Kalimullah's inspirational quotes

Kalimullah's inspirational quotes

Share

Your character is your actual address.

22/12/2025

With all the problems in life,
We face a lot of challenges that lie,
Inside our lives, looking for a way,
To fight the battle that blocks our way.

But still we rise, we face the test,
And find the strength to do our best,
For every challenge, a lesson's learned,
And every battle, a victory earned."

Sit down and think of the situations,
Think of ways to solve it, don't shun,
Know that every problem has a path,
Of rectifying the challenges that patch

Time flows like a river, swift and serene,
Each moment a droplet, clear and unseen.
It whispers of ages, both future and past,
A treasure we hold, but never can grasp.

In morning’s soft light, the hours awake,
A canvas unpainted, a path to partake.
Each second a seed, with care we must sow,
For the fruits of our labor, in time, will show.

Waste not on worry, nor idle despair,
But dance in the present, with mindful care.
For time, like a tide, ebbs and it flows,
And wisdom is knowing when to let go.

Cherish the moments, both large and small,
For time is a gift, the greatest of all.
Spend it with love, with purpose and grace,
And in its reflection, your life you’ll trace.

So let the clock tick, and let the sun rise,
For time spent wisely, is life’s greatest prize.
In the hands of the wise, time is a friend,
A journey well traveled, from beginning to end.

Remain blessed

Signed: Motivator & Author Kalimullah Ahmad Hinna (Hasken Yamaltu) The 1st
The Chairman of MYCN, Gombe Chapter

20/12/2025

Life's journey twists and turns,
Redirection's not a roadblock that burns,
But a detour to a better place,
A chance to find a new pace.

Don't lose hope when paths diverge,
See the opportunity, let go of the urge,
To cling to what's familiar and known,
For in the unknown, a brighter dawn is sown.

Setbacks are stepping stones to growth,
Alternative routes to a better truth,
Trust that every redirection's guide,
To a future bright, where dreams reside.

So when life pushes you off course,
Don't be discouraged, find your force,
In every detour, a new path's laid,
Leading you to a brighter day.

When all seems lost, and you are at your end
Allah shows up, with a miracle to lend
A helping hand, a guiding light
A new beginning, a fresh sight

So hold on tight, don't let go
For in His time, the miracle will show
Allah's love and power, will see you through
And in His presence, hope will shine anew

Always have hope

Signed: Motivator & Author Kaleemullah Ahmad Hinna (Hasken Yamaltu) The 1st
The Chairman of MYCN Gombe Chapter

19/12/2025

Be proud of yourself for how far you've come and never stop pushing to be the best you can be.

25/08/2024

IDAN KAI MARUBUCI NE, KA QARA DUBA TSARIN ALQALAMIN KA!

A sansanin tasarrufin sarrafa irin kalar alqalamin ka, kada kace sannu da zuwa idan kasan ba baqo ka gani ba, babu laifi don kace ina maka barka da dawowa, domin da yan gida ake sanin abokan zaman su.

Zance nake sakewa don gudun samun tangarďar kifewar bazata. Watakila zaka ce na wofantar da tunanin ka, sam abun ba haka bane. Taho muje ka rakani don bana so kamin nisa, muje tare, mu koyo kada mu yarda fai'dan hakan ya ku6uce mana ni dakai baki ďaya.

Ban kai ga dasa Ayah ba tukunna. Nasan kana sauri kaga mene ne zai zama qarshen furucin nawa. Ah ah, kada kasha mamaki, idan kasani hakan bai zama abun ďaga hankali ba gare ka. Manufar shine, zai fi kyautuwa ga mai isar da saqo, ya zama ya tattaro dukkan tunanin sa yayin shirya tsarin hakan gare shi.

Banbancin dabba da mutum shine zurfafa tunani bisa lura da ankararwa kan mai zan rubuta, mai ya k**ata ace rubutun nawa ya karkata kansa? Ka zama cikin shirin baje kolin irin qarfin fahimtar ka a bisa adalci da sanin ya k**ata.

Ko shakka babu, ba dukkan mai rubutu bane marubuci, kaifin nazari da wanzar dashi bisa tsarin da ya k**ata shine asalin batuna kuma shine tubalin da nake magana kansa don ginin zancena. Idan zaka rubuta ka nutsu, sannan ka hanga kuma ka hango a irin mahangar tabarau na qwaqwalwar ka, don baka ta6a rubuta wani abu face hakan ya nuna shine asalin taswirar irin qwaqwalwar da kake tunani dashi. Me kake so ka rubuta, kuma wani irin fa'ida hakan ya qunsa?

Tambayar ce tana da nauyin gaske, amma ga dukkan wanda ya yi tanadin tawada da kaifaffen alqalami mai kyau, yasan inda mafarin tashin sa yake da kuma inda zai qarqare, wanda daman tuncan yasan irin guzurin tunanin da ya yi kafin ya ďora alqalamin nashi don fara rubutun sa.

