03/02/2025
SHUGABAN IZALA NA DUNIYA YAYI KIRA KUMA MUN AMSA
AlhamdulilLah na cika da farin ciki sosai bayan sanarwan da na gani daga Shugaban Kungiyar Izala na duniya Sheikh Dr Abdullahi Bala Lau (H) akan mas'alar gidan Marigayi Sheikh Albaniy Zaria
Malam yace a dakata da fitar da abubuwa, yayi alkawarin zai nada kwamiti cikin sauri da zasu binciki lamarin, kuma ya bawa dukkan bangarorin hakuri a kai zuciya nesa, muna tabbatar wa Shugaba Bala Lau cewa mun amsa kiranka, kuma zamu dakatar da fitar da bidiyo Insha Allah
Da farko na ji dadi matuka da wannan mataki da Shugaba Bala Lau ya dauka, mun yaba masa sosai da ya shigo cikin lamarin wanda tun farko abinda muke ta kira kenan cewa manyan Malamai su shiga suyi bincike a dauki matakin da ya dace
A shekarar 2015 aka fara zaman sulhu akan rikicin Darul Hadith da iyalan Malam Albaniy, anyi zama tare da Sheikh Professor Isa Ali Pantami (H), Sheikh Bello Yabo Sokoto, Sheikh Sa'idu Maikwano da Sheikh Abdu Gwani Yobe, tare da daliban Malam Albaniy Zaria da suke jagorancin Darul Hadith
An kusa gama samun mafita akan zaman sai daya daga cikin daliban Malam Albaniy ya tashi tsaye ya warware duk abinda aka cimma matsaya a kai, takardan da aka rubuta sharadin sulhun ya yagata, har ma ya yiwa su Malam Isah Ali Pantami rashin kunya, s**a ki yadda a samu mafita, ku tambayi Malaman da na ambata zasu tabbatar muku da faruwar haka
Wannan fa bayan shekaru 10 kenan da faruwar haka, sannna a watannin baya kadan lokacin da muka fara fito da mas'alar a media, Sheikh Al-Qasim Hotoro ya kira taron zaman sulhu da masu jagorancin Darul Hadith da wasu daga cikin manyan Daliban Malam Albaniy da aka kora daga Darul Hadith da kuma 'ya'yan Malam, sun je gidansa a Kano akayi zama, amma a karshe daliban Malam din s**a bijire ma matsayar da aka dauka don a samu adalci
Don haka jama'a ku fahimta, ba wai yanzu ne mas'alar ta faru ba, Malamai sun yi ta kokari domin a samu mafita amma maciya amanar nan suna ta kaucewa, ba yadda aka iya sama da a fito da abin