22/07/2021
SANARWA!
Mun chanza wa wannan shafi suna zuwa Daidaitacciyar Hausa. Munyi hakan ne sabo da mu bada gudunmawa wajen kyautata Harshen Hausa a magance da kuma rubuce. Mun lura al'ummar Hausawa da ma wadanda ke jin Hausa ba su fiye mai da hankali wajen kyautata rubutun Hausa ba musanman a kafafen sada zumunta. Muna fata gudunmawar da zamu bada a wannan shafin zai taimaka wajen magance kura-kuren rubutun Hausa da fiye da kaso 80 (80%) na mutane ke yi wajen rubutun Hausa.
Kofa a bude take wajen bada gudunmawa ta ko wace fuska akan wannan kuduri na inganta Hausa ta hanyar wannan shfi daga mabiya da manazarta a ko'ina suke a fadin duniya.
Me ake nufi da Daidaitacciyar Hausa?
Daidatacciyar Hausa ita ce Hausar da masana Harshen Hausa s**a yarda a yi amfani da ita wajen rubuta Hausa. Da irinta ake amfani a dukkan tsangayu da sassan nazarin Harshen Hausa a manya da ƙananan makarantu k**a daga firamare har zuwa jami’a a faɗin duniya. Ita ce Hausar da marubuta littattafai da mawallafa da kafafen yaɗa labaru na duniya ke amfani da ita. Misalin irin waɗannan kafafen yaɗa labaru akwai BBC Hausa, VOA Hausa, DW Hausa, CRI Hausa, FRI Hausa da dai sauransu. Rumbun Ilimi ma da ka ke karatu a cikinsa, da ita aka yi amfani.
Kenan, kai tsaye muna iya cewa, daidaitaciyyar Hausa, wacce wasu marubutan ke kira karɓaɓɓiyar Hausa, ita ce Hausar da masana Harshen Hausa tun dauri s**a haɗu a kan cewa, da ita za a yi amfani wajen yin rubutun Hausa domin samun daidaito.
Wannan kuma saboda akwai kare-karen Hausa da dama, da s**a haɗa da Kananci, Katsinanci, Zazzaganci, Dauranci, Sakkwatanci, Aranci, da sauransu. Idan aka ce kowa zai yi rubutu da nasa karin k**ar yadda ya ke magana da shi, to abin zai zama babu tsari babu kan-gado, wanda kuma hakan zai hana tsayuwa a kan ƙa’ida bai daya.
Asalin Daidaitacciyar Hausa
Zarruƙ, Kafin Hausa da Alhassan (2010), sun ce, “Daidaitacciyar Hausa an gina ta ne akan Kananci”. Sun kafa hujja da zamowar garin Kano a matsayin matattarar jama’a a Ƙasar Hausa da kuma zaman Ɗanhausa (Hans Visch) a garin, wanda shi ne ya fara kafa ƙa’idojin rubutun Hausa.
Ɗauraya
Daidaitacciyar Hausa ita ce rubutacciyar Hausa, wacce ke da ƙa’idojin rubutu da ake amfani da ita a faɗin duniya wajen rubuta Harshen Hausa. Wannan kuma ya bayar da gudunmawa mai gwaɓi wajen samar da daidaitacciyar hanyar rubuta Hausa guda ɗaya rak. An yi amfani da Kananci daga cikin kare-karen Harshen Hausa da ake da su, kasantuwar garin Kano shi ne matattarar jama’a a Ƙasar Hausa da kuma ƙarin zaman Ɗanhausa, wanda shi ya fara rubuta ƙa’idojin rubutun Hausa a garin na Kano.