07/10/2025
*MISALIN WANNAN DUNIYAR...*
-
"Misalin wannan duniyar kamar misalin ɗan tafiya ne acikinta, wanda yaga wata inuwar bishiya acikinta bayan yasha doguwar tafiya saiya tsaya ajikinta ya ɗan huta a inuwar tata"
-
"Manzon Allah ﷺ, yace: misalin duniya akan lahira bai kasance face kamar misalin ɗayanku ya sanya yatsansa (hanunsa) ne acikin kogi, to yayi dubi yagani, shin menene zai dawo dashi"
(Sunan Ibn Majah: 4108)
-
"Kada ka ɗauki son duniya ka ɗorawa kanka, ta yadda bazaka hangi lahirarka ba b***e kayi mata wani tanadin alkhairi, domin lallai wannan duniyar gidan ruɗu ce da ƙyale-ƙyale"
-
Allah Yasa mudace 💯 ❤️ 🤝 💯🙏 👍