01/02/2026
*_AYYUKAN ‘YAN ALJANNA_* 001.
_*TSARKAKE TAUHIDI DA IKHLASI GA ALLAH*_
_‘Yan Aljanna su ne wadanda s**a tsarkake bautarsu ga Allah Shi kaɗai, s**a kebance niyyarsu gare Shi, ba su haɗa Allah da kowa ba, kuma ba sa yin aiki sai domin yardar Allah._
_Ya ku bayin Allah! Ku ji tsoron Allah matuƙar jin tsoronsa. Ku sani cewa babban aikin da ya fi dukkan ayyuka daraja, wanda babu ‘yan Aljanna sai da shi, shi ne *Tauhidi tare da Ikhlasi.*_
Allah madaukakin Sarki yana cewa
> وَمَا أُمِرُوا إِلَّا لِيَعْبُدُوا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ
[البينة: 5]
*_(Ba a umarce su da komai ba face su bauta wa Allah suna tsarkake masa addini)._*
_‘Yan Aljanna sun fahimci cewa duk wani aiki *—sallah, azumi, sadaka, jihadi, karatun Alƙur’ani* idan babu ikhlasi, aikin ya rushe._
Allah Ta’ala yana cewa:
> قُلْ إِنِّي أُمِرْتُ أَنْ أَعْبُدَ اللَّهَ مُخْلِصًا لَّهُ الدِّينَ
[الزمر:
_*(Ka ce: Lallai an umurce ni ne da in bauta wa Allah ina tsarkake masa addini).*_
_Yaku bayin Allah! Annabi ﷺ ya bayyana mana tushen karɓuwar aiki inda ya ce_
> “Lallai ayyuka suna tare da niyya, kuma kowane mutum yana da abin da ya yi niyya.”
(Bukhari da Muslim s**a ruwaito shi).
_‘Yan Aljanna basa neman yabo, basa neman suna, basa yin aiki don a ce musu *waliyyai ko malamai ko masu ibada.* Allah suke nema, Allah suke so, Allah suke tsoro._
_Allah Madaukakin Sarki yana cewa a cikin Hadisi Qudsi_
> Ni ne mafi wadatar abokan tarayya. Duk wanda ya yi aiki ya haɗa Ni da wani a cikinsa, Na bar shi da wanda ya haɗa Ni da shi.”
(Muslim ya ruwaito shi).
_Yaku bayin Allah! Ku sani cewa shirka da riya su ne mafi hatsarin abin da ke rushe aiki. Saboda haka ‘yan Aljanna suna tsananin tsoron aikata aiki ba don Allah ba._
Daga Mahmud bn Labid (RA), Annabi ﷺ ya ce:
> “Abin da nake fi tsoro a kanku shi ne shirka ƙanana.” Sahabbai s**a ce: “Menene shirka ƙanana ?” Sai ya ce: “Riya.”
(Ahmad ya ruwaito shi).
_‘Yan Aljanna suna yawaita duba zuciyarsu kafin aiki, a yayin aiki, da bayan aiki. Suna roƙon Allah Ya tsarkake niyyarsu, domin sun san Allah ba ya karɓar aiki sai wanda aka yi don Shi kaɗai._
Allah Madaukakin Sarki yana cewa:
> فَمَن كَانَ يَرْجُو لِقَاءَ رَبِّهِ فَلْيَعْمَلْ عَمَلًا صَالِحًا وَلَا يُشْرِكْ بِعِبَادَةِ رَبِّهِ أَحَدًا
[الكهف: 110]
*_(Duk wanda yake fatan haɗuwa da Ubangijinsa, to ya aikata aiki nagari, kuma kada ya haɗa kowa da bautar Ubangijinsa)._*
_Ya kai bawan Allah! Ka tambayi kanka...._
_Shin sallah da nake yi don Allah nake yi ?_
_Shin sadakar da nake bayarwa don Allah nake yi ?_
_Shin abin da nake aikawa mutane don gani ne, ko don Allah ne ?_
*Da Tauhidi da Ikhlasi kaɗai ake shiga Aljanna.*
*الله تعالى أعلم*
You can join our WhatsApp chat for more lectures and don't forget to follow and like too
https://chat.whatsapp.com/GPhYoq8X6GzIvWH6NBcnLw