13/06/2023
Congratulations Rt. Hon . Abbas Tajudden Iyan Zazzau as you emerged speaker of the 10th national assembly🙏🙏 may ALLAH SWT Guide you through. And We pray it should be of benefit to humanity (Kaduna)
Amadadin kungiyar agajin fityanul islam zaria local government akarkashin jagoranci darkhatan agaji tare da in majalisarsa muna rukon Allah yatayaka ruko Allah yadafamaka Allah yashiga lamarinka,alfarmar shugaba Annabi Muhammadu S.A.W.
✍ Zakariyya Salisu
Director media
17/05/2023
Maulana Muna Ziyara Cikin Allah
13/10/2022
MAULUD DAGA DHAMAR YEMEN
Wani Yanki Na Masu Murna Da Zagayowar Ranar Da Aka Haifi Fiyayyen Halitta Annabi Muhammadu SAW A Birnin Dhamar A Yemen.
Allah Ya Kara Wa Manzon Allah SAW Masoya, Ya Kara Mana Soyayyan Sa. Amiin
12/10/2022
Cigaba da Mauludin Annabi S.A.W
TARIHIN ANNABI MUHAMMADU SALLALLAHU ALAIHI WASALLAMA KASHI NA GOMA SHA UKU. ( 13 )
Abin da ya biyo bayan Shekarar Hijirar Habasha
A lokacin da Musulmi masu hijira a Habasha s**a samu sararawa kuma wakilan mutanen Makka s**a koma gida ba tare da samun nasarar shawo kan Sarkin Habasha ba, yanayin da Annabi (SAW) da jama’arsa suke ciki a garin Makka kuma sai kara munana yake yi. Makiya Annabi (SAW) sun sake damara don su katse hanzarinsa. Don haka s**a fito da hanyoyi daban-daban da s**a hada da kara musguna wa Musulmi da hada baki don kaurace musu da yin batanci ga Annabi (SAW) da shirya kashe shi da hana baki da s**a shigo gari saurarensa da janye kariyar kabila ga mutanensa da sauransu.
Daga cikin cutarwar fatar baki da s**a yi ga Manzon Allah (SAW) akwai kiransa da mahaukaci ko boka, ko mai sihiri, ko makaryaci, ko mai raba kan jama’a da sauransu. Amma Allah (SWT) Ya wanke shi daga wadannan zarge-zarge, kuma Ya sanya jifar da suke yi masa da wadannan miyagun kalmomi ba su yi tasiri a tsakanin mutane ba.
Kokarin Kuraishawa na kashe Annabi (SAW):
Kuraishawa sun ji bakin cikin ganin addinin yana kara samun daukaka Musulunci na ci gaba da yaduwa, kuma ga Abu Dalib (RA) ya tsaya tsayin daka wajen taimakonsa da kare shi daga farmakinsu, domin shi sadauki ne na gaske. A karshe s**a fara tunanin kamar kokarinsu yana tafiya ba tare da samun wata nasara ba, sai s**a yanke shawarar su kashe shi. A kokarin haka Utbah dan Abu Lahab ya nufi Annabi (SAW) bai yi nasara ba, Annabi (SAW) ya yi wata addu’a a kansa ya ce “Ya Allah Ka aiko masa daya daga karnukanKa. Da Utbah ya yi tafiya zuwa Sham cikin fatake s**a sauka a wani wuri sai ga zaki yana kewaya su a nan ya gane wannan zakin ne makashinsa har ya furta haka. Da za su kwanta barci sai aka sanya Utbah a tsakiyar mutane, amma da s**a yi barci haka zakin ya fizge shi ta kansa ya kashe shi.
