Madarasatu Ibn Hibban Litahfizil Qur'aneel Kareem Alkaleri.

Madarasatu Ibn Hibban Litahfizil Qur'aneel Kareem Alkaleri. ILIMI HASKEN RAYUWA

MADARASATU IBN HIBBAN LITAHFIZIL QUR'ANIL KARIMAdireshi: Central Primary School, AlkaleriSANARWA GA IYAYE DA DALIBAIAmad...
13/05/2025

MADARASATU IBN HIBBAN LITAHFIZIL QUR'ANIL KARIM
Adireshi: Central Primary School, Alkaleri

SANARWA GA IYAYE DA DALIBAI

Amadadin Hukumar Wannan makaranta, Mai suna da adreshi a sama Tana sanar da iyaye da ɗalibai cewar an janye yajin aikin da Kungiyar Malaman Islamiyya ta karamar hukumar Alkaleri ta shiga tun daga ranar 10/05/2025 zuwa yau Talata 13/05/2025.

Saboda haka, za a ci gaba da gudanar da darussa kamar yadda aka saba daga gobe Laraba, 14/05/2025, in Allah Ya kai mu.

Muna godiya da hakuri da fahimta daga iyaye da ɗalibai a lokacin tsaikon da ya gabata. Allah Ya saka da alheri, Ya kuma kara mana nisan kwana cikin zaman lafiya da cigaba.

—Hukumar Makaranta

30/04/2025
مد ر  سة  ابن حبا  لتحفيظ   القرآن  الكريمMADARSATU IBN HIBBAN LITAHFIZIL QUR'ANIL KARIM.Amadadin Hukumar Wannan  Makara...
13/01/2024

مد ر سة ابن حبا لتحفيظ القرآن الكريم
MADARSATU IBN HIBBAN LITAHFIZIL QUR'ANIL KARIM.

Amadadin Hukumar Wannan Makaranta Mai Suna Asama Tanayin Amfani Da Wannan Kafa Ta Facebook, Wajen Mika Sakon Godiyarta Wa Honourable Bappah Tata Abisa Taimakonta Da Taburmai, Guda 10 dayayi, Domin Dalibai Sunayin Sallah Akayi, Wannan Sako Yazoshi Tahannun Amininshi wanda Akafi sani da Comr Tata Alkaleri .

Amadanin Dukkan Malamai Da DalibaI Na Wannan Makarata Mai Albarka, Sunayiwa Wannan Bawon Allah Fatan Alkhairi , Allah Taala Yabiya Mishi Bukatunsa Na Alkhairi.

Ameen Summa Ameen
Mungode
👃👃

HUKUMAR MAKARANTA.
13/01/2023.

Abubuwan da zasu taimakawa Dalibi Wajen Saurin haddace Qurani 1. Yin Alwala kafin fara hadda wato duk lokacin da zai had...
09/01/2024

Abubuwan da zasu taimakawa Dalibi Wajen Saurin haddace Qurani

1. Yin Alwala kafin fara hadda wato duk lokacin da zai hadda yakasance cikin tsarki da kuma alwala

2. ⁠Yin hadda bayan Sallan Asuba ko daga 3:30 na dare zuwa 9 na Safe

3. ⁠yin Hadda Cikin Tsafta da kuma Fiskantan Alqibla tare da nisantan Hayaniyan mutane

4. Yin Hadda bayan Malami Ya karanta maka Ayoyin wato Malami ya qarawa dalibin Haddan sannan kuma yakamata dalibin ya samu Sautin wani Qwararre ya saurari Haddan sosai kaman Minshawi ko Ayyubi ko Khalil Husari ko Malamanmu na Nigeria da makamantansu

5. yin Hadda cikin rige rige ko ince Competition tsakanin mai hadda da Abokin haddanshi

6. yin Hadda bayan kaucewa aikata dukkan Alfasha da kuma kyautata niyya wato yin hadda tsakani da Allah badon neman wani abun duniya ba

7. yakamata kayi addua duk lokacin da kayi Sallah don neman taimakon Allah ya yassare maka Haddan Qurani

8. Qasqantadda kai da girmama Malamai ko ladabi zai qara maka budi da taimako wajen Cimma nasara a neman iliminka musamman Quran

9. Son samu dalibi yasamu wuri mai kyau da kuma yaci abu mai dadi amma kar ya qoshi sosai kuma kar yayi hadda cikin yunwa ya zama tsaka tsaki, hakan ma zai taimaka wajen haddan Qurani.

Allah yabamu ilimi mai amfani mainalbarka.

Masha Allah 🙏مد رسة  ابن حبان لتحفيظ. القرآن الكريم ADDRESS: CENTERAL PRIMARY SCHOOL ALKALERI, BAUCHI STATE.TEL No: 0706...
26/12/2023

Masha Allah 🙏

مد رسة ابن حبان لتحفيظ. القرآن الكريم


ADDRESS: CENTERAL PRIMARY SCHOOL ALKALERI, BAUCHI STATE.

TEL No: 07061016461,07035494740.

MOTTO: النور القرآن

30/03/2023

MASHA ALLAH 🙏

22/11/2022

Saukan Al-qur'ani a kwana 3 cikin sauqi a wannan lokacin
Bayan sallan asuba izfi 4
Bayan sallan azahar izfi 4
Bayan sallan laasar izfi 4
Bayan sallan magrib izfi 4
Bayan sallan isha'i izfi 4
Idan ka haďa zai baka izfi 20 kullum 20×3=60

Saukan Al-qur'ani a kwana 6 cikin sauqi a wannan lokacin
Bayan sallan asuba izfi 2
Bayan sallan azahar izfi 2
Bayan sallan laasar izfi 2
Bayan sallan magrib izfi 2
Bayan sallan isha'i izfi 2
Idan ka haďa zai baka izfi 10 kullum 10×6=60

Saukan Al-qur'ani a kwana 12 cikin sauqi a wannan lokacin
Bayan sallan asuba izfi 1
Bayan sallan azahar izfi 1
Bayan sallan laasar izfi 1
Bayan sallan magrib izfi 1
Bayan sallan isha'i izfi 1
Idan ka haďa zai baka izfi 5 kullum 5×12=60
..وَعَسَى أَنْ تَكْرَهُواْ شَيْئًا وَهُوَ خَيْرٌ لَّكُمْ...

Allah ya bamu ikon aikata hakan
copied.

Address

Unguwar Maimadiri Alkaleri
Alkaleri

Telephone

+2347061016461

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Madarasatu Ibn Hibban Litahfizil Qur'aneel Kareem Alkaleri. posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The School

Send a message to Madarasatu Ibn Hibban Litahfizil Qur'aneel Kareem Alkaleri.:

Shortcuts

Share

Category