Dr. Abdurrahman Sani Yakubu Zaria.

Dr. Abdurrahman Sani Yakubu Zaria. (๐€ ๐๐ข๐ ๐ž๐ซ๐ข๐š๐ง ๐š๐œ๐š๐๐ž๐ฆ๐ข๐œ ๐ซ๐ž๐ฌ๐ž๐š๐ซ๐œ๐ก๐ž๐ซ ๐–๐ก๐จ ๐ก๐จ๐ฅ๐๐ฌ ๐š ๐๐จ๐œ๐ญ๐จ๐ซ๐š๐ญ๐ž ๐๐ž๐ ๐ซ๐ž๐ž ๐ข๐ง ๐ญ๐ก๐ž ๐Ÿ๐ข๐ž๐ฅ๐ ๐จ๐Ÿ ๐œ๐ซ๐ž๐ž๐ (๐€๐ช๐ข๐๐š๐ก) ๐š๐ญ ๐ญ๐ก๐ž ๐ˆ๐ฌ๐ฅ๐š๐ฆ๐ข๐œ ๐”๐ง๐ข๐ฏ๐ž๐ซ๐ฌ๐ข๐ญ๐ฒ ๐จ๐Ÿ ๐Œ๐š๐๐ข๐ง๐š๐ก).

18/09/2026
18/09/2026

KAI TSAYE

Daga wajen Tafsirin mako mako da Sheikh Dr Abdurrahman M. Sani Yakubu yake gabatarwa.

Masallaci: Maitama Central Mosque Abuja.
Lokaci: Tsakanin Magriba da Isha.

Allฤh ya saka da alkhairi.

NASIHA GA DALIBAN ILIMIA wajen neman ilimi, babu girman kai ko jin kaskanci. Malami ko da kuwa ya kai wani matsayi, idan...
17/09/2026

NASIHA GA DALIBAN ILIMI

A wajen neman ilimi, babu girman kai ko jin kaskanci. Malami ko da kuwa ya kai wani matsayi, idan ya samu damar amfana da ilimi, yana zama cikin tawaliโ€™u.

Dr. Abdurrahman Sani Yakubu da kansa ya zauna a ฦ™asa yana Jan baki tare ษ—aukar bayanin Sheikh Dr. Khalid ibn Abdallah Al-Maliki, a yayin karatun littafin Aqidatul-Wasitiyyah na Sheikhul-Islam Ibn Taymiyyah ุฑุญู…ู‡ ุงู„ู„ู‡.

Wannan darasi ne ga ษ—aliban ilimi: duk wanda yake son ฦ™aruwa da ilimi, ya kasance mai tawaliโ€™u, ya girmama malamai, kuma kada ya ji cewa ya riga ya isa.

๐Ÿคฒ Allah Ya ฦ™ara mana ilimi mai amfani da tawaliโ€™u.

โ€” Ofishin Yaษ—a Labarai da Sadarwa
Dr. Abdurrahman Sani Yakubu

17/09/2026

๐ŸŽ™๏ธ JAWABI CIKIN HARSHEN LARABCI

A yayin bikin rufe Daura ta Ilimi, wadda ta gudana ฦ™arฦ™ashin gudanarwar ุงู„ู…ู„ุญู‚ูŠุฉ ุงู„ุฏูŠู†ูŠุฉ ุจุณูุงุฑุฉ ุฎุงุฏู… ุงู„ุญุฑู…ูŠู† ุงู„ุดุฑูŠููŠู† ุจุฃุจูˆุฌุง โ€“ ู†ูŠุฌูŠุฑูŠุง, a JIBWIS Islamic Centre, Guzape โ€“ Abuja.

Dr. Abdurrahman Sani Yakubu Zaria ya gabatar da jawabi mai ฦ™ayatarwa cikin harshen Larabci, cike da nasiha, hikima da darussa masu amfani.

๐ŸŽฅ Ku saurari cikakken jawabin.