Haqiqa, abunda ke rarraba tsakanin tsaki, dusa da gari mai kyau shine, tankaďe da rairaye, hakan shine zai baka damar gano manufata. Har kullum kada ka nuna kidahumanci da rashin sanin abunda kake zantawa kansa a ya yin da kake rubutu. Mai kake son rubutawa, mai ka rubuta kafun ka sake rubutun naka, sannan shin hakan babu matsala ciki b***e har yakai ga ya cutar da wanin ka? Ina anfanin ka riqe alqalami amma baka san mai za ka rubuta ba, sai wauta da sakarci? Anfanuwar ka yana cikin sanin haqinanin abunda tsaftatcccen tunani ya tantance shi.

Kasani cewa akan yi son barka ne kan abunda ya zama tabbatacce abun yabawa, sai ka zama cikin shiri don fafe gorar ka kafun tasamma balaguro cikin hanyar ka. Mai fahimtar gaskiya shine wanda ya sakankance zuciyar shi bisa fahimtar abunda ya k**ata ya fahimta, ba tare da anyi ja in ja dashi ba. Dolo wawa shike shigar bultu cikin duhun dajin da baisan maqurar sa ba. Ba barin inda ka fito ba, shin kasan hanyar da ka k**a zuwa ga matakin da inda kake son isa ko a'a?

Haqiqanin saqo na shine, kayi rubutu mai sunan rubutu, kada ka zama mai hauma hauma da baragada, daga qarshe kayi tsammanin ka ta6uka abu mai kyau alhali kaine abun tausayi, waďanda ke kewaye da kai suna maka kallon marar tunani, kai ko kana ganin hakan a matsayin cin nasara. Idan zaka yi rubutu kasan mai za ka rubuta a dandalin facebook da duk sauran sassan kakafen sadarwa, don banbancin dake tsakanin Jaki da mutum shine tunani. Mu huta gajiya, sai kuma wani jiqon.

Allah ya datar damu bisa hanyar dacewa

Signed: Motivator & Author Kaleemullah Ahmad Hinna (Hasken Yamaltu) The 1st

06/05/2024

“Gombawa diban Fari. Ba a kwan daku ba, amma an tashi daku” Mun gode Hauwa yar Fulanin Gombe. A lokaci huda ga ruwan sama na sauka a Birnin Bubayero (Gombe).
اللهم صيبا نافعا

05/05/2024

Babu masu ruruta maganar wannan Hadith na makomar iyayen fiyayyen halitta, fiye da wadanda suke qoqarin qaryatawa a fakaice. Idan bakwa so a yada, meyasa kuke ta kumfar baki? Ku taqaitu mana tunda baku yarda ba. Allah shine masani

02/05/2024

KA GYARA AQEEDAR KA

Mafi ingancin musulunci shine musuluncin da Manzon yazo dashi ya kuma koyar da Sahabban sa kansa. Shiko musulunci baya ta6a inganta ya zama kar6a66e abun yardewa sai dole an tabbata kan irin karantarwar da Manzon Allah yayi daga Qur'ani da kuma maganganun sa, ayyukan sa na ga66ai da waďanda ke bayan haka (Sunnah). Shiyasa Aqeeedah shine musulunci, shima musulunci shine Aqeedah, abubuwan dake qarfafa haka sune madogarori biyu: Qur'ani da Sunnah.

Ko shakka babu, sune ke koyar da tabbatuwar ingantaccen Aqeedah, wanda dukkan wanda yayi sake da haka babu makawa ya kauce ga barin karantarwan Musulunci a bisa hasken Qur'ani da Sunnah. Shiyasa qinshiqin asalin tushen gyaruwar Aqeedah yana tattare da maganganu da ayyuka wanda Imani dasu da qudurce hakan cikin zuciya ta irin fuskar da aka koyar da ita bisa Sunnah shi ake kira gyaran Adeedah. A tattare da haka tushen sa yana ta'allaquwa da abubuwa waďanda Malamai s**a karantar da abunda haqiqanin Imani ya qunsa wanda hakan ke tabbtar da gyaruwar Adqeeda. Ga abunda Malamai s**a ce:

العقيدة الصحيحة تتلخص في: الإيمان بالله، وملائكته، وكتبه، ورسله، واليوم الآخر، وبالقدر خيره وشره، فهذه الأمور الستة هي أصول العقيدة الصحيحة

"Aqeedah ingantacciya tana tsarkaka ne cikin: Imani da Allah, da Mala'ikun sa, Littatafan sa, da Mazannin sa (Annabawa yan aike) da Ranar Qarshe da Qaddara alkhairin sa da sharrin sa. Waďannan al'amura shida sune asalin Aqeeda Ingantacce"

Haka nan mafi sauqin abunda zamu karkata kansa don imgata Aqeedah shine, ga tambayar da akayi wa Sheikh Bin baz kan yanda ya k**ata mutum ya gyara Aqeedar sa:

السؤال:
يقول هذا السائل: كيف يصحح المسلم العقيدة الإسلامية، وكيف يحافظ عليها؟

"Wannan mai tambyar yana cewa: Yaya Musulmi zai gyara Aqeedar sa ta Musulunci, yaya zai kiyaye akan ta?

