10/08/2023
All History of Islamic movement onder leadership sharfudden
Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from All History of Islamic movement onder leadership sharfudden, Education, Abuja.
10/08/2023
07/08/2023
TSAKANINMU DA NIJAR YA FI KARFIN DANJUMA DA DANJUMMAI, HASAN DA HUSAINI NE!
- Inji Jagora Shaikh Zakzaky
Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)
Da yake ganawa da kungiyar Mahaddatan Alkur’ani daga Cibiyar Karatun Alkur’ani mai girma (CQR) a gidansa da ke Abuja, ranar Asabar 18 ga watan Almuharram 1445 (5/8/2023), Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya bayyana takaicinsa a kan yadda makiya ke neman hada rigima tsakanin Nijeriya da Nijar don cimma muradin kashin kansu.
Shaikh Zakzaky ya ce: “Abin Allah ya kiyaye, yanzu ga shi haka kawai, haka siddan, Faransa da Amurka sun zo za su yi amfani da Nijeriya su kai wa Nijar hari. To, wannan abu da ban-al’ajabi shi ma. Don mu tsakaninmu da Nijar muna ganin abu daya ne, in ma Kudu suna ganin ba su a ciki, to mu nan Arewacin Nijeriya an yi daular Shehu Usman Danfodiyo, da kuma Daular Borno. Wadannan daulolin guda biyu, su aka tsaga su tsakanin Nijer da Nijeriya.”
Ya ce: “Kun ga da nake ce muku Gazargamu shi ne babban birnin Borno ko? To har yanzu ganuwar garin na nan, don an bar garin da wadansu gine-gine. To kun san rabin ganuwar garin yana Nijar ne (yanzu haka), rabin ganuwar yana Nijeria, an tsaga biyu ne kan iyaka din. Lokacin da ake tsaga kan iyakan nan, ba su yi la’akari da tarihinmu ba.”
Jagora ya cigaba da cewa: “Kamar yadda nake ce muku, Borno an raba ta hudu, Nijeriya, Kamaru, Chadi, da Nijer, duk Borno ne. Sannan kuma idan ka bi Daular Shehu Usmanu, tun daga Borno din har ka kai Sakkwato kowane gari an raba shi biyu ne. Ainihin za ka ga Hadejia akwai wani bangare ya koma Nijar (a yanzu bayan da Turawa s**a tsaga), Gumel wani bangare ya koma Nijar, in ka je kana wuce Maigatari, idan ka tsallaka Gumel kake, amma ya koma Nijar. Kazaure ma haka nan wani wuri yana Nijar.
“To Daura ma haka, mafi yawan Daura ma Nijar ta koma. Mafi yawan Daura tana Nijar ne (a yanzu). Katsina ma an raba ta biyu, da Katsinan Maradi da Katsinan Katsina. Haka aka raba. Sannan kuma Daular Gobir ta da, an raba ta ne, wasu na bangaren Nijar, wasu na Nijeriya. Mahaifan Shehu Usman Danfodiyo, Marata, tana cikin Nijar.”
Shaikh Zakzaky yace: “Saboda haka mu tsakaninmu nan da Nijar, ya wuce kace tsakanin Danjuma da Danjummai, don Danjuma da Danjummai suna s**a tara, mu Hasan da Husaini ne, uwarmu daya ubanmu daya. An fahimta ai!”
Yace: “Su ne Hasan, tunda mahaifan babanmu Shehu Usman Danfodiyo yana wajensu, sabida haka su ne Hasan, mu ne Husaini din. Mu bamu san yadda za a yi a ce ko da mafarki wai muna fada da junanmu ba. Amma ka ga wadannan la’anannun mutane, sun zo wai su ne za su yi amfani da nan su je su kai ma ‘yan uwanmu hari. Mu kashe kanmu kenan ko?”
Ya nesanta al’ummar Nijeriya daga al’amarin da cewa: “Na ji wadansu ‘yan Nijar suna cewa Nijeriya za su kawo musu hari. Nace, a’a ku daina cewa haka nan, in ma abin ace an kai muku hari ne, -Allah Ya sauwake. Ina fata ba zai auku ba. To ba mu ne muka kai muku hari ba, ainihin an yi amfani da wani ne, wanda aka ce shi ne shugaban kasa, aka je aka kai muku hari. Ba dai Nijeriya ba, ba da yawunmu ba, ba da saninmu ba, ba da amincewarmu ba, ba yadda za a yi mu kashe kanmu! Saboda haka, ba Nijeriya za ta kai hari ba, wasu ne za su yi amfani da Nijeriya. Kuma sun sha yi.”
Shaikh Zakzaky, ya ba da misalan yadda Amurka ta rika hada fada tsakanin kasashen da suke makwafta ko tare da juna, kamar yadda ta hada yakin da aka shekara takwas ana yi tsakanin Saddam Husaini daga Iraq da kasar Iran, alhali tuntuni kasashen Iran da Iraq suna daukar kansu a matsayin al’umma guda ne.
Ya kuma ba da misalin yadda Amurka ta hada fada tsakanin Saudi Arabiyya da Yemen. Da kuma yadda Faransa da Amurka s**a hadu wajen haddasa fadan Kabilanci tsakanin kabilun Hutu da Tutsi a Afirka ta Yamma inda s**a rika kashe junansu, da makamantansu.
Sannan ya yi gargadi da cewa: “Don mu gargadi masu zumudin za su je su kaima Nijar hari, su sani cewa za su yi babban kuskure. Ba mu fatan ya auku, amma in abin su yi ne, za su yi ma makiya aiki ne, kuma in ba su burge makiyan ba karshe, yadda aka rataye Saddam shi ma wannan Agwalagwa din haka za su rataye shi. Basu ga amfaninshi ba (a lokacin), ya gama amfani.”