ู†ุณุฃู„ ุงู„ู„ู‡ ุฃู† ูŠู†ูุนู†ุง ุจุงู„ุนู„ู…ุŒ ูˆุฃู† ูŠุจุงุฑูƒ ููŠ ุฌู‡ูˆุฏ ุงู„ู‚ุงุฆู…ูŠู† ุนู„ู‰ ู‡ุฐู‡ ุงู„ุฏูˆุฑุฉ.

KAMMALA DAURA TA ILIMIAn kammala Daura ta Ilimi cikin nasara a JIBWIS Islamic Centre, Guzape, Abuja, ฦ™arฦ™ashin kulawar S...
17/09/2026

KAMMALA DAURA TA ILIMI

An kammala Daura ta Ilimi cikin nasara a JIBWIS Islamic Centre, Guzape, Abuja, ฦ™arฦ™ashin kulawar Sashen Harkokin Addini na Ofishin Jakadancin Saudiyya a Abuja.

A yayin taron, Dr. Abdurrahman Sani Yakubu Zaria ya gabatar da jawabi mai zurfi kan muhimmancin neman ilimi da amfani da shi wajen gyaran alโ€™umma.

๐Ÿคฒ Allah Ya sanya ilimin ya zama mai amfani, Ya saka wa dukkan masu gudummawa da alheri.

Ofishin Yaษ—a Labarai da Sadarwa
Dr. Abdurrahman Sani Yakubu

ู‚ุงู„ ุดูŠุฎ ุงู„ุฅุณู„ุงู…:  "ู…ู† ุชุฏุจุฑ ุงู„ู‚ุฑุขู† ุทุงู„ุจ ุงู„ู‡ุฏู‰ ู…ู†ู‡ุ› ุชุจูŠู† ู„ู‡ ุทุฑูŠู‚ ุงู„ุญู‚" ุงู„ุนู‚ูŠุฏุฉ ุงู„ูˆุงุณุทูŠุฉ ุต: ูกู Sheikhul Islam ya ce: โ€œDuk Wa...
15/09/2026

ู‚ุงู„ ุดูŠุฎ ุงู„ุฅุณู„ุงู…: "ู…ู† ุชุฏุจุฑ ุงู„ู‚ุฑุขู† ุทุงู„ุจ ุงู„ู‡ุฏู‰ ู…ู†ู‡ุ› ุชุจูŠู† ู„ู‡ ุทุฑูŠู‚ ุงู„ุญู‚" ุงู„ุนู‚ูŠุฏุฉ ุงู„ูˆุงุณุทูŠุฉ ุต: ูกู 

Sheikhul Islam ya ce: โ€œDuk Wanda ya nazarci Alkurโ€™ani, yana mai Neman shiriya daga cikinsa; to, hanyar gaskiya za ta bayyana gare shiโ€.
Alwasitiyyah, P: 10.

-Sheikh Dr Abdurrahman M. Sani YakubuAbdurrahman M. Sani Yakubu

NASIHA Kada ka bari abin da ya faru a jiya ya hana ka kyautata yau.Mutum ba ya rayuwa da abin da ya wuce, sai dai ya koy...
10/09/2026

NASIHA

Kada ka bari abin da ya faru a jiya ya hana ka kyautata yau.

Mutum ba ya rayuwa da abin da ya wuce, sai dai ya koyi darasi daga gare shi. Idan ka yi kuskure, ka tuba. Idan ka yi rashin nasara, ka sake ฦ™oฦ™ari. Idan kuma ka samu niโ€™ima, ka gode wa Allah.

Rayuwa dama ce; kada ka bari ta wuce ba tare da ka kusanci Allah ba. ๐Ÿคฒ

Dr. Abdurrahman Sani Yakubu

Address

Plot, 120 Nile Street Maitama FCT Abuja
Abuja

Telephone

+2348169360884

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Dr. Abdurrahman Sani Yakubu Zaria. posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The School

Send a message to Dr. Abdurrahman Sani Yakubu Zaria.:

Shortcuts

Share

Category