Learn • Relearn • Unlearn

Learn • Relearn • Unlearn Question what you know. Explore what you don't. Think beyond assumptions.

🌍 THE WORLD IS FULL OF THINGS WE DON'T KNOW.Every day, we encounter things we barely stop to think about.Why do some cul...
04/09/2026

🌍 THE WORLD IS FULL OF THINGS WE DON'T KNOW.

Every day, we encounter things we barely stop to think about.

Why do some cultures do things differently?
How did ancient people solve problems without modern technology?
Why do humans behave the way they do?
Who decided that certain things should be done the way they are?
What stories have disappeared from history?
And what discoveries are still waiting to be made?

Curiosity doesn't belong to one subject.

It belongs to everything.

Here, we'll explore the fascinating, the strange, the forgotten, the controversial and the unexpected.

Sometimes we'll learn something new.

Sometimes we'll relearn something we thought we understood.

And sometimes we'll unlearn an assumption we never thought to question.

Learn • Relearn • Unlearn

Question. Explore. Understand.

Sararin Rana ( Sun's atmosphere) yafi doron ta zafi! Tsakiyan Rana yana da tsananin zafin da yakai 15 million degree cel...
27/04/2026

Sararin Rana ( Sun's atmosphere) yafi doron ta zafi!

Tsakiyan Rana yana da tsananin zafin da yakai 15 million degree celsius, tsananin zafin da ya nunka zafin volcano 🌋 sau sama 2500, ta yadda babu wani abu a wannan duniya da zai iya jure ko kusa da wannan zafin.

A yayin da doron Ranar kuma yake da zafin 5,500 degree celsius. Amma ga mamakin masana kimiyya shi kuma outermost sun's atmosphere abinda ake kira da corona yana da zafin da yakai sama 1 million degree celsius.

Hakan ya zama abu mai daure kai ga scientists, domin kamar ace ne, zafin tiririn tukunya a daidai ta wajen ceiling din kitchen, yafi murfin tukunyar zafi da kusan miliyan guda.
Wannan shine abinda scientists s**a kira da "coronal heating problem".

Intercontinental Ballistic Missile (ICBM) 🚀Mizayil ne wanda aka tsara shi don yin tafiya mai nisan kilomitoti, nisan da ...
15/04/2026

Intercontinental Ballistic Missile (ICBM) 🚀

Mizayil ne wanda aka tsara shi don yin tafiya mai nisan kilomitoti, nisan da yakan tsallake nahiyoyi.

Yanda yake aiki shine:

Ana harba shi ne zuwa cikin sararin samaniya, kamar yanda ake harba Roka(rocket) Sai ya dauki hanya lankwasasshe(curve) da ake kira "ballistic trajectory"
Bayan yayi tafiya mai nisa a cikin sararin samaniya, cikin sananin sauri sai ya fado kan abun da aka hara(target)

Abubuwan da ya kumsa:

Yakan yi nisan kilomitoti 5,500 zuwa sama, a zahiri, yafi nisan Makkah zuwa Lagos.

Yana da tsananin saurin tafiya(extreme speed)

Yana dauke da abubuwan fashewa(warheads)

Yana da matukar wahalar kakkabewa idan aka harbo shi

Cruise Missile 🛩️

Shi cruise missile, mizayil ne wanda ake sarrafa shi yayi tafiya kamar yanda ake sarrafa tafiyan jirgin sama.

Ga yanda yake aiki:

Shi yana tafiya ne kasa-kasa don kada na'urar Radar na kakkabo Roka ta iya gano shi(to avoid radar) ya kakkabe shi.

Yana amfani ne da inji irin na jirgin Jet don tuka shi a sama cikin iska.

Ana sarrafa tafiyansa ne da na'urar tsarin GPS, da Radar ko taswirar doron Kasa.

Abubuwan da ya kumsa:
Yana yin dogon zangon da baya wuce daruruwan zuwa duban kilomitoti

Bashi da saurin tafiya irin na Ballistic Missile.

Amma yafi Ballistic Missile samun target yanda ya kamata

Yana dauke da abubuwan fashewa kamar irin na Ballistic

Drones (Misalin irin na Iran, Shahed drones) 🛸

Drones sune kananun jirage marasa matuka, wasun su, ana amfani da su ne don yin leken asiri ko kai harin Bom.