Jagora yace: “Tunkuda shi za su yi ya yi barna, shi ya dauka zai zama gwarzo ne. Yanzu an ce har ya katse Lantarki, ya kuma rufe Boda (kan iyaka). To ai duk wannan bashi da iko ma ya yi bisa ka’ida. Ba an ce za a yi Damukuradiyya ba ne? Wai zai kai Damukuradiyya ne Nijar ba? To Damukurdiyya ne ya bashi damar ya katse wutan lantarki? Wutan landarkin nan wa ya katse ma? Sojojon da suke mulki ya katse ma ko mutanen Nijar? Mutane ne suke amfani da shi. Kuma ciniki ne aka yi ai, yarjejeniya ne aka yi ai, suna biya ne, ba kyauta ake basu wutan ba.”
Yace: “Kuma ECOWAS, ba kungiya ce ta tsaro ta soja ba, “Ecowas” kamar sunan shi ne ‘Economic Community’, ainihin sha’anin Tattalin arziki ne ya hada su, ba yaki ba. Ba inda aka rubuta a cikin tsarinsu za su kai yaki. Ba aikinsu ba ne. Amma yanzu aka zo wai da sunan Ecowas ne (za a kai hari). To kuma yanzu sun fara tunanin Nijeriya ne ma da Nijar za a kai hari. Allah Ya sauwake.”
A karshen ganawarsa da Gwanaye da Alarammomin, Shaikh Zakzaky ya jaddada musu cewa, ba mu da makamin da ya wuce riko da Allah Ta’ala. Mu koma ga Allah Ta’ala.
Ya kuma yi addu’a da fatan neman taimakon Allah Ta’ala, tare da kira ga re su da cewa: “A cigaba da Ihtimami da Alkur’ani kamar yadda ake yi, Alhamdulillahi mun godewa Allah. Wannan ni’ima ce babba. Mun godewa Allah da wannan ni’ima. Ba wata ni’ima kamarta, wanda duk Allah Ya bashi Alkur’ani, to kar ya ga an ba wani wani abu ya ga ya fi shi, domin shi yana da abin da ya fi komai.”
06/08/2023
21/07/2023
21/07/2023
Sanarwa:
بسم الله الرحمن الرحيم
اللهم صل على محمد وال محمد وعجل فرجهم.
Ana sanar da yan'uwa cewa yau Talata 29 ga Zhul Hijjah shekarar 1444 ta kare don ta cika kwana 354 daidai. Kuma ba ta zama kabisa ba kamar yadda muka zata. Don haka gobe Laraba za ta zama 1 ga watan Al-Muharram 1445.
Kamar yadda aka saba za a shiga zaman jajen tunawa da shahadar Abi Abdillah (AS).
18/07/2023
20/07/2023
A cikin
wasikar da Imam (SA) ya aikawa kaninsa Muhammad bin Hanafiyyah, ya bayyana dalilan da s**a sanya shi barin Madina da kuma jagorantar wannan babban yunkuri na fada da mulkin zaluncin banu Umayyawa, inda yace:
"وأني لم أخرج أشرا ولا بطرا ولا مفسدا ولا ظالما وإنما خرجت لطلب الاصلاح في أمة جدي صلى الله عليه وآله أريد أن آمر بالمعروف وأنهى عن المنكر، وأسير بسيرة جدي وأبي علي..."
Hausa:
"Ni ban fito domin girman kai ko alfahari ba, ba kuma domin barna a bayan kasa ko zalunci ba. Abin da kawai ya fito da ni shi ne neman gyara a cikin al'ummar kakana, Manzon Allah (SA). Ina nufin yin umurni da kyakkyawan aiki da hana mummuna, in kuma bi irin rayuwar kakana da babana Ali bin Abi Talib (SA)....."
Madogara: Maqtalul Husaini na Khawarizmi, juzu'i na 1, shafi na 88.
لبيك ياحسين✋️✋️
19/07/2023
16/07/2023
Update
(04)
“A SHIGA A GYARA, BA MAFITA BA CE!”
Masu cewa za su shiga cikin lalataccen tsarin Nijeriya su yi gyara, mafarki suke yi. Batun shiga cikin lalataccen tsari ka ce za ka kawo gyara, to sai dai tsarin ya lalataka! Tsarin da ya rube ya lalace, tarkata shi ake a watsar a bola a qona! A kawo sabo a shinfixa! Gwamnatin qasar nan ginin Toka ce!
“JUYIN JUYA HALI NE MAFITA, BA CANJIN GWAMNATI BA!”
Canja Gwamnati ta hanyar katin zave ba shi ne mafita na halin quncin rayuwa da ake ciki ba, kullum aka samu sabon shugaba sai an ce gara na baya da shi, kuma hakan zai ci gaba muddin ba mun canza tsarin bane. Kamar mota ce ta rigaya ta lalace, injinta ya buga, sai ka ce ai direban ne bai iya tuqi ba, ka cire wannan ka sanya wancan, to, in ba ka gyara motar ba ne, babu yadda za a yi ta koma daidai, saboda ainihin lamarin ba direban ba ne, motar ce! Dan haka, qasar nan tana buqatar ‘Juyin Juya Hali ne’ ba ‘Canjin Gwamnati ba!.
Allah (T) Yakawo mana Karshen Zalinci da Azzalumai Bihakki Muhammad wa ahli muhammad wa ajjil F***j.
16/07/2023
Click here to claim your Sponsored Listing.
Location
Category
Website
Address
Abuja