21/04/2026
Prof Ibrahim Ahmad Maqari Fans
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Prof Ibrahim Ahmad Maqari Fans, Tutor/Teacher, Abuja Central Mosque, Abuja.
21/04/2026
17/04/2026
Akwai waɗanda kusantarsu bashi da wani amfani sai taƙaita saurin tafiyarka cikin aiwatar da umurnin Allah
Hassada, ƙyashi, gulma, rashin bayyanannen manufa da aikin don isa gareshi, suna cikin manyan alamominsu
Ba zaka taɓa isa tudun tsira ba har sai ka koyi ganosu da ciresu cikin rayuwarka tare da sauyasu da abokan tafiyar gaske.
~Maulana Prof. Ibrahim Maqari (H)
16/04/2026
Allah Ya yafe gajiyawarmu, Ya sanyamu cikin bayin da Yake ƴantawa ba don wata ibada tamu da ta cancanci haka ba, don babu ita, sai dai kawai don girman FalalarSa wacce ta zarce duk lissafin sababi
Ina matuƙar barar Addu'arka; akan rayuwa cikin cin albarkacin Manzon Allah SallalLahu AlaiHi wa AliHi wa sallam da rasuwa cikin Musulunci
15/04/2026
Kada ka boye gaskiya saboda kwaɗayin wani abu, ko tsoron rasa wani abu daga wani mutum..
Babu abinda ya cancanci tsoro, ko kwaɗayi sai abinda zai amfaneka a lahzar wafatinka
14/04/2026
Alƙur'ani Mai Girma Ya zo ne domin tabbatar da manufofi guda uku:
- Kadaitawa (Tauheedi) :Tsakanin Bawa da Mahaliccinsa
- Gyaran Zuciya (Tazkiyah) : Tsakanin Bawa da Kansa
- Ingantawa/Kyautatawa (Umran): Tsakanin Bawa da dukka sauran halittar Allah
Ka rubutashi a zuciya, ka mayar dashi ma'auninka cikin komai a rayuwa..
Zaka dace insha Allah
13/04/2026
Yazama wajibi muso birnin Madina
Bayan an taƙurawa Manzon Allah S.A.W a Makka yayi Hijira daga Makka zuwa Madina,
Mutanen Madina sun yiwa Manzon Allah S.A.W kyakkyawar Tarba
Sun bashi masauki sunyi imani da shi
Sun baiwa Manzon Allah S.A.W kariya
Sun baiwa Masoyansa kariya
Kuma Makwancin Manzon Allah S.A.W yana Birnin Madina
Wallahi yazama wajibi muso birnin Madina Saboda Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam yana cikinta
12/04/2026
Kada tsanar mafi yawan mutane ta dameka, sau da yawa alama ce ta bijirewa soye-soyen rayukansu.
Ka tuna cewa mafi yawan waɗanda a yau muke tutaya dasu, mafi yawan mutanen zamaninsu sun tsanesu
08/04/2026
“ Allah Mun gode
•Allah ka kara daukaka gaskiya akan karya
• Adalci akan zalumci
•Imani akan kafirci
Allah ka kara taimakon jamhuriyar Musulunci akan Sahaniya da masoyansu”
04/04/2026
Idan bayi s**a yi sakaci cikin wani abu da Allah Ya basu iko akansa, to Allah Ba zai canza yanayin da wannan sakaci ya kawo masu ba har sai sun canza halayensu..
Amma kada muyi ƙasa a gwiwa, domin duk abinda sakacin Ɗan-Adam ne ya haifar dashi, ƙoƙarin Ɗan-Adam zai iya gyarashi
03/04/2026
Babu abinda da ya halakar da Al'ummun da s**a gabacemu sai (selective justice)
Sun kasance idan wane ɗan wane yayi laifi, sai suyi masa kwaskwarima.
Idan kuma talaka ne yayi laifi, sai su gwada iko da fushi akansa.
02/04/2026
Mayar da Malaman Addini mabarata yana daga cikin mafi girman makircin masu mulkin Mallaka.
Duk malamin da ba zai iya kamewa daga roƙon kowa komai na duniya ba to ya nemi sana'a ya haƙura daga karantarwa domin bai cancanci a amince masa a cikin isar da saqon Allah ba
31/03/2026
Ya Allah
Shugabanninmu sun kasa,
Jami’an tsaronmu sun kasa,
Talakawa mun kasa,
Kowa da kowa ya kasa
Ya Allah Kai Mai Iko ne marar tuqewa,
Ya Allah Kai Mai Isa ne marar Iyaka
Ya Allah mun tuba
Ya Allah Ka iya mana abinda ba zamu Iya ba
Babu iyawa sai IyawarKa
Click here to claim your Sponsored Listing.
Location
Category
Culinary Team
Attire
Website
Address
Abuja Central Mosque
Abuja