Misalansu sune:

Irin su Shahed 136 na Kasar Iran, da Lucas na Kasar US.

Yanda drones masu kai hari suke aiki:

Ana sarrafa su ne daga gida ko a gina su ta hanyan computer programming don kai hari da kansu

Wasun su, suna yawo ne a sararin samaniyan wurin da za su kai hari, kafin su fara kaddamar da harin, suna tafiya ne kasa-kasa, suna da arha wurin kerasu, sannan suna da amfani sosai.

Abubuwan da s**a kumsa:

Sukan yi nisan tafiyan daruruwan kilomita zuwa duban kilomitoti, kamar yanda Shahed na Iran muka ga yayi nisan zangon da ya haura kilomitoti 2500.

Basu da saurin tafiya kamar irin na missiles
Basu da tsada wurin kera su
Yawanci ana amfani da su ne da yawa wurin kai hari(swarm attacks)

Cluster mu*****ns missiles

Mizayil ne na makami wanda basu fashewa a wuri guda, Sai dai su bude a sararin samaniya su rarrabu su zama kananan Bom da yawa da ake kiransu "submu*****ns ko bombletes" su faffadi a wurare daban-daban.

Cluster Mu*****ns kontena ne da yake dauke da kananun bomabomai wanda yake fashewa a sararin samaniyan wurin da zai kaddamar da hari

Yanda yake aiki shine:
Idan aka harba shi, ya tafi a sararin samaniya, ya iso wurin da ake so a kaddamar da harin, a cikin sararin samaniyan sai ya fashe ya zubar da kananan bomabomai, su rika fadowa suna fashewa idan s**a yi karo da abun da suke son kai wa hari

Cluster Missile, Yana zuwa ne kamar sauran missiles, Sai dai kawai shi yana dauke ne da bomabomai masu fashewa, da yake tarwasa su zuwa kananan bomabomai su fadi a wurare daban-daban.

Dalilan da yasa Cluster Missiles yake shan s**a(criticism) shine:

1. Wurin da s**a fadi suna yin illa ne wurare daban-daban masu yawa(wide area) wanda hakan yakan shafi fararen hula.

2. Wasu daga cikin kananan bomaboman basu fashewa nan take idan sun fado kasa, sai su zauna a kasa kamar bomabomai da ake binne su a cikin kasa(mines), wanda hakan yakan zama hatsari idan aka zo cire su ko aka yi karo da su bisa kuskure.

3. Suna zama hatsari na tsawon lokaci ga fararen hula, musamman kananan yara, s**an fashe ko bayan shekaru da fadowansu.

🌍 Shin yawan ruwa a duniya yana raguwa? 💧Assalamu alaikum, ’yan uwa masu sha’awar kimiyya!A yau za mu duba wata tambaya ...
15/04/2026

🌍 Shin yawan ruwa a duniya yana raguwa? 💧

Assalamu alaikum, ’yan uwa masu sha’awar kimiyya!

A yau za mu duba wata tambaya mai muhimmanci da mutane da dama ke yi: shin yawan ruwa a duniya yana raguwa?

Amsa ta kimiyya ita ce: A’a, ba ya raguwa a ma’ana ta zahiri.

Jimlar ruwan da ke doron ƙasa—wato na cikin tekuna, koguna, tafkuna, kankara, cikin ƙasa, har ma da wanda ke cikin iska, volume nashi yakai kusan kilomita cubic biliyan 1.4 Wannan adadi ba ya canzawa sosai daga shekara zuwa shekara. Dalili kuwa shi ne: duniya tana da ingantaccen tsarin zagayowar ruwa (hydrological cycle).

Yaya wannan zagayowar ruwa yake?

Ruwa ba ya ɓacewa, sai dai yana canza wuri da yanayi:

1- Yana tashi zuwa sama sakamakon zafin rana (evaporation)
2- Yana zama gajimare (condensation)
3- Yana saukowa a matsayin ruwan sama ko ƙanƙara (precipitation)
4- Sannan yana komawa cikin ƙasa, koguna da tekuna

Saboda haka, ruwa yana ci gaba da zagayawa ba tare da yankewa ba.

Shin akwai asarar ruwa kwata-kwata?

