merawa Argungu posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share