الجواب:
يتفقه في الدين، يتبصر ويتعلم حتى يعرف العقيدة ويحافظ عليها، يسأل أهل العلم، وإن كان طالب علم يتأمل القرآن والسنة، حتى يعرف العقيدة الصحيحة التي دل عليها القرآن، ويتمسك بها، ويستقيم عليها، وإذا كان عنده إشكال يسأل أهل العلم الذين يثق فيهم ويطمئن إليهم عما أشكل عليه، حتى يكون على بصيرة.

نور على الدرب: كيفية تصحيح العقيدة

"Yayi fahimta cikin Addini, yayi dubiya ya koya har sai yasan Aqeedah ya kuma kiyaye akan ta, ya kuma tambayi Ma'abota ilimi, idan ya kasance Dalibin ilimi yana lura da Qur'ani da Sunnah, har sai yasan Aqeeda Ingantacciya wacce Qur'ani ke nuni akan ta, yayi riqo da ita ya daidaitu akan ta, idan ya kasance yana da matsala ya tambayi ma'abota ilimi waďanda yake da tabbaci akansu yake kuma da nutsuwa dasu kan abunda ya shige masa duhu akan sa, har sai ya kasance akan basira"

Wannan kenan a taqaice

Signed: Motivator & Author Abu Imtiyaz Ahmad Hinna (Hasken Yamaltu) The 1st

01/05/2024

"Allah ba zai yi umurni kan wani abu ba, face Shaid'an ya samu macira guda biyu, ya cira mutane ga wufce iyaka da qetarewa, wasu kuma ya kira su ga kasawa, da ja da baya wajen kasa zuwa inda ake so aje" Ibnul Qayyim

01/05/2024

Babu wadanda s**a fi cin mutuncin Manzon Allah da qasqantar da lamarin sa fiye da sufaye, musamman yan Tijjaniya. A cikinsu ake samun wanda zai ce maka Salatul Fatih gba yake Salatin Annabi (Ibrahimiyyah). Ance ga Hadisin Annabi an karanta anyi bayani, amma sun qaryata. Anya kuwa son Manzon Allah kuke da gaske. Abun mamaki harda Ahlus-Sunnah masu qoqarin tawili don faranta ma maqiya Annabi rai.

Annabi Muhammad yafi mu son mahaifan sa, wannan ma dalilin da yasa yace:

استأذنت ربي في أن أستغفر لها فلم يؤذن لي ، واستأذنته في أن أزور قبرها فأذن لي

“Na nemi izinin Ubangijina na nema mata gafara. Ammai bai bani izini ba. Kuma na nemi izinin sa na ziyarci qabarin ta, ya bani izini”

Allah ya fimu sanin hikimar sa na zartas da haka. Don haka, rashin sallamawar ka game da lamarin ubangiji, kana nuna kokontar da abun da yaja hankalin ka da cewa:
“وَمَا تَشَاءُونَ إِلَّا أَن يَشَاءَ اللَّهُ رَبُّ الْعَالَمِينَ”

“Abunda kuke so sai abunda yaso, Ubangijin dukkan halittu”

Assa’idy yace:

فمشيئته نافذة، لا يمكن أن تعارض أو تمانع

“Mashi’ar sa a taskance take, bai yiwuya ayi jayayya da ita, kuma babu wanda zai hana”

Don haka, Allah yafi kowa sanin irin hikimar da ya tsara a cikin Mashi’arsa. Babu mai cewa don me yasa Allah ya yi kaza da kaza

لَا يُسْـَٔلُ عَمَّا يَفْعَلُ وَهُمْ يُسْـَٔلُونَ
(الأنبياء - 23)

“Ba a tambayar kan abun yake aikatawa, sune mutane za a tambaya”

Don haka, shi Annabin mu Muhammad dan aiken Allah ne, babu wanda yakai shi gata cikin dukkan halittun Allah a wajen Allah. Ya isar da saqon da aka saukar masa, indai kai masoyin sa ne da gaske, yin Imani da haka shine haqiqanin soyayya gare shi. Amma ka dinga chakuda haskiya da qarya da sunan Son Annabi, qarya ne, yaudarar kanka kake yi. Allah shine Masani

Allah ya nuna mana daidai

Signed: Motivator & Author Abu Imtiyaz Ahmad Hinna

01/05/2024

Duk ilimin da kaji ana tattauna shi, musamman ace a daga Sunnah yazo, ana tattauna shi ne don ya tabbata. Amma zancen kace a daina tattauna shi tabbas akwai sakarci a ciki, saidai daman idan ba daga Sunnar yazo ba. Idan kace ba riba, ribar kenan ayi bayanin sa yadda yazo. Allah shine masani

Signed: Motivator & Author Abu Imtiyaz Ahmad Hinna (Hasken Yamaltu) The 1st

30/04/2024

Dole duk wani masoyin Manzon Allah na gaskiya, zai ji wani abu a ransa na rashin jin dadi, a duk sadda aka ambaci wannan Hadisi na cewa iyayensa na wuta. Saidai Sallama wa lamarin Ubangiji shine mafi qololuwar nuna soyayya ga Manzon Allah. Allah shine masani

Want your school to be the top-listed School/college in Abuja?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Website

Address


Abuja