Eh, amma kaɗan ƙwarai.
A wasu lokuta, hasken rana na iya raba ruwa zuwa hydrogen da oxygen, sai hydrogen ya tsere zuwa sararin samaniya. Amma wannan adadi ƙanƙanta ne matuƙa—ba zai kai ko kaso mai ma’ana ba a rayuwarmu.

To me ya sa wasu ke ganin ruwa yana raguwa?

Ba wai ruwan duniya ne yake raguwa ba, amma:

- Ana samun fari a wasu yankuna (saboda canjin yanayi)
- Ana gurɓata ruwa, wanda ke rage ingancinsa
- Ana amfani da ruwan ƙasa fiye da yadda yake sabuntawa

Wadannan su ne ke haifar da ƙarancin ruwa mai amfani, ba wai ƙarancin jimillar ruwa ba.

Muhimmin darasi:

Ruwa ba zai ƙare ba… Amma idan ba mu kula da shi ba, za mu iya rasa ruwa mai tsafta da amfani.

RIJIYOYIN HAKO MAI(OIL FIELDS).Yayin da aka kashe injinan hako Mai cikin gaugawa, zai iya yin illa wa rijiyoyin Mai, ill...
14/04/2026

RIJIYOYIN HAKO MAI(OIL FIELDS).

Yayin da aka kashe injinan hako Mai cikin gaugawa, zai iya yin illa wa rijiyoyin Mai, illa wanda gyaransu baya yiwuwa na har abada.

Dalili kuwa shine:

Mai da yake a karkashin Kasa yana dogara ne da karfin pressure na karkashin Kasa, Sai ya turo Mai zuwa sama(kamar misalin ka dauki kwalbar lemo ka jijjiga shi sai ka bude marfinsa, karfin iska zai turo lemon ya zubo, wannan shine pressure da ake magana a kai) kashe injinan hako Mai zai iya kawo tsaiko ma wannan daidaiton pressure din, har ya bada matsala da ake fada.

Babban hatsarin shine:

Yayin da riyoyin Mai s**a rasa wannan Pressure din, za a samu karancin Mai a cikinsu.

Cikin rijiyar Mai, Ruwa yana zama ne a Kasar Mai, yayin da aka samu sauyin Pressure ruwa zai haura sama zuwa cikin bututun Mai, Sai Ruwa ya cakudu da Mai, wanda hakan zai sa fitar da Mai yayi wahala ko ya gagara fita gabaki daya.

Hargitsewar Iskar Gas:

Shi kuma iskar Gas da ake hakowa, yana zama ne a saman Mai(oil) shi yake taimakawa wurin danno Mai ya biyo ta cikin bututu zuwa sama, sai Mai ya fito.

Kashewa da kunnawan injinan hako Mai, zai iya saka iskar Gas ya motsa ba bisa ka'ida ba, sai a samu raguwan karfin Pressure da yake fitar da Mai.

Duwatsun da suke kewaye da rijiyar Mai, wanda suke bada Mai, kofofinsu yakan toshe da Minerals da dattin laaka.

Yaya abun yake ga Kasar Iran da take fama da rikicin Yaki da America/Israel?

Jiya Kasar US ta sanar da rufe Mashigar Hormuz, idan kuwa ya tabbata Iran ba zata iya fitar da Mai ba, wurin ajiye Mai na Kasar zai cike da Mai yayin da aka ci gaba da hako Mai(oil), an kiyasta cikin kwana 13 wurin ajiye Mai na Kasar zai iya cikewa.

Shin wannan babban barazana ne ga Kasar Iran?

Da yawan wuraren rijiyoyin Mai na Kasar Iran tsofi ne(mature fields).

Irin wadannan tsofin rijiyoyin Mai din sun fi samun matsalar sauyin Pressure yayin da aka kashe injinansu aka sake kunna su.

Akwai hadurukan aukuwan damejin da ba za su gyaru ba.

Menene “Hadarukan damejin da ba za su gyaru ba ga rijiyoyin Mai”
yake nufi:

Ba wai za su rasa rijiyoyin Mai din su duka bane.

Sai dai, wasu daga cikin rijiyoyin Mai din, ba za a iya gyaransu ba na har abada, ko su zama wadanda ciran Mai a cikinsu zai chaji Iran kudi masu yawa, wanda hakan zai zama asara ce kawai.