Abu Jahil da ya ga kashe Annabi (SAW) ya ci tura kuma ya ki daina aibata abubuwan bautarsu, sai ya ce
11/10/2022
ABIN ALFAHARI
Aisha Abubakar Hussain daga jihar Kano, tazo na biyu a gasar Karatun Qur'ani na duniya izu sittin da ya gudana a Daular Larabawa Kasar Dubai
Allah Ya sa Qur'ani Ya cecemu ranar Hisabi
11/10/2022
ZALIKA FADULULLAHI YA LISANUL FAIDAI
KHADIMUL QUR'ANI
Tun Diga Farkon Halittar Duniya Irin Maulana Shehu Dahiru Usmani R t a Shika Daine Malam Munji Tarihin Magabata Mazan Gaske Kowa Da Kalar Falalarsa Irinta Maulana Shehu Dahiru Ta Dabance
Malam Ka Tabajin Mutum Kalarsa Kuwa Indai Qur'ani Ake Son Sani To Shehu Haskene Tundiga Kan Kakansa Alhaji Adamu Hafixine Masanin Qur'ani Alaramman Arammomi Hakaza Mahaifinsa Alhaji Usman Hafixine Batijjane Muqaddamine Cikin Dariqar Shehuna Ahmad Tijjani R t a Arifi Masanin Allah Mahaifiyarsa Sama Ba'a Barta Abaya Ba Itama Hafizace Batijjaniya Muqadda Mace Cikin Dariqar Shehuna Ahmad Tijjani R t a Kuma Iyayensa Sun Sallamawa Sahibul Waqty Sahibul Faidah Maulana Alhaji Ibrahim Niass R t a Iyayensa Dakan Su S**a Sallamarda Shi Agurin Maulana Niass Gausul Wara Alhamdulillah
Maulana Shehu Dahiru Hafixine Muqaddamine Cikin Dariqar Maulana Shehuna Ahmad Tijjani R t a Yanada 'Ya'ya Samada (80) Hafixai Masana Qur'ani Hakaza Jikoki Da 'Ya'yan Jikoki Suma Mafi Yawan Su (80%) Hafizaine Maulana Yayi Fuce Cikin Zamaninsa Maulana Shehu Dahiru Shehu Ibrahim Yace Da Shi Komai Kafada Nina Fada Wato Harshen Faidah (Lisanul Faidah) Tuba Nake Maulana Aikin Bai Faduwa Sautul Islam
09/10/2022
AIKI SAI MESHI LISANUL FAIDAH MAZA
ABUN AIKEN MAZA
Wani Aikin Sai Sautul Islam Lisanul Faidah Hujjar Allah Maulana Inyayi Kira Kowa Amsa Masa Yakeyi Jinnu Insu Malaku Shehu Kenan Rijalan Kenan Shehu Mai Abun Al'ajabi Na Sahibul Faidah Dattijo Muradi Haiya Shehu Uban Ibrahim Babbar Gaba Gatan Ahmad Tijjani Damo Sarkin Haquri Shehu Kai Keda Dr.Bashiru Ooo Na Sirrin Bai Hasken Duniya Aba Fatihu Ja Ragamar Zamani Maulana
Mauludun Nabiyi Kenan Da Ya Gudana A Fadilatu Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi Sautul Islam Lisanul Faidah Khudubul Fardu Na Bauchi Mai Dariqar Gado Sannu Dai Ya Khalipan Shehuna Ahmad Tijjani Gaskiyar Haqiqanin Samuwar Baye Gumma Niass Sahibul Waqty Labbaika Ya Sautul Islam
M Taheer Bayee
DAHIRIYYA MEDIA NEWS
09/10/2022
Sama Da Islamiyoyi Dubu Biyar Ne S**a Fito Zagayen Maulidin Annabi Muhammadu ﷺ A Birnin Gombe Da Kewaya Don Nuna Murna Da Zagayowar Ranar Da Aka Haifi Fiyayyen Halitta Manzon Allah SAW Maza Da Mata
Allah Ya Kara Mana Soyayyan Manzon Allah SAW Ya Sa Mu Yi Taro Lafiya. Amin.
07/10/2022
Yadda Dubban Al’ummar Musulmi s**a fito zagayen Mauludin Annabi Muhammadu SAW na bana, a garin Patiskum da ke jihar Yobe.
📷: El-Tafseer
07/10/2022
INNAL'ILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN!!
Allah ya yi wa Ɗan Agajin Munazzatul Fityanul Islam Rasuwa, Sakamakon Ambaliyar Ruwa da yayi awon gaba dashi.
