Barrister Rabiu Adam Fulani Katsina

Barrister Rabiu Adam Fulani Katsina

Share

Injustice to one means injustice to all, as he said not as i means.

Photos from Tambaya mabudin Ilimi's post 06/02/2022
01/02/2022

Lokacin juyin mulki ya wuce a Nijeriya, in ji Buhari

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ce ba za a sake yin juyin mulki na sojoji a Nijeriya ba.

Buhari ya faɗi hakan ne a wani martani kan damuwar da gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi ya nuna kan guguwar juyin mulki da ta taso a Afirka da ta haɗa da hamɓare gwamnatocin domokraɗiyya a Mali, Guinea da Burkina Faso.

Kamfamin Daillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya rawaito cewa Buhari ya ce ya na da ƙarfin yaƙinin cewa Nijeriya ta wuce lokacin yin juyin mulki.

Buhari ya baiyana haka ne a wata liyafa da kwamitin ƴan siyasa, ƴan kasuwa, ƴan jarida da ƙungiyoyi masu zaman kansu su ka haɗa a fadar shugaba kasa a jiya Litinin.

A watan Nuwambar 2021 ne Buhari, tsohon shugaban ƙasa na mulkin soji, ya jaddada cewa Afirka ba za ta lamunci juyin mulki ba bayan da a ka yi juyin mulki a Guinea da Mali.

Photos from Arewa Media's post 01/02/2022
01/02/2022
01/02/2022

LABARAI DA DUMI-DUMIN SU!

Yanzu haka da rana tsaka 'yan bindiga sun afkawa garin Rarah dake cikin karamar hukumar Rabah jihar Sokoto suna harbe-harbe

Rahotanni da ke zuwa mana yanzu haka sun tabbatar da cewa 'yan bindiga sun afkawa garin Rarah da ke cikin karamar hukumar Rabah jihar Sokoto.

Wani dan garin Malam Haliru Ibrahim Rarah ya shaidawa jaridar Nasara cewa yanzu haka suna can suna harbe-harbe cikin garin.

Nasara
Media News

Photos from HQ Nigerian Army's post 01/02/2022
01/02/2022

Duk Wanda Zai Gajeni Zai Kwashi Garaɓasar Gyararriyar Kasa Da Haɓɓakar Tsaro, Cewar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari

Rahoton Daily Nigerian Hausa

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi alƙawarin bar wa magajin sa gyararriyar ƙasa mai cike da haɓɓakar noma, tattalin arziki, cigaban dimokaraɗiyya da kuma haɓɓakar tsaro.

Buhari ya baiyana haka ne a wata liyafa da kwamitin ƴan siyasa, ƴan kasuwa, ƴan jarida da ƙungiyoyi masu zaman kansu su ka haɗa a fadar shugaba kasa a jiya Litinin.

Buhari ya ce yana ƙoƙarin ya bar mulki a 2023 gami da miƙawa magajinsa ƙasa mai cike da haɗin kai, zaman lafiya da ci gaba a shekaru 24 na mulkin dimokuraɗiyya ba tare da samun cikas ba.

Ya ce ƴan kasuwa maza da mata za su samu haɓɓakar kasuwanci da tattalin arziki.

Ya kuma baiyana jin daɗin sa na yadda ƴan bokon ƙasar nan su ka gane cewa gyaran ƙasar hakki ne a kan kowa da kowa.

Buhari ya ƙara da cewa akwai aiki ja a gaban ƴan ƙasa wajen gyaran ƙasar, inda ya baiyana ƙwarin gwiwa cewa gyaran ba zai gagari gwamnati da al'umma ba.

Masu karatu me zakuce?

Want your school to be the top-listed School/college in Abuja?

Click here to claim your Sponsored Listing.

Location

Telephone

Website

Address


Wuse Zone 2
Abuja