Yawan fitar da Mai din ne zai ragu sosai na har abada.

Kashe injinan hako Mai ta hanyar da ba bisa ka'ida ba, zai rage wa Kasar yawan Mai da take hakowa na har abada musamman a tsofin rijiyoyin Mai, Sai dai damejin da za a iya samu ya dogara ne da yanda injiniyoyin za su iya manejin pressure da sauransu, wanda yin hakan abu ne mai wahala a iya yinsa cikin lokaci kankani.

14/04/2026

Jama'a ayi hakuri da post namu na gaba da zamu iya sake shi.

Ba zamu yi sa bane don musun addini ko bangaranci, ko abun da ya shafi goyon bayan wata Kasa.

Za mu yi sa ne don karuwan ilimi.

Ubangiji Da Kimiyya.Kimiyya ba wai ta yi watsi da lamuran Ubangiji bane—Kawai kimiyya ba a tsarata ta hanyan karantan la...
12/04/2026

Ubangiji Da Kimiyya.

Kimiyya ba wai ta yi watsi da lamuran Ubangiji bane—Kawai kimiyya ba a tsarata ta hanyan karantan lamuran Ubangiji ba.

Kimiyya tana aiki ne akan bayanan da ake iya daurasu akan sikelin gwaji, an gina kimiyya ne akan wani tsari da ake kira "Empiricism" wato abun da ya tabbata mana ta hanyan sani, gwaji, da tabbatarwa, akasin "theory"

Abun da ake nufi, shine duk wani Idea dole a gwada shi, a auna shi, sannan kuma a daura shi akan sikelin.

Sannan kuma, sakamakon da aka samu dole ya zama abu daya a duk lokacin da wani yabi matakin da aka bi ta farko.

Masana kimiyya sai su tambaya cewa; Zamu iya gwada wannan abun, zamu iya tabbatar da shi?

Kimiyya tana bin wani ka'ida ne da ake kira "Methodological Naturalism" — ma'ana kimiyya tana amfani ne da aukuwan yanayi sai tayi bayanin abu "Natural Cause"

Hakan ba yana nufin abin-alajabi(supernatural) karya bane, sai sai dai kawai ba a iya tabbatar da su ne a kimiyyancen

Misali, idan akayi walkiya a sararin samaniya, kimiyya zata ce maka wutan lantarki ce a cikin gajimarai.

Ba wai ba za a shigo da lamuran Ubangiji a ciki bane

Sai dai kawai don kimiyya zata iya gwajin lantarkin da yake samar da walkiya a cikin sararin samaniya.

Kimiyya ta dogara ne akan gwajin da za a iya tabbatar da shi ko akasin haka— ma'ana, kafin abu ya zama kimiyya sai inya zama za a iya tabbatar da shi ba daidai ba, akasin addini ko lamuran addini da yake zama ba a iya karyatawa.

Abu idan aka ce "Ubangiji ne sanadi" — ba zamu iya tabbatar da shi ko karyata shi a wurin gwaji ba(Lab).

Saboda haka, kimiyya ba za ta iya tabbatar da shi ko karyata shi ba, sai kimiyya ta koma gefe.

Kimiyya da Imani suna amsa tambayoyi wanda kalansu ba daya ba– ma'ana, suna mayar da hankali ne akan Ideas mabanbanta: misali;

Kimiyya zata ce; Ta yaya Kaunu take gudana?
Addini Kuma zata ce; Me Dan Adam yazo yi a Duniya, Me ma'anar rayuwan Dan Adam a doron Kasa?

Saboda haka;
Kimiyya tana fayyace yanda abubuwa suke wakana ne "mechanism".
Addini kuma suna Neman Ma'ana ne da Dalilan Rayuwan.

Kimiyya ba tana fada ne da wanzuwan Ubangiji ba, kawai kimiyya tana tsaka-tsaki ne

Bata tabbatar da samuwan Ubangiji
Bata kuma karyata samuwansa

Kawai, kimiyya tana da hanyoyinta da take bi wurin lamuran gwaje-gwajenta, wasu tambayoyin bata amfani da wannan hanyan wurin amsa su.

Address

Abuja

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Learn • Relearn • Unlearn posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share