Allah Ya jiƙanshi ya karɓi shahadar shi..🤲
29/09/2022
NASIHOHI GUDA SITTIN (60) GA MATA
1 Karki kasance mace marar kamun kai.
2 ki kasance mace mai kunya.
3 ki kasance mace mai tsare mutuncinta.
4 ki kasance mace mai nutsuwa.
5 ki kasance mace mai gaskiya.
6 ki kasance mace mai rikon amana.
7 babu ruwanki dayin gulman mutane.
8 karki yarda ki zama munafuka.
9 ki zauna da kowa lafiya.
10 karki yarda da shaidanun wasu mazan zamani.
11 babu ruwanki dayin kawa ta banza.
12 idan kinga kawarki batada kamun kai kiyi nisa da ita.
13 karki kuskura kina shiga abinda bai dame ki ba.
14 kiyiwa iyayenki biyayyah.
15 kiyiwa mijinki biyayyah.
16 ki girmama 'yan'uwan mijinki.
17 ki girmama iyayen mijinki.
18 karki yarda da zugan kawaye.
19 karki yarda asaki a hanyar dabata dace ba.
20 ki dinga rufawa mijinki Asiri.
21 karki kuskura kina tonawa mijinki asiri.
22 ki zama mace jaruma.
23 ki zama mace mai hakuri
24 ki zama mace mai kula da dukiyar mijinta.
25 ki zama mace mai kula da tarbiyyar 'ya'yanki.
26 karki zama mace mai kwadayi.
27 karki zama mace mai yaudara.
28 karki zama mace mai dogon buri.
29 ki zauna da mijinki da zuciya daya.
30 ki zama mace mai taimakon mijinta.
31 karki yarda kizama mace mai bin bokaye 'yan tsibbu,don zaki hallaka kanki ne.
32 karki yarda kina daga sautin muryarki wa mijinki.
33 duk kuma bacin ran dak**e ciki karki kuskura kice wa mijinki ya sakeki.
34 idan kin bata mishi rai kibashi hakuri.
35 karki zama mace mai girman kai.
36 kar kuma kina daurawa mijinki abinda yafi karfin sa.
37 karki kasance mace mai kin mijinta don wani abu yasameshi ki guje masa.
38 ki zauna da kishiyoyinki lafiya.
39 ki dauki kishiya a matsayin 'yar uwa.
40 ki kula da yaran mijinki da zuciya daya.
41 ki dinga shigar kamala idan zaki fita.
42 karki yarda ki zama ballagazar mace kina tsafta.
43 karki yarda ki kasance mace mai wulakanta iyayen miji.
44 karki yarda kina wulakanta 'yan uwan mijinki.
45 ki zama mace mai taimako.
46 ki kula da kanki Amana.
47 yiwa mijinki biyayyah.
48 kisa a zuciyarki Aljannarki k**e nema.
49 karki y
29/09/2022
MAULUDI YA ZO {2}
NASABARSA MAƊAUKAKI
Shugabanmu Annabi Muhammad sallallahu alaiHi wasallam Shi ne ɗan Abdullahi ɗan Abdulmudallib ɗan Hashim, ɗan Abdulmanafi, ɗan Ƙusayyi, ɗan Kilabi {Shi gwani ne} ɗan Murrata, ɗan Luwayyi, ɗan Galibi, ɗan Fihiri, ɗan Maliki, ɗan Nadari, ɗan Kinanata, ɗan Khuzaimat, ɗan Mudrikata, ɗan Iliyasu, ɗan Mudar, ɗan Nizar, ɗan Ma'addi, ɗan Adnana wanda nasabarsa ta tafi zuwa ga sayyiduna Isma'ila ɗan Annabi Ibrahim ba-daɗin Allah masu tsira da amincin Allah
Mahaifiyarsa ita ce Aminatu ƴar Wahabi, ɗan Abdulmanafi, ɗan Zuhrata, ɗan Kilabi {Shi gwani ne} kaka ne na biyar ga Annabin Allah.
Ya Allah Ka ƙara mana son Annabi da bin sunnarsa
Ameeeeeen
Mustapha Ibrahim malumfashi
28/9/2022